Tushen ilimi.

380 43 2
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).



Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.




Wanda aikinsa ya jinkirtar da shi, dangantakarsa ba zata daukaka shi ba.


A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, wasa-wasa har an raba ramadan biyu domin yau ne aka kai azumi na sha-biyar cif!, bayan sallar asham Bintu na zaune a ɗakin Inna, tana jiranta ta gama kimtsawa su fara lakcar yau, domin dama dai-dai wannan lokacinne Inna ta ware ma Bintu ta riƙa zuwa tana mata ƙarin litittafai, ko ta bata tarihi annabawanmu da suka shuɗe, ku kuma tayi mata wa'azi mai ratsa jiki tare ɗora ta akan lamuran DUNIYA ta hanyar amfani da lafazi na fahimta da hikima.

Suma su Fadil dai ba'a barsu a baya ba domin ana masu dai-dai da fahimtar ƙwaƙwalwarsu.

Sai da Inna ta gama kaye-kayen data saba kana ta isko Bintu a ɗaki, lokacin Nabil dai ya ɓugas!, dan shi ba ruwanshi da neman faɗa da rigimar ɗan uwansa Fadil, shi kam kullum ne sai an buga yake bacci.

Bintu na kan duba littafin da Inna ta bata, ta jiyo shigowarta, suna haɗa ido ta saki murmushi cikin zaƙuwa tace "Inna yau ma dan Allah a cigaba da tarihin Annabi Sulaiman A.S, akwai daɗi sosai, Allah jiya kamar kar a tsaya".

"Aiko dai! ai tarihin annabi Sulaiman A.S akwai daɗi, Allah ya bashi mulki, mulki ba irin na kowa ba, ya bashi dukkan wani abu da kowanne irin sarki zai so samu, ya bashi sodoji, kayayyaki, aljanu, mutane, tsuntsaye, dabbobi, ilimim kimiya (science) da kuma ilimin ayyana alƙaluma (expression)".

"Lallai Allah mai iko ne akan dukkan komai, Inna mun tsaya ne a inda wata rana Annabi sulaiman yana zaune a fada, sai ga tsuntsaye sun zo kamar yadda suka saba, a kowace rana kowane irin launi da jinsin tsuntsu za su zaɓi ɗaya da zai wakilcesu, sai suje fadarsa, ranar bayan sun isa sai yaga babu jinsin tsuntsu guda ɗaya, sai yace "ya naga banga jinsi kaza na tsuntsuye ba? ko kuma bai zo bane kwata-kwata? Aiko in dai haka ne zan bashi horo mai tsanani ko kuma ma na kashe shi, in har bai faɗi ƙwaƙw-ƙwaran dalilin rashin zuwansa ba".

Ba'a daɗe ba sai ga wannan jinsin na tsuntsun ya shigo, ya iso ga annabi Sulaiman A.S yana me cewa "Nazo da labari wanda bamu san da shi ba, na zo da sahihiyar labari daga garin saba/sheba dake cikin garin Yamen, a can na gano wata mace ce ke mulka su....... a dai-dai nan kika tsaya Inna."

"Masha Allah Bintu gaskiya kina biye dani sosai, sai dai yau ba tarihi zamu yi ba domin akwai wani mahimmim abu da nake so na gaya maki, dan haka in Allah ya kai mu da rai gobe sai mu cigaba".

"To Inna Allah ya kaimu goben".

"Ameen, yau zamu tattauna ne akan tushen ilimi, babban jigo kuma maganin dukkan matsalolin DUNIYA, kamar yadda muka shafe satuttuka a baya ina koya maki sunayen Allah, har Allah yasa kika haddace su gaba ɗaya, kuma ina fata yanzu in nace ki kawo su gaba ɗaya zaki iya?".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now