Sa lalle💅.

197 17 0
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.







----------------------------------------------------------

Saura ƙiris mu cin ma burinmu, wani lokaci ƙalilan me zuwa da zamu buɗi ido a matsayin mamallakan juna, shin akwai farin cikin da yafi wannan cikin wannan hali da muke ciki a rayuwarmu?...
BINTU DA AL'AMEEN.

--------------------------------------------------------------






DUNIYA LABARI!, wai yanzu Ya Saleem shima ya zama wani labari a doron ƙasa, abunda ta lura shine da mutum ya tafi tashi rayuwarce kawai ta ƙare!, tashi rayuwarce kawai ta tsaya! amman komai zai cigaba da wanzuwa ga sauran ababe masu rai kamar yadda ya kamata, tafiyar mutum baze tare komai ba, kuma bazai hana wani abu faruwa ba.

Me jin yanwa zai ci abincinsa, me jin bacci zai yi kayansa, me tafiya ze yi abunsa, me biki zai yi aurensa, dole a cigaba da sabgogin rayuwa domin ba wanda zai tsaya domin tafiyar wani, lallai mutum ba a bakin komai yake ba.

Yanzu dai gashi kwana goma kenan kawai da mutuwar Ya Saleem amma ana nan ana ta hidimar bikinta da ze kama kwana biyar masu zuwa, duk da mafiya yawan su zuciyoyinsu na ɗauke da alhini na rashinsa.

Ba abunda yafi bata mamaki kalar tashin hankalin da akai yau a gidansu da aka kawo lefenta, akwatuna goma sha biyu aka kawo, saiti biyu me shidda-shidda, shine fa akai ta tsegumi da cece kuce a gidan musanman da aka ga kallar kayan da aka zubo a ciki, sai hassada ƙiri-ƙiri ta rinƙa tashi.

Babban abun mamakin wai hadda Iyatu kan gaba wajen wannan batu kamar ba ita bace tasha bori ƴan kwanaki akan mutuwar ɗanta ba, duk ta natsu kwana biyun nan, har ana tunanin ko mutuwarshi ce zata sa ta natsu a rayuwarta, to ashe me hali dai baya fasa halinshi.

Ita kam da tasan haka za'ai wannan al'amari da tace mashi ma kar ya kawo lefen nan ya bar mata can kawai in taje tayi amfani dashi, to a hakan ma yace mata ba duka ne ya kawo ba wasu na can gida banda kuma saiti guda dake gidan Yakumbo wanda suka sayo a Katsina, ƙila da sun san da sauran da haɗiyar zuciya zasui su mutu ko?.

Ita bama taso aka kawo nan gidan ba, dan dai Baba yace dole hidimar biki nan gidashi za'a dawo a yita, shiyasa Yakumbo ta kwaso mutanenta aka zo aka tarbi lefe cikin karamci, haka suka haɗa ma ƴan kawo lefen nan tukuici da yawa suka basu.

Suna tsaitsaye tarinsu himili guda kowa ya kasa ido ana ta ƙara maimaicin kallon lefen nan kamar kallonsu ze sa ya zama nasu, sai ƙara ɗuruwa ake ana ƙara yawa don hadda mutanen unguwa, da Yakumbo taga abun ya fara keta hankali an taru kamar za'a dasa wawa, tace a zuge mata akwatunan dama ta baza wa inda tasan basa ɗaukar wargi a akwatunan daga haka tace kowa ya fita an gama ganin lefen.

Sai da tai jan ido kana aka watse balle an san hali, ita dai Bintu na gefe rakuɓe tana binsu da kallo kawai, don ita abunda ya dameta shi ya ishe ta, tana kallo Yakumbo ta buɗe ɗakin Inna karo na farko kenan tun bayan rasuwarta, suka sa kayan a ciki, tana daga can nesa tana ɗan leƙa ɗakin kamar zata ga Inna ne a ciki.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now