TIME ONLY MAKE IT WORSE🤧.

344 35 4
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.

***************************************
We parted so suddenly Inna!😭,........ I want to see you very much😩, It has not been easy without you, it's really hard for me to believe you are no more🙆‍♀😭, ......i wish to drown my sorrow in a cup of chilled water, but the sorrow is getting intenser😫😫, i know life is full of twist and turns, losses and gains, but sepration is the most unbearable, expecially between parents and their children, mostly mothers, wa zai iya gaya mun taya zan iya mantawa da Inna cikin ƙanƙanin lokaci?..........
BINTU.
***************************************




"Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki kinji? kin manta dukkan mai rai sai ya mutu? yanzu haka abunda Inna tafi buƙata addu'ar kice, ba wannan kukan ba ko ɗaga hankalin da kike, ita ta riga ta tafi kuma bazata taɓa dawowa ba.

''''Bazata taɓa dawowa ba''''

''''Bazata taɓa dawowa ba!!!''''''.

Abun muji mata daɗi ne saboda ƙarshenta yayi kyau, shahada tayi, yanzu haka kin san in tana nan bazata ji daɗi ba in ta ga halin da kike ciki ko? to me yasa haka?, zaki fara bijire mata ne tun yanzu?.

Abunda nake so ki sani shine Inna ganinta ne kawai ba kya yi, amman tana kusa da zuciyarki a ko yaushe, kuma zaki iya cigaba da yawo da ita a cikin jikinki har ƙarshen rayuwarki, ko ba kiso?"

Ɗaga kai tayi alamar "eh" kana ya cigaba, "Yauwa ko kefa Teemama, ai Inna ta baki abunda zaki rayu dashi har ƙarshen rayuwarki wallahi, duk sadda kika ji kewarta addu'a zaki ta mata, shi tsarin Allah ba wanda ya isa ya shiga ko ya canja sa, abunda Allah ya ƙaddara ma bawa bai da wani iko a kansa.

Kamar yadda duk wanda ya shigo duniyarnan ba makawa sai ya barta, ta wannan hanya ɗayan dai tal!
wato mutuwa!, kowa sai ya ɗanɗane ta, fata ɗaya shine Allah yasa mudace, shine kawai" Ya Saleem ya faɗa da dukkan wani yaƙinin mai nuni da yana da buƙatar ta saurare shi, domin kwata-kwata a ƴan kwanakin nan halin da tasa kanta yana firgita shi ainun!.

Daga nan likitan wanda abokinshi ne shima yasa baki, haka sukai ta kwantar mata da hankali, musanman shi Ya Saleem da hankalinshi yafi tashi sosai dangane da lamarin nata.

A kwanaki biyu da suka wuce da likitan ke shaida mashi jininta ya hau sosai, so yai yaƙi yadda, dan daga ƙarshe har ansar spig ɗin yayi ya ƙara aunawa da kanshi, sai da ya gwada fiye da ƙirgar yatsu kamin ya yadda cewa jinin Bintu ne da gaske yakai 180/100.

Tashin hankali iya tsabarsa ya shigesa, gani yake duk wani jinin Inna kamar wata babbar amana ce a hannunsa, domin Inna shikanshi yasan uwa ce a gareshi, haihuwarshi ce kawai batai ba.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now