Wata Ƙaddarar😓

173 15 0
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.






.

--------------------------------------------------------------

Wasu ƙadarorin tamkar zanen dutse suke, sune ƙaddarorin da mutum baze iya tsallake masu ba, domin alƙalami ya riga ya bushe a kansu, tafe kawai nake a rayuwa ina tuntuɓe da irinsu ban kuma san nawa ne a gaba da ban cinmawa ba! Haka rayuwar take!.
BINTU

-------------------------------------------------------------








Washegari tunda safe suka shirya yazo ya ɗauke su green house suka fara zuwa, haka ya zauna yana ta zaɓar kalar hijabi ana ɗinkawa tun tana ce mashi dan Allah ya barshi haka har ta saduda ta zuba ma sarautar Allah ido, har su Maryam da Bahijja duk sai da ya ɗiɗɗinka masu kala biyar-biyar hatta Aunty Deeja sai da ta samu rabonta, Yakumbo da Naty ma dake can gida ba'a manta dasu ba.

Daga nan ya wuce dasu wani babban kanti na underwears zalla gasu nan birjik haɗaɗɗau masu kyau, sannan yace ta zaɓa, ita kam kunya kasheta yai a wajen, ya ze mata haka? Ai ita a iya nata tunanin in za'a haɗa lefe, kamar dai ita yanzu ba se ya tambayi Maryam size ɗinta ba? shi kuma sai yaje can ya siya ko kuma yaba Ammie ko ma yayye mata in yana dasu su siya ba? Kai ko su Zarah ya ba ai zasu iya siya, sai kawai ya kwasota gata gashi kuma wai ta zaɓa😩.

Aiko ta tsaya mashi ƙiƙam, Maryam yaja tunda ta gwada mashi size ɗinta na komai, ya shiga zagayawa yana ɗiɓar duk kallar da yaga ta mashi kyau, da yake shagon hadda irin kayan matsun nan, suma duk wanda yai mashi kyau sai ya ɗauka duk da ya siya irinsu da yawa daga India be ma haɗa su a akwatin lefe ba gidansu ya kai ya jera mata a wardrobe sai taje ta gani.

Yace ma Maryam da Bahijja suma su ɗiɗɗiba wanda suke so, ita kam tunda Allah ya taimaketa ta kame natsuwarta a wata kujera da mai shagon ya bata, sai ta zuba masu ido kawai tana kallo tana jero tasbihi a zuciyarta.

Sun shiga central, sun yawata sosai, sun kuma yo siyayya ta tashin hankali, ita ko sai mamaki take sai kace yanzu ne ze fara haɗa lefen duk ina zasu kai waccen uwayen kayan da ya siya?.

Da ƙyar da suɗin goshi ta iya lallaɓarshi suka bar kasuwarnan, dan ita ta fara ganin kamar be san ciwon kuɗi ba Allah, be ƙara saurararta ba ya ƙara tsayawa wani kantin maƙulashe ya ƴebo masu kayan daɗi harda tsarabarsu twins da Abdul, daga nan niƙi-niƙi suka koma gidan Ya Saleem, dama wai su gabatar da sallar azahar suci abinci kana su ɗibi hanyar Mani kuma.

Lokacin da suka isa Ya Saleem be nan, dama sun fita akan ze je Mani Baba yayi kiranshi baze daɗe ba zai dawo, dan yana son in ya dawo ya shiga asibiti a yau ɗin akwai wasu patients ɗinshi da yake son dubawa.

Suna isa suka hau fitar da kaya zuwa ciki, don yace su fitar su kimtsasu, su fitar ma nasu Aunty Deejah, sai su kammala sauran, ganin kayan da yawa dama sunci uban booth, bayan motar ma a takure du Maryam suka zauna, ganin kayan nada yawa sosai sai yace masu bari yaje yanzu ze dawo.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now