Burning Desire.

288 33 6
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

DUNIYA MAKARANTA CE!.

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎


STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).






Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara ƙasa suka gina gida mai kyau sai su sa ƙafa su rusa.






SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.






Kimar mutum tana daidai gwargwadon himmarsa, gaskiyarsa kuma tana daidai mutuncinsa, jarumtakarsa tana daidai gwargwadon karfinsa, kamewarsa tana daidai gwargwadon kishinsa.
BINTU.






Y

au asabar, Kawu Sulaiman na gida kuma zai yi manyan mahinman baƙi, dan haka tunda asuba suka shiga aikin gyaran gidan, bayan sun gama suka turara shi da turarurrukan wuta masu ƙamshi, daga nan suka ɗunguma kitchen suka shiga taya Aunty Naseey girke-girken da take, sai tara dai-dai suka kammala komai suka jera, ba'a daɗe ba ko sai ga baƙin sun iso, sai da suka gaishe su kana suka wuce ɗaki.

Suna kan gyaran ɗakinsu Bintu tace "Mairo yau ne fa Al'ameen yace zai kai ni na gano gida, ki shirya muje ki rakani dan Allah ban san zuwa ni kaɗai".

"Haka kawai gayyar soɗi, ni ba'a gayyace ni ba sai kawai na kama na biki, ƙarshe ku barni mai take maku baya!".

Dariya tai tace "ke fa daɗi na dake iyayinki yayi yawa sai kace baku saba dashi ba meye ne in kin bini?".

"Abu ne mana babba, ke da bakinki kika ce mun saba to me yasa da ya tashi cewa ki shirya kuje ganin gidan ku, yasan dani kuma mun saba ɗin baice, Maryam ma ta shirya muje ba?".

"Kee Allah ko cewa yai mu shirya mu biyu, to bari kiji hada ma El-mansoor za'a".

"To kun faɗo da baku gaya mun da wuri ba, dan ni kam ma yau AP gareni, Adeel zai kai ni Musieum, kuma mun daɗe muna sa lokaci, kin san su ba lokaci garesu sosai ba, jiya yayi call to yau off yake, bari ma kiga yanzu nai sauri nai wanka kamin yazo" ta tashi tana murguɗa ma Bintu ƙugu.

Bintu ta harareta tace "kuje ma gaba da Musium".

Lokacin Maryam har ta shige bayi ta leƙo kai tace "ai har can zamu dama" ta shige tana dariya ita ma Bintu dariya tai tana faɗin "Allah ya shiryeki Mairo".

Bayan sallar Azahar yace zai zo ya ɗauketa dan haka suna gama kalaci ta wuce kitchen ta fara hidimar ɗora abincin rana, 11:30 Maryam ta tafi, ita kuma sai da ta gama kammala komai tsab kana ta wuce ta sheƙo wanka, tana fitowa dai-dai lokacin an tada azahar sai ta sauke farali sannan ta shiga shiryawa.

Har tasa wasu skirt da riga na atamfa sai taji skirt ɗin ya matseta sosai gashi kayan sun mata kyau matuƙa, hakanan ta cire sai ta sa wata doguwar rigar atamfa mai ruwan hoda da zanen ruwan ƙasa mai duhu rigar ta buɗe daga ƙasa sosai, tai mata kyau ƙwarai, bata ɗaura kallabi ba sai ta kawo gyalanta ta aza bisa kai ta lulluɓa shi, da yake gyalan da ɗan girma sai ya kawo mata har wajen ƙugu.

DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now