The missing bag.

526 60 4
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.




🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.





Shirye-shiryene gadan-gadan ake tayi a sashen su Bintu, kasancewar gobe suna, tunda safe Baba ya kawo jibga-jibgan raguna ya ɗaure su, ba laifi yayi ruwa yayi tsaki dai-dai gwargwadon halinsa, ya bada kuɗi anyi tanadin sunan, wanda su Inna Balaraba ne da Yakumbo suke ta faɗi tashi wajen ganin komai yana tafiya yadda ya dace.

Ɓangaren matan gidan duk sun zo sun ma Inna barka, koma da wacce sukai ita kam ta karɓa kuma bata kalle su da komai ba dangane da abunda ya faru, ko wane hali dai mutum yayi shuka ce yake ma kansa.

Ya Gwal-Gwal ma duk yadda taso ta maze ta kasa, dan yaran akwai su da shiga rai, dan haka kullum sai ta leƙa da sunan tazo ganin masu wanka, hakan kuma bai hana in abun nata ya zo ba ta yaɓa ma Inna a ka.

Inna Balaraba kam ba irin tsegumin da bata sha ba wai ita ƴar suna daɗi ba? taje ta tare a gindin mai-jego, ko suce duk gulma ne yake kaita, ita kam tai kunnen uwar shegu da su saboda ita tasan dan wa take yi, in ma dan gulma ne ta rasa inda za taje ta tare sai wajen su Inna, suda basu da abun gulma komai a sarari suke yin shi, ai in dai maganar gulma ne kam aka zo wajen su masu bakin faɗen to a shafa fatiha kawai, dan sai an ɗibi abinda yafi gulma.

Adda Manga, babbar yayar su Naty dake zaune a Belan-gada, dama ita ke wankan su Inna da Yakumbo, duk da dai wannan ba haihuwar farko bace amman rainan ƴan-biyu barin ma ga Inna da ba wai ta cika lafiya bane, saboda hawan jinin da take dashi, dole sai an dafa mata. Tunda akai haihuwar Naty ta sanar mata sai ko gata washegari ta iso.

Ita ke wankan Babies, ɗayan ɗakin Inna tasa Bintu ta gyara mata, sai dai ana suna zata koma gidan Naty ta rinƙa zuwa safe da maraice in ta gama wankan sai ta koma can ta kwana, wannan kwana shiddan ma da ya aka yadda za tayi shi dan ma dai su Inna da Yakumbo sun matsa ne.

Washe-gari tun asubar fari Bintu ta buɗa ido, tana tashi ta tada Maryam dake gefenta, nan suka hau karaɗi a cikin gidan suna ta suruce-surucensu, can dai shirin sune suma. Ba laifi mutane sun ɗan taru, dan tun jiya ƴan-uwan Naty daga belan-gada suka rinƙa isowa, wasu kuma sai zuwa yau zasu iso.

Fannin su Baba ɗan tsoho ma ƴan nesa waenda basa cikin garin Mani suma sun fara sauka, wasu daga cikin baƙin a nan suka kwana wasu kuma a gidan Naty, masha Allah Inna dai ƴar dangi ce dan ga dangi nan rututu, tun ma sha'ani bai kankama ba.

Ɓangaren ƴan uwan Alhaji Muhammadu na nesa sun iso, sai dai duk sun raba kai a gidan kowa ta kwana ɗakin wacce suke shiri da ita a cikin matan gidan.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now