Unspoken word

535 54 31
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎




STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).




Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.



SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.





Am dedicating this chapter to my cute-little😜-cousin-sister, Amina Ibraheem Ɗan-mallam, I love you so much Amina Babba,😘😘 this page is all yours sweato, so do as much as u wish,😘😘😘😘 I wish u success in your up-coming examinations, u and Haji peeey (boiby-boiby)🤣🤣🤣, i pray a good-pious-handsome spouse for you guys, love from this side😍.

Helloh Readers🙌 hope u're oll fairing well!.

Okay now brace yourself to a chapter of 4600+ words😁.

Happy reading😊.









"Wai Bintu yau ba zaki yi kwanan wajen bane?".

"Eh Inna yau a ɗaki zan kwana kawai, ban jin zafi sosai".

"To shikenan jeki gyara shimfiɗarsu Fadil a ɗakin ki, sai kizo ki kwashe su".

"To Inna".

Bayan ta shimfiɗe su a katifarsu, ta wage duka tagogin ɗakin dan iska ta shigo, kana ta kwanta a ɗan gadonta, lamo tayi dan ba wai da niyyar bacci ta kwanta ba so take ta samu sarari daga Inna ta buga ma Mai-takalmi waya, dan tuni ta farauto wayarta ta ɓoye a ƙarƙashin filo, tasan dai ba zata buƙaci wayar da daddare ba in dai ba don kunna tocila ba, wanda hakan ne yasa ta nemo tsohuwar lantern ɗin su ta caja ta lokacin da suka maido wuta da magriba, sannan ta kunna ma ta ita.

Idonta a buɗe yake tana kallon hasken farin wata da ya shigo ɗakin ta kafafen tagogin, sannan tana iya jiyo sautin yaran gidan suna ta wasan su hankali kwance yadda kasan goman dare bata gota ba.

Jira kawai take Inna ta shigo dubasu kamin ta kwanta bacci kamar yadda ta saba, tana kwance tana ta aikin saƙa da warwara a cikin zuciyarta taji shigowar Inna, tun daga nesa ta hango hasken fitilar hannunta dan haka da sauri ta rufe idanunta tare da ƙara lamewa kamar wata mai baccin gaske, ita kanta tana mamakin kanta akan ƙoƙarin ɓoye ma Inna wannan al'amarin, ko me yasa ne sai ta ɓoye ne zata iya waya da Mai-takalmi? Oho dai!.

Ko da yake ma ta sha kuruminta ne, ai indai Inna ce tasan ba zata iya ɓoye mata komai ba, na tsawon lokaci, ba tare da ta gano ba ko kuma ita da kanta ta tona kanta ba, amman dai zata ga har zuwa wane tsawon lokacin ne zata iya ɓoye ma Inna Mai-takalmi.

Ko da Inna ta shigo ita ta fara haskawa kan ta koma kan twins, fo ɗinsu ta ɗauka ta ɗora su akai, aiko nan aka fara daru domin kuka suka saki kamar yadda suka saba a duk lokacin da aka katse masu bacci domin suyi fitsari, nan tayi ta fama dasu da ƙyar ta samu sukai fitsarin ta basu ruwa suka sha, ta daɗe tana lallashi kamin su koma bacci, to yanzu hankalinta kwance ta san su da tashi kuma sai asuba, sai da ta tofe su da addu'a, Bintu ma ta tofa mata, ta tofa ayatul kursiy a ko wacce kusurwa ta ɗakin kana ta fita da fitilarta a hannu.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now