Soulmates.

351 35 3
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).


Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.


Dangantakar jini ba ita kaɗai ce shaidar ƴan-uwantaka ba, ɗan-uwa shine abokin da zuciyarka bata natsuwa idan baya nan.




Cikin sati biyun da suka wuce ba ƙaramar shaƙuwa ce ta ƙara shiga tsakanin Binana da Deey ba, kusan kullum suna tare da juna da sun rabu kuma suna maƙale a waya, ɓangarensu Maryam da Adeel ɗinta suma abu yai nisa dan soyayya suke narkawa san ransu, a makarantarsu kuma ba abunda ya canja suna maida hankali sosai kuma yanzu sunyi nisa ba laifi.

Rayuwar Abuja tayi masu daɗi dan har wani ƙiba, haske da kyau suka ƙara, sun wani murje abunsu, gayu kam yayi gaba, yau saturday Aunty Naseey tace su shirya su rakata su je gaishe da Hajiya Aunty, suka ce wacece Hajiyar Aunty? Aunty Naseey ta amsa masu da mamansu Al'ameen ce, a tare suka riƙe baki suka ce "gidansu Al'ameen?" Aunty Naseey tai dariya tace "eh ko ba kwa zuwa ne?".

"A'a zamu je!" cewar Maryam, Bintu kam ta shiga wani yanayi.

Aunty Naseey ta cigaba "Al'ameen ɗin ma da kansa zai kai mu yana nan zuwa ƙarfe sha biyu".

Wato Deey yasan da zuwansu kenan?, to me yasa bai gaya mata ba? bayan jiya da daddaren nan suka rabu, "shi zai kaimu?" ta tambaya.

"Eh yanzu nan na kirashi naji ko yana da time dan Mallan Lado (direbansu) yayi tafiya garinsu, jiya".

***
Anko din da aka masu na atamfa su uku hadda Tatus shi su kasa, sunyi kyau abunsu kowa dai da kallar style ɗinta, sun girka ma Hajiya Aunty Waina lafiyayya da miyar taushe, ƙarfe sha biyu dai-dai ya iso dan shi dama a tsarinshi ba wani abu wai shi African-time.

Aunty Naseey ce a gaba suna ta hira da Al'ameen su kuma a baya suka ɗure, duk ɗagowar da za tai sai ta tsinci idon shi akanta ta center mirrow, shi kam a nashi ɓangaren tayi masa kyau ne sosai musanman ɗaurin kallabin da tayi very matured, kuma ya tafi dai-dai da zubin fuskarta.

Maitama suka nufa inda gidansu Al'ameen yake, Bintu tana ta ganin yadda suke wuce gidaje masu kyau da ban sha'awa, sakin baki tai ganin gidan da suka doshi gate ɗinsa gadan-gadan, tuni mai gadi ya wangale masu tangamemen gate ɗin da ya bayyana wani tsararren gida, zubi da tsarin gidan komi ya tafi da zamani yayi kyau sosai.

Aiko tun kamin su sauka Bintu ta gama bama zuciyarta magana cewa duk abunda zata gani vidio da hotuna kawai zata riƙa ɗauka a ƙwaƙwalwarta ba tare da ta nuna cewa ta gansu a lokacin ba sai a sa'ilin da ta koma gida zata zauna tayi playing da zooming sai ta saki baki tai mamakinta ita kaɗai, abunda ya kama na dariya ma tai ma kanta, dan ta tabbata ire-irin wa innan gidan ta tabbata bazaka shiga ka fita ba tare da kaga wani baƙon abu ba, musanman su da suka fito daga ƙauye.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now