The Cinema.🏦

342 30 0
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.



Idan ka kasance cikin tahowa da-baya-da-baya, mutuwa kuma cikin gabatowa gaba, to lallai ya mamakin saurin haduwa!

Yau Juma'atu babbar rana, ana tashi makaranta suka wuce Garki market suka yo siyayya cikin kuɗaɗen da Kawu ke basu, dama Bintu tace ma Al'ameen kar yazo ɗaukarsu because they are going for their first date today bata so ya ganta sai lokacin da sukai fixing ma fitar, duk list ɗin da suka rubuta sai da suka samo komai, kana niƙi-niƙi suka koma gida.

Suna shiga kuwa ba wani ɓata lokaci suka faɗa Kitchen, sai da suka ida nasa ɗan waken da suka tarar Aunty Naseey na nasawa kana suka shiga aikin snacks ɗin da za suyi, duk shirin tarbar Adeel suke da zai dawo gobe, sai yanma liƙis sukai retering a ɗakinsu, suna hutawa.

Bintu na kwance akan gado tana chatting da Karime dan ita ma yanzu ta faso gari tayi babbar waya, voice note kawai suke suna shan dariyarsu, Karime na bata labarin wani saurayi da tai mai shago a kantin kwari, dai-dai lokacin Meerat ta hawo online, Maryam dake bakin wardrobe tana ta fito da kaya, ta ƙara tambayar Bintu a karo na ba adadi tace "kalla Bintu ko na sa wa innan" ta faɗa tana jona wata doguwar riga a jikinta.

Bintu tasa hannu ta tallafe kanta tace "Na shiga uku Maryam, wai ke me ke damunki ne? Yau ne zaki fara haɗuwa da saurayi a rayuwarki ne, da duk zaki bi ki firgita kwanciyar hankalinki, ki addabi mutane, ha'a".

"Hmm wallahi am a bit nervous Sisto".

"There's no reason to be, ki kwantar da hankalinki pls".

Fuskar tausayi Maryam tai, tana rungume hannayenta, sai ta ba Bintu dariya, tana sakin dariya ita ma Maryam ɗin ta ɗauka, nan suka cigaba da dariyar.

Bayan sun gama sallar isha'i, tana ida kimtsawa Deey ya kirata cewa ya iso, sai da ta kammala tsab kana ta fito tana waving Maryam dake naɗe akan gado tana waya da Adeel ɗinta, sai da ta gayo ma Aunty Naseey zata tafi tace "Allah ya tsare ki kula da kanki kuma kar ki wuce tym ɗin da nace".

"To insha Allah" ta fita tana ma Ameer wayo dake kukan sai ya bita, motar shi na waje ta isa a hankali ta buɗa ta zauna a mazauninta, ya zuba mata ido, "Deey barka da dare!" ta faɗa tana ɗan ƙyafta idanu kaɗan-kaɗan.

"Barka dai gimbiyar mata nayi missing ɗinki Allah".

"Jiya kamar yanzu ne fa muka rabu".

"Awa ashirin da huɗu fa! muna gari ɗaya, yau a office ma kewarki ta hanani aiki da na ɗan juya sai inga kamar zan ganki".

"To Ƴallaɓai ai mun afuwa, yanzu kam gani har sai lokacinmu ya ƙare".

"Ok love! let's move" ya faɗa yana saka seat belt ɗinsa, sai yanzu ta ƙare mai kallo ba ƙaramin kyau yai ba cikin ƙananan kaya black ɗin wando da ash ɗin riga mai dogon hannu, gashin nan nashi sai ƙyalli yake, mafi yawan lokuta takanso ace tana da damar taɓa gashinsa domin dai abin burgewa ne kuma yana samun kulawa sosai wajen mamallakinsa.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now