Yakumbo

636 62 5
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎



STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).



Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.



🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))


SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.



Ƙarfe biyu mutan Abuja suka iso, su Aunty Naseebah, matar kawu Sulaimam (ƙanin Inna), da gudu Bintu da Maryam suka tarbo su, suna faɗin "oyoyo ga su Aunty Naseey".

Bintu ta karɓe Amir hannun Aunty Naseba, ita kuma Maryam taja Tatus gefe, yarinya ƴar shekara huɗu amman akwai tsabar iyayi da son gayu, itama Fatima sunanta suke ce mata Tatus amma anyi ruwan kyau a yarinyar nan kar kuso ku ganta, ko maganarta cikin yanga take, gaskiya nan gaba ƴan matancinta akwai kallo, layin su ɗaya da Bahijjah shi yasa tasu tazo ɗaya gasu sa'annin juna, suna haɗewa kuwa suka cigaba da iyayinsu.

Taran suna dai yayi armashi ƴan-biyu kam da suka ci sunan Fadil da Nabil, sunyi goshi fiye da zaton Inna, Matan gidan ko duk yadda suka so aji kunya abun ya faskara, don zuwa suka riƙayi karɓar abinci wai ma baƙin su kuma ba'a hanasu ba akai ta basu, dama manufar su abincin ya ƙare yadda za'aji kunya, sai dai basu san sunyi a banza ba domin su Inna sun shirya ma sha'anin da kyau, tun ba yau ba dama suke ta tarin sha'anin, anyi abinci kala-kala sai aka bar wasu a gidan Yakumbo, sai abincin nan yayi ƙasa sai a ɗauko nacan, ga abincin Allah ya samai albarka, ga wasu mutanen ma sun kakkawo, Naty ma ba'a barta baya ba domin lafiyayyen sinasir da alala ta shiryo ta aiko gidan sunan.

Aiko sun sha mamaki dan da sunce a zuba abinci kam ba gargada sai suga an ɗauko wani sabon nau'i na abincin, har ma sai sun zaɓa wanda suke so, Ya Gwal-Gwal ma duk iya handamarta tayi ta gama, dan ita jida tai tayi tana tulawa a ɗaki, tunda babu a house ta aje gobe da jibi taci mai daɗi, wanda daga gani ma asara ce zata tafka tunda bata da fridge ƙarshenta ma ya lalace ta zubar.

Allah ya rufa masu asiri addu'ar da Inna tai tayi kamin suna Allah ya karɓa, Abinci kam har almajirai aka rinƙa raba mawa banda wanda ya kwana aka ɗunɗuma.
A safiyar ne haƙar ƴan gidan ta cin ma ruwa dan sai da sukai kaca-kaca akan naman suna.

Abun da ya faru tunda aka gama yan-yankawa, su Yakumbo da sauran dangin sukai ta haƙilon soyawa ba wacce ta fito a matan gidan tayo, sai ma kujerar habaici da suka dasa, dama Yakumbo ba daga nan ba, duk tana jin habaicin da suke saki akansu bata ce komai ba, su ka gama suyarsu dama suna yi tana kwasa tana kaiwa ɗayan ɗakin Inna da ba'a cika amfani da shi ba tana kullewa, ana gamawa ta tattara ta maida can gaba ɗaya ta kulle.
Ta koma can ɗayan ɗakin ta kwanta tana jiran su, ilae ko sai ga aiken yara nan, wai ance a raba nama a basu nasu, dama jira take da sauri ta tashi ta dubi ɗan aiken "Kaje kace masu wai naman yayi ƙafa su bishi su kamo!".

Yaron yace "iye?" cikin rashin fahimta.

"Kai dai kawai kaje ka faɗa masu haka".

Inna tace "kinga murja nifa ban san rigima ki raba nama ki basu kasonsu, me ar tsiya me ar nama?".

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now