Gabatarwa.

2.6K 93 5
                                    

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌍🌍🌍🌏🌎🌎🌎🌎🌎🌎

*DUNIYA MAKARANTA CE.*

🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎🌎

STORY & WRITTEN BY:
BILKISU ALIYU KANKIA
(👸QUEEN BK👸).



Duniya Labari,

Duniya Makaranta,

Duniya Kasuwa,

Duniya wasan gidan yara idan suka tara kasa suka gina gida mai kyau sai su sa kafa su rusa.



GABATARWA

Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai.


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah a bisa ni'imominsa na bayyane da na ɓoye, daɗaɗɗu da fararru. Kuma tsira da aminci su tabbata ga Annabinsa kuma Manzonsa, Muhammadu da alayensa da sahabbansa.

Bayan haka wannan taƙaitaccen littafi ne da yake tattaruwa a bisa duniyarmu a taƙaice dai rayuwa ta ɗan adam da abunda ta ƙunsa duk da labari ne da ya ta'allaƙa akan mutum guda sai nasabobi da sauran characters ɗin suke da shi akan main character ɗin, amman duk da haka ya ƙunsa abubuwa da yawa na hikimomin rayuwar ɗan adam kama daga gidansa, iyayensa, iyalansa, da sauran mutane haɗe da bambance-bambance ra'ayoyi da zukatan mutane harma da sauran abubuwa da yawa wanda insha Allah gaba a cikin littafin zaku fuskanta, labari ne na wata baiwar Allah wanda rayuwarta ke ƙunshe da tulin darussa bi ma'ana abun koyi, bazan tsunduma wajen faɗa maku ra'ayi, dalili da kuma babban maƙasudin rubuta wannan littafin ba sai ubangiji Allah mai iko ya bani ikon kawo maku ƙarshen labarin nan da izininsa kamar yadda ya bani dama da ikon fara rubuta maku shi.

Abu na biyu kuma littafina na "SARAUNIYA BILƘIS"  da na fara rubuto maku labarinshi zan jingine shi a gefe kasancewar akwai babban saƙo insha Allah da na ke so na isar maku ta wannan labarin me taken DUNIYA MAKARANTA CE   amman duk da haka ba ina nufin zan rataye labarin sarauniya bilƙis gaba ɗaya ba, a'a insha Allah in Allah ya bani iko zanna maku typing ɗinsa amman once in a while, abunda nake so na isar shine: cikin taƙaitaccen lokacina zan fi emphasizing akan wannan book ɗin shi kuma ɗayan jefi jefi zanna updating ɗinshi da fatan hakan ya tafi da ra'ayoyinku.

MAFIFICIN GODIYA.

Mafificin godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki, ubangijin talikai, mahallicin sammai da ƙassai, me sanin abunda ke ɓoye da abunda ke sarari, shine mafi cika alƙawari wanda ya umarce mu da bauta masa muyi halin kirki na gari anan duniya, muna roƙonshi da ya ɗora mu a hanya wacce itace madaidaiciya.

MUƊUGU UBAN TAFIYA.

Masoya na abun alfahari na a kullum zan zamto mai sako ku a gaba gaba domin bana tuya na manta da albasa, domin haka ne na kasance me maku fatan alkhairi a dukkanin al'amuranku na duniya da lahira, ina roƙan Allah ya sa maku fitila mai haske a duhun rayuwarku, ya kare manku a iya tsayin rayuwarku ya albarkaceku da zuri'arku baki ɗaya, na gode na gode da ƙaunarku a gareni, ubangiji Allah ya haɗa fuskojin mu a Aljannatul firdaus.

FAƊAKARWA

Ƙirƙira tun ma ba ta labari irin na zube ba, aba ce wacce ta ke ƙulluwa da zururruka masu kishiyar juna ta fuskar halaye da ɗabi'u waɗanda sukan sha bam bam daga wannan mutum zuwa ga wancan mutum, daga wannan gida zuwa ga wancan gida, daga wannan gari zuwa ga wancan gari, daga wannan ƙabila zuwa ga wancan ƙabila, daga wannan al'umma zuwa ga wancam al'umma.
Don haka labarin dake cikin wannan littafin ƙagaggen labari ne don faɗakarwa da nishaɗantar da mai karatu saboda haka duk wanda wani hali a cikin wannan labarin ya yi kamanceceniya da nasa/nata, to arashi ne aka samu, kamar yadda na cikin labarin ba zai ce wani mutum da yake a wajen labarin ya ɗaukar masa hali ba to shima wanda yake waje kada yace an aikata halinsa, idan an samu kamanceceniya arashi ne aka samu, dan haka sai a guji yin zargi ko zaton cewa anyi wannan labarin ne domin a musgunawa wani ko wasu, haka ma sunaye da garuruwan da ke cikin wannan labarin duk an sane kawai don ƙayata labarin.

GARGAƊI

Wannan litafin da labarin da ya ƙunsa duk mallakar marubuciya ne, ban yarda wani ko wata ya juya wannan littafin ta kowacce irin siga ba sai da aikakken izinin marubuciya a rabuce don haka a kiyaye, mubi doka mu zauna lafiya!.

DAGA MARUBUCIYAR:

ZAN SOKA A HAKA.
SARAUNIYA BILƘIS.
DUNIYA MAKARANTA.

SANARWA.

Banyi alƙawarin yi maku typing duk rana ba, amman insha Allah zanna muskutawa ina maku akan kari.

SADAUKARWA

NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GABA ƊAYAN SHI GA MAHAIFIYATA ABUN ALFAHARINA, WACCE TAKE ITACE SILLAR KO WANE MATSAYI DA MATAKI DA NAKE TUNƘAHO KO NA TAKA A RAYUWATA, HAR KULLUM INA ƘARA GODE MA ALLAH DA SAMUNTA A MATSAYIN MAHAIFIYA KUMA ABUN KOYI A GARENI, UBANGIJI ALLAH YA ƘARA JA DA ZAMANINKI UMMAHNA YA KARE MANA KE DA KAREWARSA.


DUNIYA MAKARANTA CE.Where stories live. Discover now