Chapter 50

1K 70 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


              *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Even If You Never Know It, Each And Every Kind Act Affects Someone, Your Small Act Of Kindness Might Be The One Small Thing That Keeps Another Holding On."

                5⃣0⃣

*WASHEGARI*

     Uncle ne ya hadawa Minal ruwan zafi sannan ya raka ta har bathroom dan ta gasa jikinta tayi kwanta, da kyar ta iya zama cikin ruwan zafin saboda wani radadi da takeji, ban da hawaye ba abunda takeyi, seda ta gasa jikinta sosai sannan tayi wanka tayi alwallah ta fito, koda ta fito Uncle baya dakin, wurin dressing mirror taje tayi en shafe shafenta tasa wani atampa super wax baki me ratsin ja, sosai kayan yamata kyau tayi kwalliyan ta daidai gwargado, sallah ta tashi tayi tana idarwa Uncle ya shigo dakin cikin Blue jeans da black gucci top, karasowa yayi cikin dakin ya tsugunna kusa da ita yace "har kin gama", kada mai kai tayi kanta a sunkuye yayi murmushi yace "toh kalleni mana, ko kunyar ce har yanzu", girgiza kai tayi yace "inaga ban cire kunyar nan ba har yanzu, bari nazo na cire shi yanzu", ai kafin ya gama magana har ta dago tace "a'a wlh nadaina, kagama ina kallonka", dariya yayi yace "ashe dai bakya so a maimaita", zatayi magana sukaji ana dannan door bell, tashi yayi yace "ina zuwa", sannan ya fita ita kuma ta tashi ta cire hijabin jikinta ta daura dankwali. Yana bude kofa su *ZYNAH*  yagani ita da Basma rike da coolers a hannu,  "a uncle ashe kun tashi, har nake cewa kilama baku tashi ba", cewar *ZYNAH* tana magana tana dariya, kala bace mata ba illa jingina da yayi jikin kofa ya rungume hannuwanshi yana kallonsu, Basma ce tace "breakfast muka kowa muku, adda Minal bata tashi bane", "bata tashi ba, ku miko kullolin kuyi gaba", *ZYNAH* ta kalleshi tace "haba Uncle, koranmu kuma kakeyi", jin muryan Minal tana cewa "a'a kune a gidan me kukeyi a bakin kofa da bazaku shigo ba", yasa suka kalli Uncle a tare sannan suka raba ta gefenshi sukayi ciki *ZYNAH* tace "mijinki yace baki tashi ba", kallonshi tayi ya tsaya yana hararansu yace "toh ku ina kuka taba ganin anzo gidan amarya da sassafe, Basma tace "shadaya fa yanzu, rana ta kusa", Uncle Yusuf yace "wat ever, ku kai abincin dinning kuzo ku wuce", amma inaaaa yaran nan kin tafiya sukayi daga karshe ma dasu akayi breakfast din wai basu tsaya sunci abinci a gida ba.

     Su *ZYNAH* basu suka bar gidan ba se yamma lis saboda masu zuwa duba amarya da mata sallama dan dayawansu a yau zasu koma sauran kuma washegari, suna kaiwa gida sukayi wanka sannan suka sauko zuwa parlour, Ammi tace "ku kuma daga ku kai abinci ku dawo se kuje ku shantake a gidan", hakuri suka bayar tareda cewa sun tsaya sun gyara mata gidane saboda bakin da tayi, Momsie tace "ya muku kyau", sudai tsit sukayi suna kallon movie din da akeyi.

*ZARIA*

     *ASHRAF* ne da Sameer zaune a dakin Sameer, Sameer yace " guy look kai kake damun kanka da zancen wani KB, waye KB, abunda yake takama dashi muma dashi muke takama,kawai zamuje mu sameshi ne muja mai warning akan kar mu kara ganinshi kusa da *ZYNAH* shikenan, in yaji toh, in kuma yakiji se mu nuna mishi namu iya shegen", sauke ajiyan zuciya *ASHRAF* yayi yace "gaskiya bana ganin zan iya risking rayuwar *ZYNAH* ta wannan hanyar, kai kanka kasan waye KB, yanzu zamu iya muyi mishi magana shikuma a lokacin zeso ya nuna mana nashi tabarar, and  honestly speaking i can't do dat, i can't put her in more danger", kallonshi kawai Sameer keyi yace " toh yanzu ya kakeso ayi, kace har yanzu yana binta nd u want to protect her, na kawoma solution kuma kace be maka ba, toh kai kawo naka shawaran", gyara zama *ASHRAF* yayi yace "inaga d only way out is muje da sunan bashi hakuri mugani kozai hakura, dan wlh if he tries any thing silly wit her am going to skin him alive", murmushi Sameer yayi yace shikenan bari na shirya muje nasan inda zamu shi", tashi yayi ya shirya suka fito *ASHRAF* ne mai tukin sukayi gaba.

