The Message.

294 38 2
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).


Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.





SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.









Duniya! Zamanta ba a nemi lahira ba kamar kasuwanci ne da ba riba a cikinsa.........
BINTU









"Hmmm! Ni na rasa ma ta ina zan fara baku labari Allah!" Lamunde ta faɗa lokacin da suke fitowa daga makarantar islamiya ta safe tahfiz da ake duk ranakun hutu, wato asabar da lahadi ƙarfe takwas na safe suke zuwa su tashi ɗaya, sai kuma su koma ta yanma ƙarfe huɗu wacce suke tashi biyar da rabi.

Dukkansu sanye suke da farare ƙal ɗin uniform ɗin makarantar suna tafiya a tsari cike da ƙasaita irin ta cikakkun mata masu ji da kansu.

"Ta ina zaki fara dama in ba farko ba?" cewar Maryam, yayinda Bintu tai shiru tana saurarensu dan ita har yanzu tana cikin alhinin rashin maigidanta a kusa da ita, yau sati kusan biyu da tafiyarsa inda ba'a dawowa sai dai a tadda shi, amman kullum mutuwarsa sabuwa take koma mata musanman in taje gidan ta taras Naty ce kawai a ciki, sai wata jikar ƙanwarta Indo, yarinya ƴar shekara bakwai da aka kawo mata domin ta rinƙa ɗebe mata kewa.

A hankali Lamunde ta fara basu labari "kun san meye? tun zuwa na Kano hutun nan da naje naso na baku labarin wani guy, sai dai dalilin shiruna shine ganin abubuwa basu kankama ba, ban gama gane inda ya dosa bane kar nazo na baku ƙanzon kurege.

Dama in naje Kanon gidan Momi, Aunty Kilishi wacce suke same father da Baba anan nake sauka, shi kuma guy ɗin sunanshi Abdul Samad ɗan mijinta ne wanda take riƙonshi tun yana ƙanƙani, shi Ya Abudul-Samadun soja ne, kusan ma ni zance a da ban sanshi ba sai labarinshi.

Dan kusan lokuta in naje gidan yana wajen aikinsa, sai wannan hutun da naje na idda shi a gida, ni daga farko ma dana fara ganinshi Allah tsoro yake bani, saboda yadda yake da ƙira irinta zaratan maza masu yawan motsa jikinsu, gani nake kamar da ya kaimun duka ko bangaza zan tashi aiki.

Sai dai a hankali na gane shi mutum ne mai fara'a da barkwanci sosai, duk da a lukuta da dama in ya ɗaure zaka rantse baya dariya, musanman in ka ganshi cikin kakinsa na sodoji yayi shirin zuwa aiki, baza kaga alamun wasa a tattare da fuskarshi ba.

Inaga jinin mune ya haɗu, dan tun ranar da ya ƙyallara ido ya ganni a cikin gidansu shikenan kashi na ya bushe, zai ta jana da labari da zolaya wata ran har sai ya sani ƙwalla saboda yadda yake zolayata kuma ya maida abu kamar da gaske, da ya lura bana so shine ya samu abin tsokanata.

A rashin sani na ashe shi tun lakocin da ya fara ɗora idanunshi a kaina ya sallama yayi matar aure a cewar shi domin wai duk yadda yake mafarkin matar shi ta kasance na kai har na wuce, shi yana abunshi a ɓoye ni ban sani ba.

In taƙaice maku labari ranar da ya faɗa mun naji tsoron maganar sosai, ranar yaje ɗauko ni daga Wudil wajen Inna wuro kakata, a ranar ya fayyace mun, ganin yadda na firgita da maganar sai yace ba dole zai mun ba naje nai shawara da zuciyata da kuma ubangijina.

DUNIYA MAKARANTA CE.Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang