The journey.

358 41 3
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎


STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.





Duhu baya gusar da Duhu: haske kawai ke yin wannan. Tsana bata gusar da tsana (kiyayya): So kawai ke yin wannan.






Tabbas kam sun bani, basu taɓa kai sha-biyun dare a waje ba, ita ma ɗin sai ranar da Inna zata haifi twins, in ta tuno cewa kuma she was with him wan can time ɗin, then she definetly knew they would be safe this time arround too, to amma wane uzuri zasu ba ma su Inna Atika, tasan Inna Atika tsab! yau kam sai ta zazzage su tas!, amman me yasa hankalinta bai tashi ba kamar yadda ya kamata ace ya tashi? wani ɓangare na zuciyarta yana gaya mata cewa she was with him, and she really enjoyed his company and so? duk ma abunda zai faru zai wuce ne.

Sai lokacin yai magana "to har an gama dinner ne?", Maryam Kam duk a tsorace take dan bata san sadda lokaci ya wuce haka ba, abunda bata sani ba kuwa? ba ita kaɗai bace bata lura da lokacin ba, gaba ɗayansu ne, kamar me shirin kuka tace "wallahi ko partyn sheɗanu suke yaci a ce sun gama, Bintu i maza ki kira mana muji".

Cikin rawar hannu ta fara latsa wayar, tama rasa wa zata kira, kawai sai ta kira Amarya, "Hello ya Ruƙai kuna ina ne?".

"Bintuu! kuna ina? yanzu nan muka dawo gida, ya akai baku iso ba har yanzu?".

Da sauri maryam ta ziro hannu ta karɓe wayar daga kunnen Bintu, da yake wayar a loudspeake ne duk suna ji, cewa tai "Ya Ruƙai gamu nan bamu samu mota bane, ki gaya mana kwatancen gidan".

"Bari in kira shi ince yaje ya ɗauko ku".

"A'a yanzu mun samu mota kwatancen gidan kawai zaki mana".

"To bari in kira shi nima ban san kwatancen ba", ba'a daɗe ba sai gashi ta ƙara kira tace "kuce National, kwanar opposite audu fari ko sauƙi fish, kuna shanyo kwanar gida na biyu by your left, gida me baƙin gate", Allah yaso Al'ameen ɗan gari ne, shi ya gane kwatancen dan haka ya jasu suka tafi, suna zuwa suka sauka da ƙyar ma suka amsa shawarmansu da yake basu.

Washegari da safe aka gudanar da walima a cikin gidan, motoci biyu suka kawo wanda zai kwashi ƴan-Mani, dan haka wajen ba zai ishesu ba, ana ta ƴan-shawarwari can daga gefe Maryam tace ma Bintu "ke Bintu, kawai ki yadda mu bi Ya Al'ameen da yace mu bishi, kina dai gani yanzu maganar yadda za'a zauna ma ake, da alamu dai sai dai ayi ƴar-goyo kuma kinsan zamu ji jiki ba kaɗan ba".

"Ni kam ki rabani, wallahi tsoro nake ji Maryam, kawai sai mu kama mu bishi? sai in ga kamar bai dace ba Allah! To tukunna ma taya zamu fara faɗa masu? taya zamu amsa tambayoyin waye shi ɗin da zai ɗauke mu? meye alaƙarmu?".

"Kefa daɗi na dake kin cika tsoro kamar farar kura, in mun bishi sace mu zai yi? kuma meye rashin dacewa anan? bayan ba ke kaɗai zaki bishi ba? ina dai daga zaman mota ne abun zai tsaya? to kuma?".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now