Cikin duhun dare...

617 60 2
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa.


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

Wanda na kusa ya tozarta shi, sai a yalwata masa samun na nesa.


Yau su Bintu suka zana jarabawarsu ta ƙarshe a primary, tafe suke ita da Karime suna ta labarinsu kamar yadda suka saba.

Hankalinta gaba ɗaya yayi wajen kakanninta, dan haka ta yanke shawarar yau can zata fara yada zango, mafiya yawan lokuta dama daga makaranta take biyawa tacan su sha surutunsu da ƴar tsohuwa, in taci sa'a kuma ta tadda Baba to su sha barkwanci.

To kwana biyu bata leƙosu ba, duk sai taji tayi kewarsu, gashi bawai suna da nisa bane da gidansu.

Sai da Karime taja ta har cikin gidansu suka gaisa da Innarta sannan ta fito tai hanyarta.

Tun a zaure ƙarar Radio ya fara dakar kunnenta kamar kullum, murmushi tayi, "Naty sarkin jin labarai kenan." sannan ta ƙarasa ciki, nan tsakar gida ta taras da ita kishingiɗe kan tabarma, ɗaure da zani a ƙirji mafecin kaba a hanunta tana ta fifita, goro ne a bakinta ga Radionta a gefe tana ta aikin watso labarai.

"Ajuzatun tsohuwa tana cin goro wiii-wiii" Bintu ta faɗa cikin sigar zolaya tana wata tafiya kamar me ta-ta-ta.

"Ah-Ah-ha! Ah-Ah-ha! ga Bintoto ga Bintoto" ƴar tsohuwar ta faɗa tana tashi daga kwanciyar tare da gyara ɗauren zaninta kan rigarta.

"Shikenan kinyi layar zana, ganinki sai yau takwara? Kullum muna duban hanya amman sai dare ya riske mu ba muga zuwanki ba, ɗazu nan ma mai-gidan naki ya gama faɗin anya baza a cigito lafiyarki ba?".

Bintu ta ƙyal-ƙyale da dariya tana wancakalar da sandal ɗinta da jakarta gefe guda dan shagwaɓa take zuba ma kakannin nata sosai.

Mazauni tai ma kanta kan tabarmar kusa da Naty, ta yaye ƴar hijabinta kana ta sauke ajiyar zuciya.

"Wallahi Naty kuna raina nayi kewarku sosai, Allah jarabawa muke shi yasa ban leƙo ba".

"To ya jarabawar?".

"Mun ma gama, ni bani mafecin nan nayi fifita! Ke tsohuwa dake ma har wani zafi kike ji?" ta faɗa tana amsar mafaicin a hannun Naty tana dariya.

"Kinji tsiyar ai! Da kinzo ne da mun fara, ni tashi ma ki tai gidanku gaisuwar ta isa haka, kin tare mun rawar gaban hantsi" Naty ta faɗa tana murguɗa mata baki irin yadda suka saba.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now