Ɓoyayyan al-amari

797 99 2
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎


STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).




Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa.



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.




Bi rayuwar nan a hankali don kuwa baka immata. Haka Rayuwa take da nauyi fiye da duniya.



"Bintu! Ki tashi nace, kin san bana san ƴan koke-koken nan ko? Meye kuma aka maki? ke da dama hawayenki basa tsada, ace mutum komai sai yayi kuka".

"Inna ba Ameerah bace kullum sai tai ta faɗa ma ƴan ajinmu wai Innata ƴar duniya ce, wai ƙila mani shegiya ce!" nan ta kara fashewa da kuka.

Gaban Inna ne yai mummunan faɗi, in ranta ya kai dubu to duk a bace yake, "ita Ameerah take faɗin haka! Kira mun ita".

Bintu taji mamakin furucin Inna saboda duk abunda zai faru ko yaje ya dawo kan kunnenta, bata taɓa cewa zata nemi mai laifin dan ta tuhumeshi ba, sai dai tayi haƙuri ta maida komai ba komai ba ta miƙa lamuran ga Allah kuma a kullum wasiccin da ta kema Bintu kenan akan haƙuri dai haƙuri akan komai, lallai gaskiyar hausawa da suke cewa tura takan kai bango! da alama an taɓo inda baya ma Inna daɗi sam.

Da ƙwarin gwiwa Bintu ta isa ɓangaren su Gwoggo ta kira Ameerah.

"Ameerah! Me naji kina cema ƴan ajinku?" Inna tace a yayin da take zama kan kujera dan ta dai-daita natsuwarta.

"Ni? ni ba abunda nace masu" ta faɗa tana fiki-fiki da idanu.

Nan Bintu tas ta mayar da abunda ya faru dallah-dallah.

"Ba kyau abunda kike Ameerah, maganar sirrin gidanku da kike faɗa ma mutanen waje bai kyautu ba! Kina zubar da mutuncin kanki da namu ne a idon jama'a sannan kuma maganar duniyanci da kika ce, wane duniyanci nake Ameerah? Me kika taɓa ganin na aikata da yai maki kama da duniyanci? Da har kike sheganta ƴar uwarki ta sunnah!?".

"Wallahi Inna nima ba laifi na bane ai Gwoggo ce take gaya mana kuma ma har da cewa wai ke ƴar iska ce shiyasa ma ba'a da tabbacin ko Bintu ƴar Baba ce wai ita shegiya ce!".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now