What you sow.

410 43 2
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎




STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).




Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.


Kyautatawa wanda ya kyautata maka, haka ake yi. Butulci guba ne wata rana za'a yi da-na-sani na har abada.


Wannan page ɗin gaba ɗaya sadaukarwa ne a gareki HAFSAT YAHAYA ALI, ina miƙo maki jinjinar ban girma, haƙiƙa ina matuƙar jin daɗin sharhinki akan littafin nan, na gode ƙwarai da gaske, Allah ya bar zumunci ya albarkaci rayuwarki, ameen✨✨ i love you wujiga- wujiga💋💖.





Ta gama shirin islamiya tsaf! Amman ta kasa fitowa saboda dariyar dake cike ɓam! a cikinta, ga dariya ga tausayi amman tasan dariyar tafi ƙarfi, shiyasa ta maƙale a ɗaki saboda tasan in har Inna ta kamata tana dariya akan abunda ya faru wayewar yau a gidan nasu, to ta tabbata sai Inna ta saɓa mata kamanni.

Ita ko har ga Allahnta abunda ya faru yai mata dai-dai, sabidda ko ba komai Gwoggo zata ɗan saitu ta wani fanin, saboda abu ne wanda ta daɗe tana jiye mata faruwarshi amman ita bata hango shi da kanta ba, ashe dama akwai ranar ƙin dallanci? Lallai duniyar nan abunda kai shi zai bika, kama tudinu tudanu, kayi ma wani, wani kuma ya rama maka.

In kana ganin kafi ƙarfin wani ka zalunce shi, to kaima zaka haɗu da wanda yafi ƙarfinka, in kana ganin kafi wani dukiya ka wulaƙanta shi to Allah zai iya karɓewa dare ɗaya lokaci ɗaya domin da talauci da arziƙi duk jarabawa ce ta ubangiji, in da mulki kake taƙama shima Allah ne ya baka riƙon ƙwarya, a yau ba sai gobe ba sai ya ƙwace ya bai ma wani, kai ko ma da me kake taƙama baka isa ka ja da hukuncin Allah ba.

In kuma kaga ka daɗe kana shuka tsiya amman baka girbe ba, to Allah ya ara maka lokaci ne, kuma haƙiƙa ko-ba-daɗe-ko-ba-jima ko ma meye ɗinnan ka shuka sai ka girbeshi da hannuwanka, ko ka girbe shi anan gidan Duniya a lokacin da kake da sauran dama, ko kuma ka girbe a gidan da ba zaka iya canja tunani akan wannan amfanin gona maras kyau da ka girbe ba, dole a haka nan zaka ci shi kuma ya halaka ka, ubangiji Allah yasa mu dace.

"Ke mutiniyas! lafiya? na ganki sharɓe bisa gado bayan ga lokaci yana ta shigewa, kin san a tsarinmu fa ba African time" Karime ta faɗa lokacin da ta ƙaraso cikin ɗakin ba tare da sanin Bintu ba, saboda ta lula can! duniyar tunani ko sallamar Karime ma bata ji ba, ɗago kai tai tana dubanta, suna haɗa ido ta ɓarke da dariya.

Haɓa Karime ta kama tace "yau naga walele giɓin takwaru, lafiyarki ƙalau Bintu? da kin kallan sai kawai ki sheƙe da dariya to ko dai na cika hoda ne ban sani ba?" ta faɗa tare da sa tafin hannu tana goge fuskarta.

Hakan da tayi sai ya ƙara bata dariya dan haka sai ta ƙara sheƙewa hadda ɗaga ƙafa.
"kefa muguwa ce Bintu, ba kasafai kike kallar wannan dariyar ba sai kin shirya mugunta kuma an faɗa, wannan karan dani kenan akai wasan ba tare da sani na ba, tunda na faɗa sai ki janyo ni muguwa kawai!" ta faɗa tana harararta, don ta fara ƙuluwa da dariyarta.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now