Back to Abuja.

272 29 7
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎




STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).




Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.





SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.






Ya kai ɗan adam, idan ka ga ubangijinka yana bibiyar ni'imarsa a gareka kana saɓa masa, to ka kiyaye shi.





Hannu tasa ta zuge glass ɗin side ɗinta, taɗan leƙa kanta ta waje, tana kallon Zuma Rock tana shaƙar iskar Abuja da tai missing one year back, taɓ! abun kamar a shirin film ko a labarin littafi, kamar jiya ne suka bar Abuja amman har sunyi shekara ɗaya cif! kenan rabansu da Abuja.

Tana iya tuno wancan komawar da tayi gida, sai da tai tozali da Inna da twins ta tabbatar lallai tayi missing gida, haka ta rungume Inna tana murna, twins kam rungumesu tai tayi ɗaya bayan ɗaya tana ganin yadda suka ƙara girma da wayau wata shidan kawai da bata gida, yanzu an zama big boys shekarunsu huɗu cif-cif, wanda ya kama dai dai shekaru huɗu kenan da haɗuwarsu da Al'ameen.

Lokacin da suka haɗu da Baba ya nuna murnar ganinta ƙarara, duk sai taji kunya ta kamata, dan tunda ta tafi bata taɓa kiransa domin ta gaishe shi ba, gaskiya kam bata kyauta ba, bata cika ƴa ba, Ya Saleem na gida ranar wuni sukai suna fira dashi tana bashi labarin Abuja, basu ƙara tabbatarwa sunyi missing gida ba sai washegari da Maryam tazo suka je gidan Naty, suka tarar Baba ɗan tsoho ba lafiya ashe ya ɗan kwana biyu yana fama da jikin nasa, ya kwanta ya tashi, amman yanzu jikin nashi alhamdullilah.

Lokacin da suka isa gidansu Karime kuwa abun ba acewa komai tsalle sukai tayi kamar wasu ƙananan yara, suna rungume-rungumen juna daga baya aka baje kolin labarai ana dariya sun kawo mata tsarabar kaya da yawa, kamar yadda suma suka sha tsarabar Kano.

A makaranta kuwa abun kallo da sha'awa suka zama, kowa so yake ya raɓe su, dan ganin yadda suka goge suka waye, ga manyan wayoyi a hannunsu, haka da anyi break za aje a yayyaɓe su ana ganin waya, musamman hoton da aka ga sunyi da shugaban ƙasa ya kankaro masu girma da yawa haka za'ai ta sakin baki ana kallonsu idan suna wasu abubuwa ko suna faɗin wasu abubuwan.

Tuni sun ɗora Karime a system ɗin gayu, yanzu ba ranar da zasu fita ba sui guzurin samari kala-kala ba, da wa'inda suka kai su kula da wanda ma basu kai ba, duk bakinsu ɗaya cewa suke su sun riga da sun tsaida miji, in aka tashi wani ɗan ƙayattacen biki kuwa su ake kira suyi kwalliya da yake Maryam tafi ƙwarewa sai tama amarya ita kuma Bintu tai ma ƙawayen Amarya, da haka suke samun ƴan kuɗaɗensu, suna ɗinkuna na kece raini, Sabulai da sauran abubuwan kuwa Inoninsu suka koya mawa, haka Inna da yakumbo suka haɗa kai da gwiwa suna yi suna siyarwa aiko sai Allah yasa ma abun albarka, ba ƙaramin samu suke ba abu ya cigaba har wajen gari suna fidda shi.

Ƴan gidansu Bintu kuwa ba ƙaramin baƙin ciki da wannan samu suke ba, dan dama koda Bintu ta dawo ta tarar komai ya canja amman banda lamarin gidansu, dan in ba cewa zatai wasu abubuwan sun ƙara taɓarɓarewa ba, ba zata ce wani abun ya gyaru ba, abun dai sai Allah, su Ya Gwal-Gwal an ƙara tsufa amman sai kauɗi da kwaɗayi suka ƙaru, ga masifa yanzu kowa shanta yake.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now