Chapter 59

1.1K 74 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻



              *ZYNAH*


(An Interesting Luv Story 2017)


By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)


*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*


QUOTE:-"Sometimes the strongest people are the ones who love beyond all faults, cry behind closed doors, and fight battles that nobody knows."


               5⃣9⃣

     Senator Usman ne ya shigo station din ranshi a bace, direct DPO's office ya nufa, nan ya tarar dasu Abba zazzaune suna tattauna maganan, ko kallonsu beyi ba yaja kujera ya zauna yace "Mr DPO, nazo bailing din innocent son dina", gaba dayansu kallonshi sukeyi Daddy yace " bai dace ace ka kare danka akan laifin da shida kanshi ya cewar amsa yayi ba", tasowa senator yayi cikin bacin rai yace "karka gayamun ba dadi, ance maka bansan dana bane, yaron da ko sauro be iya kashewa ne zeyi kidnapping din yarinya har yayi attempting raping dinta", shiru Daddy yayi dan yaga wannan baze kwantar da hankalinshi su fuskanci juna ba, DPO yace "senator Usman, ina so kasani cewa munkama danka dumu dumu acikin wannan kidnapping din, infact shine ma leader, kuma yanada gangsters daya tara wanda shine boss dinsu se abunda yace shi sukeyi", nan ya tada daru yace shi sam be yarda ba danshi bazeyi haka ba, ba musu DPO yasa aka shigo mishi da KB a gaban mahaifinshi ya maimaita abunda ya fada dazun, senator seda yayi shiru na minti biyu sannan yace " Kabiru dama haka kake bansani, ansha kawo min korafin ka amma bana yarda Ashe gaskiya ne, yanzu ka kyautawa kanka kenan, kana lalata yayan mutane kana batan suna a gari, Allah ya wadar wannan hali naka, kaji kunya Kabiru, yanzu gashi seda nazo na tsaya takarar Governor ka shiga hannu salon ka batamin reputation dina", shiru KB yayi kala bece ba, DPO yace a mayar dashi cell aka mayar dashi sannan senator yayi kasa da murya yace "DPO dan Allah ka taimaka maganar nan ya tsaya a nan kawai, wlh ko nawa kakeso zan baka", DPO yace shi be san zancen ba se ya kai magana kotu saboda a yanke mai hukunci daidai laifinshi, ba yanda senator beyi ba dan DPO ya hakura amma ya kiya dole ya tashi ya fita rai a bace, yana fita Daddy yace " toh yanzu ya zamuyi da wannan yarinyar", DPO yace "kuje, zamuyi mata horo na kwana uku bayan nan kuzu kuyi bailing din ta",godiya suka mishi duk da ba haka suka so ba sannan suka fito suka koma asibitin.


     *ZYNAH* ba ita ta tashi ba seda tayi 30min tana bacci har lokacin *ASHRAH* na tsaye a kanta, ba yanda su Ummi basuyi dashi ba akan yaje gida yayi wanka yaci abinci sannan ya dawo amma ya kiya, a kan idonshi ta farfado tun tana ganin dishi dishi har ta samo ganin sosai wanda fuskan masoyinta ta fara harba dashi, murmushi yayi mata, ita kuma cikin karfin hali tace "Mine", se kuma hawaye sharrrr a fuskan ta, hannu yasa ya goge mata hawayen tareda girgiza mata kai alamun kartayi kuka sannan yace " *DAMSEL* u ar safe nw, ba abunda ze sameki kuma se alhairi, i promise to always b here for u, kinji", kada mishi kai tayi sannan da taimakonshi ta tashi ta zauna tareda rike kanta, doctor ne ya shigo yace "dama nasan yanzu zata tashi", su Momsie ne suka shigo doctor yace a bata abinci taci yana zuwa, yana fita Ummi tace " *ASHRAF* tashi kaida Basma kuje gida in kayi wanka seku dauko mata kayan da zata sa ku dawo", ba musu ya tashi suka tafi, itakuma *ZYNAH* Minal ce taje ta siyo mata sabon brush da taimakonta ta wanke baki sannan aka zuba mata abinci, shinkafa da miya se romon cow tail da shayi me kauri, sosai taci abincin har ta basu mamaki dan duk sunsan bata cin abinci sosai, tana gamawa doctor yazo yabata magani tasha sannan ta shiga toilet tayi wanka, se a lokacin ta dan ji dama dama, ko kafin ta fito har su *ASHRAF* sun dawo saboda haka kayan da suka kawo mata ta karba tasa ta dawo ta kwanta kan gado duk tayi laushi kaman ba ita ba.


     Su Abba sun zo asibitin sosai sukayi mamakin ganin wai har *ASHRAF* ya warke, nan suka mai ya jiki sannan suka basu lbrn yanda suka kare da DPO, se a lokacin *ASHRAF* yakejin abubuwan da suka faru sanda yake kwance take yaji wani tsanar Humaira ya darsu a zuciyar shi ba kaman KB da yake jin da ze samu ganinshi a yanzu ba abunda ze hana shi hukunta shi. Ganin *ZYNAH*  ta koma barci ne yasa duk suka tashi dan suje su hutu saboda suma ba wani baccin kirki suka iya yi ba, shi kuwa gogan naku kin zuwa gida yayi yace su tafi shi yana nan, suna wucewa shima ya tashi ya fita, be tsaya ko ina ba se station nan yanemi ganin Humaira aka fito mai da ita, wani kallon tsana ya dinga aika mata sannan yace "amma kinji kunya, ki rasa wacce zaki ci amanar ta se kawarki da ta dauke ki kaman ya, in zatayi magana goma seta kira sunanki sau tara amma kikaje kika ha'inceta ta wannan a hanyar, gashi a sanadin ki tana kwance a hospital", nan ya dinga gaggaya mata bakar magana ita kuma banda kuka ba abunda takeyi, yana gamawa ya fita ba tareda ya nemi ganin KB ba saboda yanda yakeji  zuciyarshi na tafarfasa indan yayi harba da KB komai ze iya faruwa sedai shima a kulleshi saboda haka yayi tafiyar shi. A ranan aka kira mahaifiyar Humaira aka shaida mata halin da ake ciki, kukan kam tayi shi saboda abunda Humaira ta aikata, hakuri ta bayar sosai har cewa tayi zatazo Zarian sukace tayi zamanta ai Humairan er suce saboda haka kartaji komai, dole ta hakura ta zauna tana tunanin dalilin da zesa Humaira ta aikata wannan danyar aikin.


ZYNAHWhere stories live. Discover now