Chapter 40

1K 65 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

( An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

               4⃣0⃣

*ONE ND A HALF MONTH LATER*

     Abubuwa dayawa dun faru a cikin wata daya da rabi daya wuce, wanda daga ciki soyyayan Minal da Uncle se abinda yayi gaba da yanzu families duk sun sani har an fara shawaran sa ranan da za'a kawo kudin gaisuwa, dan Uncle Yusuf yace beson a ja lokaci saboda yanzu ne yasan yana bukatan aure, Sameer da Basma ma sun daidaita kansu se zuba soyayya suke ba kama hannun yaro, Fahad ya samu Abba da zancen yanaso a nema mishi auren *ZYNAH* batare da tunkari ta ba, Abba yace ba damuwa ze samu Daddy da maganan, KB ya dawo kuma ya nemi Humaira a waya tace mishi ita ta riga ta kuma Lagos saboda haka ba abunda zata iya taimaka mishi dashi amma bawai ta hakura bane, Islam yanzu ta dawo daidai kaman yanda take da ba abunda ke damunta, tana waya da *ZYNAH* kullum sannan yanzu tana dan kokari a school ba dan komai ba sedan conscience dinta ya kasa barin ta na siyar da filin da tayi, *ZYNAH* tana nan dauke da dakon son *ASHRAF* amma ta kasa fada mishi, a cewar ta shida yake namiji ma be fito fili ya fada mata ba se ita da take mace, batasan cewar yaki fada mata bane saboda yanada plan dinshi, yanaso seya gama final exam dinshi a ranan ze fito ya fada mata irin son da yake mata wanda exam din saura sati biyu su gama wanda zeyi daidai da ran birthday dinta.

     Yau weekend Abba yayi tafiya zuwa Lagos saboda yanason ganin Abba akan maganar da Fahad ya mai, Ummi da Ammi kuma suna Maiduguri sunje bikin er yar Ammi, saboda haka gidan ya rage yaran ne kawai suma saboda school ne ba'aje dasu ba.   Abba ya sauka lfy yayi lodging hotel, seda ya huta sannan ya kira Daddy a waya ya shaida mishi ya iso, driver Daddy ya tura hotel din ya dauko Abba, har waje Daddy ya fito yana ma Abba maraba, sannan suka karasa parlour Daddy, Momsie Daddy ya kira tazo suka gaisa, tareda tambayan su Ummi yake ce mata ai suna Maiduguri, take haka sukace da sukayi waya last, nan takira mishi Islam suka gaisa sannan suka basu wuri dan su gana, kayan drinks da snacks ne kala kala ajiye gaban Abba shida Daddy suna zaune Daddy ya maida hankali akan Abba yana sauraron shi. "Kaman yadda na fara gaya maka a waya dana Fahad yaga er wurinka *ZYNAH* yazo ya sameni da sunan yana sonta, na tambayeshi koya mata magana yace bemata ba, toh dama ni tun kan yazo min da maganar na mishi sha'awar ta se kuma gashi yazo da kanshi, shine nace mai ya bari zan nemeka na ma magana, amma wani hanzari ba gud ba nasan a kwari yarinya saboda Fahad yana shayeshaye, amma naga ya fara nutsuwa yanzu".

      Kada kai Daddy yayi alamun gamsuwa sannan yace "Dan fillo in banda abunka, ai yayana yayanka ne, sannan maganan shayeshaye ze daina Dan shiriya daga Allah ne, kuma ba wanda zeki hada zuri'a da kai saboda haka nima na bada goyon baya dari bisa dari, kaga abu ma yazo da sauki se a hada da Yusuf da Minal gaba daya", dariya Abba yayi yace, "ai Yusuf da alamun baze iya jiransu ba, tunda su da sauransu, amma shi ai Allah Allah ma yake", dariya Daddy yayi yace "lalle Yusuf yaci zero tunda ya bari sirikinshi ya gane yana Allah Allah", nan dai suka tsayar da magana cewar nan da sati biyu in sunzo Zaria birthday din *ZYNAH* zasu zaunar dasu su fada musu abunda suka yanke na hadata da  Fahad (tirkashi!!!). Abinci Islam ta shigo musu dashi ta ajiye a kan carpet, saukowa Daddy yayi yace "bismillah", shima Abba saukowa yayi suka zuba abincin, fried rice ne da pepper chicken se coslow da farfesun catfish, se Chi exotic na kwalli, seda sukaci sukayi nak sannan sukayi sallan Isha sannan Abba yace ze wuce, ba yanda Daddy beyi dashi ba kan ya kwana ba amma yaki, har wurin suka rakashi, ya ciro kudi ya mikawa Islam taki karba, seda Momsie tace mata ta karba sannan ta karba tana godiya, yaso ganin Uncle Yusuf su gaisa amma aiki ya mishi yawa shiyasa bezo gida ba duk da weekend ne, haka ya shiga mota driver ya jashi suka tafi.

