Chapter 4

1.7K 105 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

            *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

     *Ina mai ba fans dina hakuri na rashin  posting da  banyi  ba jiya , uncle dina ne  ba lfy anyi  admitting  dinshi  a  hospital shiyasa , ku tayamu da addu'a Allah ya bashi  lfy.*

QUOTE:- "Bridge between souls, stands on pillars of trust! It reflects united self and creates a path to reach each other’s hearts."

   _I dedicate dis page to my bestee *Salma Hadi* matar Korea, Allah ya baki  Sadik  Korea 😜  ta Korea dodo bada  kanki  asare ._

                0⃣4⃣

     Kiraye Kirayen  sallah Asuba ne ya tashe *ZYNAH* daga bacci , tashi tayi  ta  nufi  bathroom  ta dauro  alwallah  sannan ta fito ta shimfida  sallaya tayi raka'atainul  fajri  sannan tayi  sallan  Asuba tayi  azkar  da en adduo'in ta , ta koma ta kwanta . Ba ita tashi ba sai around 11:30  wanda shima saboda phone dinta dake  ta  ringing  ne inba haka ba *ZYNAH* akwai  son  bacci  dan somtimes in Uncle Yusuf ko Islam zasu tsokane ta sai suce mata sleeping  is my  hobby  koma  suce wai sleeping  sickness  na damunta tsetse  fly ya cijeta akaita hospital  itakuma ta bata rai tana bataso.

      Da kyar ta bude idonta tareda yaye comforter dinta  ta dauko wayan kan bedside drawer wanda by now anmata   two  missed calls , tana daukar wayan  wani  call na sake shigowa , ganin sunan dake yawo kan screen dinta ne yasa baccin wartsakewa , ai kuwa da saurinta ta daga wayan tasa a kunne "Hello bestee", ta dayan side din naji ance "swthrt hala dai barcin ne har yanzu da kikaki daga waya","wlh bestee stress dinne dayawa shiyasa", "kinji ki wani stress aikin me kikeyi in banda ki ci ki sha kiyi bacci", "kede kawai bari amma sincerely speaking jiya nagaji dayawa", " toh Allah  ya huce gajiya , dama na kirane infada miki karkije ko ina yau zanzo kinji", "dama ni ina nake zuwa sai kinzo", " ok bye ", "bye".

     Tashi tayi ta nufi bathoom tayi wanka tayi brush sannan ta fito ta zauna gaban mirror tayi drying gashinta tashafa hair cream sannan tashafa Veet Gold body lotion dinta tasa powder da lip gloss dan *ZYNAH* batayi fancy din makeup ba , ko kadan batason makeup wai yana bata fuska kuma to her wai makeup makes sumone look artificial  nd nt natural itakuma tafison natural looks dinta . Da haka ta nufi wardrobe dinta wanda nasaki baki da hanci ina kallo a zuciya na nace wai wannan duka na mutum daya ne lalle dukiya da dadi take . Wani vest ta dauko baby pink in colour anyi rubutu da blue ink a jiki da wando highwaist pencil jean mai mickie mouse a jiki blue tasa sannan ta dauko wani karamin veil baki ta dora akai, gaban mirror taje ta tsaya tana kallon kanta a ciki tareda fadin Masha Allah dan ita kanta tasan ita kyakyawa ce base anfada mataba .

     *ZYNAH* ta kasance wankan tarwada ita ba fara ba kuma baza'a ce mata baka ba irin kallan black Americans , dinnan tanada tsayi daidai gwargado, tana da round face mai dauke da dara daran idanuwanta mai uban kyau kaman na mujiya da dogon hanci amma ba mai tsini chan ba , da dan karamin bakinta mai dauke da red lips wanda in baka sani ba sai ace janbaki ne amma ba janbaki bane , tanada gashin gira mai yawa wanda yake nan kaman anyi shaping nashi amma ba'a ba ga uban gashin kai mai tsayi da tsantsi har gadon baya danko gashin Momsie da dauko ga hips da boobs dai dai dai ita saidai kawai muce Masha Allah da kowa ya ganta yasan anyi halitta anan .

