An yanka ta tashi!.

251 20 2
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.


















/////////////////////////////////////////////////

AS-SALAMU-ALAIKUM WA RAHMATULLAHI WA BARAKATUHU.

INA MIƘO SAƘON BARKA DA SHAN RUWA TARE DA FATAN ANYI SALLAH LAFIYA GA ƊAUKACIN AL'UMMAR MUSULMI, UBANGIJI ALLAH YASA MUNA CIKIN BAYIN DA YA ƳANTA KUMA YA GAFARTA MAWA A CIKIN WANNAN WATA MAI RAHAMA DA YA GABATA, TARE DA FATAN MUNA CIKIN BAYIN DA YA KARƁI IBADUNSU KUMA YA AMSA MASU ROƘONSU, AMEEN🙏.

INA ME FARIN CIKIN SAKE DAWO MAKU DOMIN CIGABAN LABARIN NAN A DAI-DAI WANNAN LOKACI, INA FATAN DUK KUNA CIKIN ƘOSHIN LAFIYA A DUK INDA KUKE, ALLAH YA ƘARE MU DA LAFIYA BAKI ƊAYA AMEEN🙏.

LABARIN DUNIYA MAKARANTA CE KAMAR YADDA NA FAƊA A FARKO, LABARI NE DANA TSARA ZAI TAFI AKAN MAIN CHARACTER KAWAI WACCE A YANZU DUK MUN SANTA WATO "BINTU" A INDA NACE BAZAN TSUNDUMA DA GAYA MAKU RA'AYI DA MAƘASUDIN RUBUTA WANNAN LABARI BA, HAR SAI ALLAH YA NUNA MUN NA KAMMALA SHI LAFIYA A CIKIN IKONSA, INA FATAN ZAKU CIGABA DA HAƘURIN BIBIYAR WANNAN LITTAFI HAR ZUWA LOKACIN DA ZAN JINGINE ALƘALAMINA.

NASAN DA YAWA A CIKINKU HARDA MA WA INDA BASUI ƘORAFI BA DUK NASAN CEWA BAKWA JIN DAƊIN YADDA UPDATE ƊIN LITTAFIN NAN YAKE ZUWA MAKU BA AKAN KARI BA, KO BA A YANDA KUKA ZATA KO KUKE SO BA, NI KAINA GASKIYA BANA JIN DAƊIN YADDA NAKE BARINKU A CIKIN TSUMAYIN SAMUN CIGABAN LABARIN NAN, HAKAN YASA NA FITO DA WANI SABON TSARI A YANZU.

DAGA WANNAN UPDATE NA YAU INSHA ALLAHU ZAKU CIGABA DA SAMUN CIGABA DUK LITININ-LITININ, MA'ANA ZAN RIƘA UPDATE SAU ƊAYA A SATI WHICH IS DUK MONDAY IN ALLAH YASO.

KUNGA YANZU KOWA YASAN UPDATE ƊIN LITTAFIN NAN ZAI RIKA ZUWA DUK RAN LITININ NE KAWAI HAR ZUWA ƘARSHEN, NI KUMA TA ƁANGARE NA INSHA ALLAHU ZANYI ƘOƘARIN SAMAR DA HAKAN KAMAR YADDA NA FAƊA, AMMAN KUMA WANNAN TSARI NANE, HAR KULLUM KUMA MUNA NAMU ALLAH NA NASHI NE, DAN HAKA KARKU ZARGE NI IN HAKAN BAI SAMU BA.

ZAN DAI YI ƘOƘARI GWARGWADON IYAWATA KUMA WALA'ALLAH ACE WANI ABU YA TASO MIN DA BAZAN IYA SAMUN YI MAKU RUBUTU RANAR LITTININ BA ZAN YI ƘOƘARI NA SANAR DAKU INSHA ALLAH, SANNAN NA RAMA MAKU A WATA RANAR, IN KUMA KUNJI SHIRU TO DAN ALLAH KUYI MAN ZATO DA FATA NA ALHERI, NAGODE, NAGODE ƘWARAI DA ƘAUNA DA KULAWARKU AGARENI, HAƘIƘA KOWANNE ƊAYA A CIKINKU INA SONSA KUMA DUK INA MAKU FATAN ALKHAIRI A RAYUWA TA DUNIYA DA LAHIRA, INA ROƘON ALLAH DA RAHAMARSA YA HAƊAMU A CIKIN GIDAN ALJANNAH MAFI ƊAUKAKA, AMEEN🤲🤲.

YAUWA! BAZAN RUFE BATARE DANA MAKU BAYANIN TSARIN RUBUTU DA ZAI CANJA BA SHIMA, ZAI TASHI DAGA 3RD PERSON YA KOMA 1ST PERSON INSHA ALLAH, ANZO DAI-DAI GAƁAR DA LABARIN NAN ZAI FI TAFIYA IN HAR ALƘALAMINA YA KOMA A BAKIN BINTU INSHA ALLAHU, INA FATAN HAKAN ZEYI MAKU, NAGODE, ASHA KARATU LAFIYA.

///////////////////////////////////////////////////////












--------------------------------------------------------

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now