*ZARIA*

     Zaune suke a parlour suna hira kowa nasa albarkacin bakinshi amma banda *ZYNAH* da tayi shiru saboda ciwon maran da ke neman tashi, ganin ciwon ze matsa matane yasa ta tashi ta shiga dakinta ta kwanta tareda rike maran, *ASHRAF* da Fahad sun lura da ita amma ba wanda yayi yunkurin tashi saboda kar a gane halin da suke ciki (me abun boyewa😡), Husna ce ta fito daga dakinsu tazo ta mikawa *ASHRAF* maths note dinta tace "Hamma na kasa solving dinshi, koya min", ze iya koya mata amma saboda yasan halin da sahibarshi ke ciki dan kwata kwata hankalinshi ba'a kwance yake ba yasa yace "jeki *ZYNAH* ta koya miki ni ba gane rubutun ki nakeyi ba", dakin ta nufa ta kwankwasa amma shiru, bude kofan tayi ta shiga ai shock tayi ta makale wuri daya tama rasa me zatayi, littafin hannunta ne ya sabule ta fita a guje se parlour tana haki, ganin yanayin ta yasa hankalinsu ya tashi Minal tace "ke lfy", bakin ta na rawa tace "Ya *ZYNAH* zata mutu", ai bata gama magana ba *ASHRAF* yayi wani dira daga saman kujeran da yake ya tsallake center table se dakin *ZYNAH*, kwance ya ganta a sume, a kidime ya karasa wurinta yana jijjigata yana kiran sunanta, Fahad na shigowa be jira wata wata ba ya kinkime ta, tasowa *ASHRAF* yayi yana cewa "ina zaka kaita", Fahad da yariga yayi gaba yace "Dan Allah Malam dauko key din mota mu kaita asibiti", se a lokacin *ASHRAF* ya tuna da wani abu waishi asibiti dan harga Allah ya manta saboda tashin hankali, dauko makullin yayi ya fito su Minal suka biyosu Fahad yace su koma saboda su Husna dan Juwairiya har tayi barci, dole suka koma sukuma suka wuce hospital da ita.

     Suna zuwa asibitin aka karbe ta emergency, wannan karon ma wannan doctor din shine yakara dubata, sosai ganin ta yabashi mamaki dan yasan da ace taji maganarshi da wuya akara kawota a wannan halin, dubata yayi sannan ya bata dakin aka samata drip lokaci daya duk ta zube ta zabge kaman ba ita ba, sosai ta rame ga wani kyau da haske data kara, Fahad ne yace *ASHRAF* yaje gida ya huta amma yaki wai ze zauna wurinta tun lokacin Fahad yafa suspecting din kaman akwai wani abu a tsakanin *ASHRAF* da *ZYNAH*.

      Haka su biyun suka zauna a asibitin har garin Allah ya waye *ASHRAF* ko gyangyadi, saboda haka idonshi yayi ja, kowa ya ganshi yasan beyi barci ba, su Minal ne sukazo gabadayansu har lokacin *ZYNAH* bata tashi ba, doctor ne ya shigo ya dubata, yana ganin *ASHRAF* yace amma bakayi barci ba, kada kai kawai *ASHRAF* yayi doctor yace yazo ya karba maganin ciwon kai in ba haka ba kanshi zeyi ciwo, ba musu yaje ya karba ya sha, Fahad yace mishi suje gida suyi wanka su dawo kan sannan ta tashi tunda su Minal na nan, da kyar ya yarda yaje gida saboda a ganinshi ba wanda ze iya kula da ita kaman yanda shi zai kula da ita, tun a mota ya fara barci saboda maganin barci doctor ya bashi, dasu ka kai gida da kyar ya kai kanshi daki, kwanciya yayi dan ba abunda ze iya yi, barci ne me nauyi ya dauke shi, bashi ya tashi ba se hudu na yamma, ganin ba kowa gidan yasan cewar duk suna asibiti, sosai yaji haushin kanshi saboda yasan yanzu ta tashi kuma bazata ganshi wurin ba, a gurguje yayi wanka ya shirya ba abunda yasa a baki  amma haka ya fita ya shiga motanshi se asibiti.


     KB da SMART ne zaune ga kwalban giya a gabansu da kwalin sigari, kallon SMART yayi yace "i hav no alternative than to kidnap dis girl nd satisfy my self", kallon shi SMART yayi yace "boss kafada abinda kakeso, mu kamota ne ko ya", "eh zaku kamo min ita amma ba yanzu ba, se Monday saboda yanzu ita kadai take zuwa school ta koma dan *ASHRAF* kanshi yayi zafi yasa project a gaba", "shikenan boss, yanda kace ayi hakan za'ayi", wani murmushin mugunta yayi yace "yarinya inkinsan wata bakisan wata ba", wayan shi ya dauka ya kira wata babe dinshi yace tazo guest house ta sameshi sannan ya ajiye wayan. *ASHRAF* na kaiwa asibitin dakin ta ya wuce, Fahad baya nan se su Minal, yana zuwa tace "yawwa dama kai nake jira, zamuje gida mu dawo", kai kawai ya kada mata dan duk haushin su yakeji saboda basu tashe ba, kujera yaja ya, zauna kusa da gadon  su kuma suka wuce, kallon ta yakeyi saboda tausayi take bashi ganin yanda ta rame, hannunta ya riko yace "sorry i didn't come on tym", murmushin karfin hali tayi tace "u don't hav to explain, Hamma Fahad told me everything, bakayi barci ba yesternight, u look after me d whole nyt, nd dats more than enough, so u don't hav to explain", murmushi yayi sannan yace "hav u eating", "yes", suna zaune suna hira sama sama saboda da kyar take magana doctor ya shigo, sosai yamata fada wannan lokacin kuma yace in aka kara kawota kuma to se ya nemo iyayenta, ta mishi alkawarin bazata kara shan zaki ba saboda yanda *ASHRAF* ya damu, ita kuma bata son damuwanshi.

*THREE DAYS LATER*

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now