Tankaɗe da rairaya...

210 25 1
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).

Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.





------------------------------------------------------------

Yana daga kaffarar zunubai taimakon wanda yake cikin ƙunci, da yayewa mai baƙin ciki baƙin cikinsa.....
QueenBk.

--------------------------------------------------------------








Miƙewa tai a dai-dai lokacin da take ganin ta gama rubuta duk abinda ta sani, sai da ta ƙare ma inda ta rubuta sunanta kallo kana taje tai submitting jarabawarta ta ƙarshe ta aji biyar, fita tai wajen ajin ta samu ƙasan wata bishiya ta zauna tana jiran Lamunde ta fito su tafi, zaman kaɗaicin da tai a wajen ya bata damar shiga duniyar tunani.

Saura kwana ashirin da biyu cif! daga yau zuwa bikinta, hakan na nufin a cikin kwanakin masu zuwa zata bar garin nan, zata bar gida kuma kenan ko? to in haka ne taya zata cika alƙawarin da ta ɗaukar ma Inna?.

"Ina so ki natsu Bintu ki san rayuwa, kece babba, ke ya kamata ki ɗaura ƙannenki akan hanya, kuma ke ya kamata ki fisu haƙuri da juriya, akkan dukkan wani sauyi da zaku samu na rayuwa...".

Wannan maganganun na Inna su suka shiga dawo mata tas! a cikin kanta, to in har tai auren ta tafi taya zata kula da su kenan? To ko dai fasa auren zata yi ne? amman zata iya fasa auren Deey kuwa? dama dai wani ne bashi ba! To ma in har ita ta iya fasawa shi zai fasa ne? Tasan abunda baze taɓa yuwuwa ba kenan, don tasan sun kai matakin da, kamar yadda mutum baze iya rayuwa ba tare da iska ba to su ma baza su iya rayuwa ba tare da juna ba.

Ta tuna lokacin da Yakumbo ta haɗo mata wasu sabulan wanka da mayukan shafawa tace ta riƙa amfani dasu kamin zuwa biki zata fito tar-tar tana sheƙi, take tace mata ita fa ta fasa auren, tas! tana iya tuna yadda fuskar Yakumbo ta hasko tashin hankali matuƙa tana kallonta a ruɗe ta shiga tambayarta akan wane dalili zata ce ta fasa?, sannan kuma da sauri ta jawota suka zauna, bayan ta tallafi fuskarta a hannunta ta cigaba da faɗin,

"Ke baki san gata ne Allah ya maki ba da ya haɗaki da mutum kamar Al'meen?, yana sonki yana kuma tausayinki, a iya nan ma in aka tsaya mun san ze riƙe ki da amana balle kuma mutum ne shi da ya cika ta ko wane ɓangare da ake son mijin aure ya kai, gashi mutumin kirki dangin shi ma mutanen kirki, kiga yadda suke sonki tun ma kan ki shiga, kin ga alamun zakije kiyi zaman wuya a gidansa ne?.

DUNIYA MAKARANTA CE.Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz