Chapter 2

2.2K 129 1
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting love story  2017)

By Aisha Muhammad   ( Mzz Daddy 💋 )

    *Ina mai baku  hakuri  akan  wani  kuskure  da  akasamu  a  page  one , zakuga  wani  wurin  na  rubuta  Islah  instead  of  Zynah  Dan  Allah   kuyi  hakuri  typing  error  ne,  kuma kaman  yanda  na  fada  muku  ni sabuwar  writer ce  shiyasa  such  mistake  are  likely  to  happen.  Tnx  for  understanding  nd d cooperation   ILYSM* ❤

QUOTE:- Don't  interrupt, even if u need to put ur hands over ur mouth to stop urself. Learn  to  fight  fairly. No name calling. Don't  make  threats, Apologise  wen u knw u should. If u'ar  too  angry  to  really  listen, stop ! go into another  room, take  space  for  urself, breath nd calm down.  
Remember : ur partner  is nt d enemy.

  _I dedicate dis page to my one only sister *Halima ( limsyberry)*_

            0⃣2⃣

  *ASALINSU*

        Alhaji Sani Mai Dala da Hajiya Hasiya sune iyayen  Alhaji  Muhammad  Sani  Mai Dala. Wanda shine da daya tilo agurinsu, saboda  haka  suka  dauki  son  duniya  suka  daura masa, baya  taba neman  abu  gurin  iyayen  shi  ya  rasa  dukda ba  wani  arziki  bane  dasu  ba  saidai  muce  rufa asirin  Allah. Alhaji  Sani  yasamu  lakabi da Mai Dala ne saboda tun yana yaro  beda  burin  da ya wuce inya  girma  yazama  mai  kudin da Naira ma baze dinga  rikesu  ba  sai  Dala, saboda  haka  abokansa  suka  sa  mashi  Mai  Dala  wanda  idan  suka  kirashi  da  sunan  wani  dadi  yakeji  kaman  ance  ga  kujeran  makka  nabaka.

     Haka sunan ya bishi dukda  Allah  bai  nufa  zaiyi  irin  wanan  kudin ba. Alhaji  Sani  ya  kasance da kasuwa inda yake siye  da siyarwa a  cikin  garin  kano  wanda  nan  ne  garinsu  kuma  tushensu. Cikin  ikon  Allah  kasuwan  cinsa  ya  fara  bunkasa  har  yana  tunanin  fara  fita  gari  gari  saro  kaya  amma  Allah  bai nufa  ba  saboda  wani  mummunan  hatsari  daya  samu akan wani  bridge  wanda  nan  take  yace ga garinmu rai yayi  halinsa (saidai  muce  Allah  ya jika shi  da rahama Ameen). 

       En uwa da abokan  arziki ba wanda baiji  mutuwan  bawan  Allahn nan  ba saboda mutum ne shi mai son jama'a da barkwanci.  Bayan anyi  arbain  aka  raba gado inda tilon  danshi  wato Muhammad   ya tashi  da kusan duka abunda  mahaifinshi  ya bari inda cikin hikima da dabara shima  yaci  gaba  da  gudanar  da  kasuwancin  mahaifinshi.

       Cikin ikon Allah  komai yazo mishi da sauki  inda kasuwancin  sa yasamu  karbuwa  har yarafa  fita gari gari kaman Lagos da Port Harcourt, ganin kasuwancin  ya bunkasa  sosai  yasa  ya  samu  yaran  aiki  yasa  a  karkashin  sa  wanda  duk  wata  yana biyansu  albashi  mai  tsoka.  Kasuwanci ya karbeshi  sosai  inda  ayanzu har  kasashen  ketare  yana  zuwa  amma  iyakanshi  Africa .

      Cikin  yawon  kasuwancin  sa ne yahadu  da  matarsa  wato  mahaifiyar  *ZYNAH* a Ethiopia  inda  yaje  wani  business  meeting  daya  last for one month, toh a dan zaman da yayi achan ya hadu da ita a wani  restaurant  dinda yake  zuwa cin abinci wanda iyayen  tane  masu restaurant  din amma ita ke managing  din wurin. Tun zuwanshi  na farko  ya hadu  da ita  wanda  nan  take  yanemi  nutsuwarsa  ya rasa . Da haka ya koma hotel dinda ya kama amma yakasa  tabka  komai  sai tunanin  kyakyawar  fuskar  budurwar  da  yagani  a restaurant  yakeyi. 

A haka ya wuni ya kwana ranan  suku suku  dashi, washegari  yana  gama  abunda  yakeyi  ya  koma  restaurant  din nan yasameta  yafada  mata abunda  ke tafe dashi  wanda  hannu  bibbiyu  ta karba  tayinshi  suka  sasanta  tsakaninsu , kafin  ya koma  Nigeria  sukaje  wurin  iyayenta da  maganan wanda  da kyar  da tsidin  goshi  suka  yarda dan basa so  ýarsu  tayi  nisa  dasu. Da haka ya dawo gida ransa fari tas, yana dawowa  yama  mahaifiyarsa  maganan  inda  ba  bata lokaci taje wurin  dangin  mahaifinshi  da maganan suma suka amince  ya biya ma  en uwan mahaifinshi  uku  kudin  jirgi  dashi  hudu  akaje   aka  nema mai  auren  Aisha masoyiyarsa inda cikin  wata  biyu  akayi  aurensu  aka  bashi matarsa  sukazo  gida  Nigeria  inda  ya  ajiyeta  a gidan mahaifiyarshi  kafin  ya kammala  ginin da yakeyi  a Lagos .

      Ya kammala gininsa  yanemi mahaifiyarsa  tabisu  su tare tare amma fir  taki  wai ita bazata bar gidan  da  mijinta yagina  ta gumisa  ba, ba yanda suka iya haka suka barta tare da samu mata mai aikin da zata dinga taimaka mata. Da haka suka tare shida  matarsa  inda suke zaune cike da soyyaya , amince , yarda ,  da kuma girmama juna . Sunyi shekara  uku  ba haihuwa amma ba wanda ya taba jinkansu  haka mahaifiyarsa  ma bata damu ba saboda tasan cewa Allah  ne mai bayarwa  , a shekara na ukun  ne ta samu ciki Wanda cikin  ikon  Allah  cikin na cika wata tara tahaifi  ýarta mace kyakyawa  son kuwa  kin Wanda yarasa , ranan suna yarinya  taci  sunan  mahaifiyar  Alhaji  Muhammad  Mai Dala wato Hasiya amma ana kiranta  da *ZYNAH*( abu mai  kyau in other words kyakyawa) , tun daga lokacin Alhaji Muhammad  ya dauki  son duniya  ya dorawa ýarsa saboda Mai sunan mamansa ce kuma tana kama da matar sa.

      Tun lokacin basu kara haihuwa  ba sai bayan wani shekara ukun sannan suka sake samun mace inda yarinya  taci sunan  Mahaifiyar  Aisha Wato Maryam amma suna kiranta  da *ISLAM*(Peace) .Tun daga kanta haihuwa  ya tsaya  ma Aisha saboda  haka  suka  dauki  son  duniya  suka  dura  masu  amma mahaifinsu  yafison  *ZYNAH* kuma agaban  kowa  nunawa yakeyi  Wanda hakan  yasa *ISLAM* bata  sakewa  dashi  sosai  tafi  sabawa  da  mahaifiyar  ta , dukda yanda  yake  nunamusu  banbanci  na bakanta  mata rai amma bata  taba  nunawa  ba .

                          Wannan kenan

Back to story  line............

   *Karku gaji  da biyoni  saboda akai  abun tausayi , al'ajabi , kunya da kiyayya  a cikin  wannan  novel din.*

       _Keep following  so u won't  miss_

     *Mzz Daddy💋* ✍🏻✍🏻

ZYNAHWhere stories live. Discover now