🔐LIFELINE💕

321 45 25
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.








Shin me nai masu suke bibiyar rayuwata?, wane ɓoyayyan abun ne yake tunkaro rayuwarmu? Kuma akan wane dalili? Game da SHI kuma, ni mai sadaukar da rayuwatace domin shi ya rayu!.
BINTU.










Sanye take da kayan makarantarta ash da fari, kayan tas-tas suke musanman fara ƙal ɗin safar ƙafarta yanda kasan yanzu ta sata domin babu alamun datti a jikinta, tana goye da jakarta tana tafiya cike da gajiya, minti-minti kuma tana share zufar dake tsatstsafo mata akan fuska kasancewar uwar ranar da ake ƙwallawa, wacce ke ƙara tafarfasa ciwon kan da ta keji, a cikin ranta take addu'ar Allah yasa ai ruwa dan an kwana biyu ma ba'a samu ruwan ba, sai zafin dake ta ƙara dafe su, dan zafin bana kam sai godiyar Allah.

Duk jikinta ba ƙwari a sanyaye take jinsa, tafiyar ita kaɗai duk ta gundireta, yau ba ƙawar tafiyar tata Lamunde sanadin ta baro makaranta ne kamin lokacin tashi, ana gama sallar azahar ta kamo hanya dan duk bata jin daɗin jikinta gashi yau ake sadakar Arba'in na Baba ɗan tsoho.

Kamar ta biya ta makarantarsu Maryam sai kuma ta fasa tuna cewa makarantarsu bama bari za'ai ta fito ba indai ba lokacin tashi ne yayi ba, kamar dai yadda suka aje, sa haɗe a gidan Naty kawai.

Yau gashi bata da asi balle ta hau abun hawa, dan haka sai kawai ta yanke hukuncin bi ta ɗan dajin da suke yanka ita da Lamunde, dan ta wajen tafi sauri, short-cut ce, kuma hanyar akwai yalwar itace wanda zasu tare mata ranar da akeyi, da wannan tunani ta juya akalar tafiyarta ta yanki wannan dajin.

Wurin cike yake da dogayen bishiyoyi wanda sukai ma ƴar siririyar hanyar da mutane ke bi ƙawanya, hakan ne yasa in ana rana wajen yake da sanyin ni'ima, a kan hanyar ne kawai ba ciyayi amman ko ina cike yake da ciyayi koraye shar, in lokacin damina ne kamar yanzu, ƙamshin ƙasar wajen kansa na dabanne.

Bata mance wancan lokutan da suna ƙanana har son bin hanyar suke in anyi ruwa saboda sui ta wasa da shimfiɗaɗɗiyar ƙasar wajen mai laushi wacce take komawa laka, haka takalmansu zasu maƙale, sui ta lalubensu a cikin lakar suna dariya, daga haka har suka maida abun wasa, sai su kusan shafe fin awa suna wasa a wajen, Allah sarki yarinta!.

A hankali ta ɗaga kanta tana kallon ɓarayinta na dama, daga inda take tsaye tana hango makeken tafkin da ya ɗan bada zurfi ƙasa, sai ka ɗan gangara zaka cin masa, murmushi tai tana tuna shima yarintar da suka aje a wajen, ba ta taɓa manta wata sallah inda wautarsu ya kaisu, wai su a dole sai sun hau kwale-kwale, dama in ba lokutan sallah ko wani sha'ani ba ba ta yadda za kaga kwale-kwale a wajen, dama wa innan lokuta ne matasa masu zaman kashe wando ke zuwa su ƙaddamar da wasan kwale-kwale don suci kuɗin yara, haka za su kawo shi yara suzo sui ta biya ana zagayawa da su cikin makeken ruwan.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now