Ƴan-biyu kyautar Allah!.

535 59 9
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎


STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).



Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))


SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.




😘😘😘Am dedicating this page to you my BFF, Asma'u Haruna Mamuda, my only Umaima in the whole Gombe state.😁😁😁

😍😍When I think about u as a friend, I can only thank u for being the perfect example of friendship.🤩
All d memories we shared are all locked in my diary, so not any is to be forgoten, d best of all is how we played under the sky when ever it rained🤣🤣 like kids, and how we sqaut flat on the ground when ever d storm screems, the arabic-paper-go in d library😂😂, our tsokana remember "laugfy face" 😂😂 oh God i can't resist this memories, last but not the least "gudun aljanin maƙyal-ƙyato" 🤣🤣 oh Allah i really love you my ƙawar arziƙi, this page is urs nd only urs, stay safe pls.♥♥ missing yer😥.



Idan ka sami iko akan maƙiyin ka, to ka sanya afuwa gare shi ta zama godiya ga Allah akan wannan iko da ka samu a kansa.





Matashin saurayi ne me kimanin shekaru 28 a duniya kwance cikin wata mota baƙa mai ƙirar Benz E200, kwantar da driver seat ɗin yayi har yana taɓo kujerun bayan, dan haka ne yake kwance comfortably ba tare da ya takura ba, yana shaƙar baccinsa, kamar a cikin mafarki ne yake jin shash-sheƙar kuka, cikin baccin yake ta ƙara toshe kunnuwansa, dan in a mafarki ne ya ƙagu ya daina jin sautin kukan, in ma a zahiri ne baya son duniyar waje ta jawo shi daga ta bacci ya juyo wannan kukan.

Sai dai bai ci nasara ba, dan sautin kukan na ƙaruwa ya haddasa mashi farkawa.

Shin wai da gaske kukan da ya keji dama ba'a mafarki bane? a zahiri ne kenan? nan ya ƙara baza kunnensa sosai tare da ɗan rage gilashin gaban motar, aiko ya faɗa dai-dai a zahirin ne!, to amman waye zai zo waje cikin talatai-nin daren nan ya rinƙa kuka? anya kuwa akwai mutumin da zai yi haka? ai yana tsammanin ko wane mutum dai, da dare yayi zai yi gida, in ma baida gida to tabbas za'a samu yana da mafaka.

Dan haka yayi tunanin kodai ƴa-ƴan aljanu ne ke kuka? wannan tunanin kawai ya haddasa mashi firgici, da sauri ya zuge glass ɗin da ya buɗe tare da ƙara ƙarfin na'urar Ac dake ta aikin sanyaya cikin motar, kana ya koma ya kwanta lamo yana ta karanto addu'oin da suka zo bakinsa.

Sai dai ina hankalin shi ya kasa tsayuwa waje ɗaya, shi ba ga baccin ba dan fin-tin-kau ya ƙaura cewa idanunshi, shi ba ga kwanciyar hankali ba dan gaba ɗaya gunjin kukan da yake jiyowa ya hana zuciyar shi sakat.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now