The power of Du'a.

380 46 11
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎


STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).


Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.


SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.




Mai aikata alheri ya fi alheri alheri, mai aikata sharri ya fi sharri sharri.



Ƙarfe ɗaya da minti sha biyar dai-dai azhan ya ƙwala kiran sallar Azahar a cikin unguwar Kan-giwa dake cikin garin Mani, a hankali tayi miƙa, da ƙƴar ta raba jikinta daga kan gadonta tana hamma, kwana biyun nan jikinta a matuƙar kasalance take jinsa, har ta shiga bayi da niyyar alwalla sai kuma taja turus! ta tsaya, wai me ma take shirin yi ne? Alwallah ko? to ai bata sallah! ita wallahi mantawa take shaf ko dan hadda wannan ne karonta na farko da fara yin haila? ko kuma dan sabo da yin sallar ne ohonmata!

Sai da tayi changing duk da ba wani rushing take ba, kana ta fito daga bayin, direct kan gadonta ta koma ta kwanta tare da jan bargonta tana ƙudundunewa, tana iya tunawa clearly kwanaki uku da suka wuce sadda ta shiga toilet da niyar fitsari tana cire pant ɗinta ta gani, ta tsorata sosai duk da dama tasan da cewa ko wacce mace sai tazo matakin da zata fara shi kuma sai ta kai wanda zata daina shi a rayuwarta, kuma ma Inna ta taɓa mata jawabi akanshi, a islamiyya ma an masu a fiqihu, infact ma daga Maryam har Karime ba wanda bai fara ba a cikinsu itace dama kawai a cikinsu bata fara ba.

Yanzu ta girma kenan? Ta shiga cikin sahun ƴan mata, ta tuna yadda ta tuɓe kayanta ta tsaya a gaban madubi tana examining jikinta, though ba wasu changes sosai ta gani ba, har yanzu dai ƴar ƙirgar dangin da ta fara shine a ƙirjinta, amman bata ƙi kula da yadda fatar ta take wani sheƙi na musamman ba, hatta gashin kanta has became oily, duk da cewa dry hair gareta, abunda kawai ta iya lura dashi kenan, lokacin ƙarfe huɗu na yanma har yayi amman ta san azuminta ya riga ya karye, sai da ta mayar da kayanta kana taje ta samu Inna da batun.

In every detail zata iya tuno dukkan jawaban da Inna ta zaunar da ita tayi mata, tunda ga kan asali, dalili, amfani, da yadda mace ya kamata ta kula da jikinta lokutan da takeyi har ma lokutan da bata yi, zuwa abubuwan da ya kamata mace ta yi da wanda bai kamata tayi ba in tana menses ba abunda Inna bata gaya mata ba, ita kam tana jin daɗin samin Inna a matsayin uwa a gareta, in aka barta ma sai tace anya akwai wanda yayi sa'ar uwa kamar yadda tai sa'ar Inna kuwa? amman ta riga da tasan duniya da faɗi take, dan haka za'a samu wacce tafi Inna ta wasu ɓangaren.

May be abunda yasa take tunanin haka mostly uwayen da take gani bata ga wanda ya kamo ƙafa da Inna wajen tarbiyar ƴaƴanshi ba, most expecially ma uwayen gidansu, ita kam tana me gode ma Allah domin Inna bata rage ta da komai ba.

Yanzu an shiga goman ƙarshe, duk da cewa bata da tsarki amman Inna bata barta ba, haka take tada ta su raya dare da ibada, Inna tana tahajjud ita kuma zata koma gefe tai ta zikri da hailala, tare da karatun alquar'ani, sannan in sun gama su koro ma Allah koken su, dan haka ne ma basu bacci sai bayyan asuba, tunda aka shiga goma masu falala musanman a dararen mara da suke sa ran ganin daren Laylatul Qadr, to ita ba tada wata matsala in ta kwanta daga asuba sai azahar take tashi tunda sunyi hutun makaranta ba zancen zuwa, to daga nan ne take tashi sai ta canji Inna wacce take kwantawa da ta gama zuhur, amman wannan tsarin nasu yana wanzuwa ne a ranukun da ba Inna ke da girki ba.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now