     Back to story

     Kasa ta sauko inda ta tarar ba kowa a parlour sai TV da keta aiki, kitchen ta tafi inda ta tarar da Momsie da Jummalo mai aiki suna girka lunch , zuwa tayi ta rungume Momsie ta baya tareda gaishe ta sannan ta gaida Jummalo duk suka amsa Momsie tace " maman daddynta sai yanzu", "eh Momsie" , " niko wannan baccin naki yafara ban tsoro hanya bazamuje asibiti ba kuwa", "kai Momsie harda ke nifa lfy ta kalau","hmm Allah ya yaye miki ga abincin ki chan kisa a warmer yadan kara zafi", " a'a Momsie banjin yunwa", " kinga baza muyi haka dake ba kici ko kadan ne kidaina barin kanki da yunwa"," Allah kuwa Momsie banjin yunwa amma bari na duba fridge nasan baza'a rasa youghurt ba sai nasha" bata jira cewar Momsie ba tayi wurin fridge ta dauko Habib youghurt ta zauna kan dinning tana sha tana danna wayan.

      Sallama taji tareda bude kofa ganin wacce ta shigo yasa ta tashi da gudunta taje suka rungume juna tareda exchanging i miss u da i miss u too bestee , sakinta tayi jin muryan Momsie na fadin " yau Humaira ce a gidan kwana biyu an mana tawaye an guje mu","a'a Momsie ba haka bane nayi busy ne kwanan nan shiyasa","ya mamanki","tana lfy tace in gaida ke"," ina amsawa" tafada tareda komawa kitchen dan dama hayaniyarsu ne yasata fito wa dan ganin waye. Nan suka nemi guri suka zauna Humaira tace "swthrt dama rakiya zaki min","ina zan rakaki","Zee Mama's boutique inso insiya gown","bestee gown kuma yaushe muka chanza kayan wardarobes dinmu i think it was last week  ai","eh ,amma kinsan birthday  din Haneefa is around corner nd d dress code is black nd pink nikuma banda  pink gown","ok ,yaushe nema birthday din","ran Wednesday  ne","gashi bana gari  lokacin ina zaria".

     "Zaria kuma mezakije yi","zanje registration  mana ko kin manta ne"," ooo yanzu na tuna amma y nt kiyi online registration","nooo  nafiso naje  saboda naga yanayin school din","ok Allah ya kaiki lfy","Ameen","toh ya zaki rakani ne ko yaya","zan rakaki mana bari na chanza kaya", ta miki tayi dakinta ita kuma Humaira kitchen ta shiga har yanzu su Momsie basu gama ba ta musu sanda  aiki sannan ta dauko glass cup da ruwa dan gidan ba bakonta bane sannan taje dakin *ZYNAH*.

     Tana zuwa taga har yanzu *ZYNAH* bata shirya ba tace "kai swthrt yi sauri mana","wlh bestee narasa kayanda zansa ne","yanzu duk yawan kayan nan kinrasa na sawa","wlh kuwa ke zoki zabomin" ruwan  da ta dauko tasha sannan tashiga zabo mata kaya. Wani jallabiya maroon ta dauko mata dan ta san ko ta dauko atampa ba sawa zatayi ba, nuna mata jallabiyan tayi tareda da cewa yayi,murmushi tayi tace tunda bestee ce ta dauko ai ko baiyi bama  yayi , karba tayi tasa design  dinda  ke jiki da black aka yishi saboda haka ga dauko black veil da gucci bag shima baki da flat half shoe. Tayi kyau sosai dukda ba makeup tayi ba, saukowa sukayi a  tare nan sukaga Momsie a parlour  tana kallo, tana ganinsu tace "enmata sai ina ","zan rakata Zee Mama's boutique ne","toh shikenan karku dade kinsan bakici abincin safe ba","eh bazamu dade ba","ok saida kun dawi", a tare sukace sai mun dawo sannan suka fice.

      "Bestee ina motanki ko badashi kikazo bane","dashi nazo a waje nayi parking saboda nasan fita zamuyi", baba mai gadi suka gaisar sannan suka fita zuwa gurin motan suka shiga Humaira ta jasu suka dau hanya.

           _Wacce Humaira_

     Humaira Abdulrahman Umar  full name dinta kenan wacce take kawa ga *ZYNAH*amma kawancensu ya wuce kawance ya kuma en uwan taka wanda har sun hada iyayensu danko yanzu har zumunci sukeyi tsakaninsu . Humaira itace Ýa ta farko a wurin iyayenta sai kanen ta biyu tagwaye maza . Humaira  kyakyawace amma bata kamo kafan *ZYNAH* ba a kyau amma ita fara ce , tsayinsu daya   da *ZYNAH* amma ta girme ta da shekara daya danko she's  18 whereas *ZYNAH*is 17 . A school suka hadu inda a kama *ZYNAH* double  promotion saboda kokarinta aka kaita ajinsu Humaira Wanda itace sit mate dinta , a dalilin haka ne suka zama best of frnds.

                     _Wannan kenan_

  Mzz  Daddy 💋 ✍🏻✍🏻

ZYNAHWhere stories live. Discover now