     A wani beer parlor suka tsaya (gidan san giya) *ASHRAF* ya kalli Sameer yace "yanzu kanaso kace mun yana nan", " eh na tabbata yana nan", *ASHRAF* a kalli Sameer yace "gaskiya bazan iya shiga nan ba, gidan giya, Allah ya kiyaye, ya tsareni", kallonshi Sameer yayi yace " solution fa mukazo nema a nan, kuma in bamu same shi yanzu ba bansan a ina kuma zamu iya samunshi ba, saboda haka daurewa kawai zakayi", girgiza kai *ASHRAF* yayi tareda sauke numfashi sannan yace "naji mushiga", fitowa sukayi suka shiga wurin *ASHRAF* badan ranshi yaso ba seda ba yanda ya iya, can lungu suka hango shi zaune da wata budurwa a kan cinyanshi ga su gulder, star,33 a gabanshi da ganinshi kasan ba'a hayyacin shi yake ba, warin giyan da wurin keyi ne yasa zuciyan *ASHRAF* yasamo tashi, ganin in be bar wurin ba komai ze iya faruwa yasa bashiri ya fita daga wurin da saurin shi, amai ne yataso mishi ya mufi bakin tap yana kwarara amai kaman ze amayo hanjin cikinshi, Sameer ne ya biyo bayanshi yace " bros lfyn ka kalau kuwa", seda ya dauraye bakinshi sannan yace "ba lau ba, bazan kara wani minti daya a nan wurin ba, muwuce gidan", " toh amma KB din da mukazo gani fa", "manta da KB zamusan abunyi", yana fadan haka yaje  ya shiga mota, wannan karon Sameer ne yaja motan, *ASHRAF* kuwa yayi shiru yana tunanin banzan ruyuwan da KB ke living.

     Suna kaiwa gida *ASHRAF* yacewa Sameer kaina na ciwo muhadu gobe, bari na shiga gida na kwanta", sallama sukayi sannan kowannensu ya shige gida, Kwanciya *ASHRAF* yayi ko kaya be cire ba, ya shiga tunanin ta yanda za'ayi su samu mafita kan KB, dan shi *ASHRAF*  ya tabbabta har yanzu KB bibiyar su yakeyi, duk da sun bar school amma KB be barsu ba yana nan yana bibiyarsu, ganin ba wani mafita dayazo mai me yasa ya dauki waya ya kira *ZYNAH* ta dauka suka gaisa sannan yake tambayanta yaushe zasu dawo take cemai gobe ko jibi, yake cemata toh in tadawo ta kula da kanta sosai saboda shi kafin ta dawo ze koma Abuja, sosai sukayi hira sannan sukayi sallama suka kashe wayan. Yana ajiye wayan ya shiga ya watsa ruwa yayi alwallah yazo yayi nafila raka'a biyu sannan yafara jero addu'oi yana nemar wa *ZYNAH* tsari daga sharrin KB, gyangyadi yafaryi saboda haka ya tashi yaje kwanta dan ya samu barci.

     Washegari *ASHRAF* yakoma Abuja, Sameer ma ya koma Kano, inda su *ZYNAH* se washegarin shi suma suka dawo kowa ya kama harkan gabanshi, amarya da ango ana can ana cin amarci, *ASHRAF* kullum seya kira *ZYNAH* su sha hiransu kuma se ya tambayeta ko taga KB tace mishi a'a, abunda basu sani ba tun randa sukaje beer parlour suka ganshi da basu samu daman yi mishi magana ba, washegarin shi shima ya bar kasan zuwa kai mahaifiyarshi treatment. Sunyi hutu har sun koma second  semester inda *ASHRAF* yana nan yana planning gidan da zasu zauna da *ZYNAH* wanda yanaso gidan ya zama one in town, shiyasa ma yake tsara gidan dakanshi, inda Sameer ne engineer din da ze tsaya har a gama ginin.

     *BAYAN WATA BIYAR*

     *ASHRAF* ya gama service dinshi inda a wurin da yayi sukace ya musu aiki amma yace a'a saboda wani company sun riga sun bashi aiki wanda ta hanyar Abba ya samu kuma a Abujan, haka suka hakura suka barshi ya tafi, shima Sameer inda yayi service sunji dadin aiki dashi inda sukace zasu dauke shi aiki as personnal assistant din MD din wurin amma saboda za'ayi transfer din MD din zuwa Abuja shima Sameer akace dashi za'aje, sosai yaji dadin wannan offer din saboda ko ba komai shida bst frnd dinshi gari daya zasu zauna, *ASHRAF* ya samu Abba da maganan ginin shi inda Abba da kanshi ya siya mishi fili a Abuja har an fara aikin, sannan ansa bikinsu nan da wata shida kafin nan an gama ginin, sosai *ASHRAF* yake shirye shiryen zuwan bikinshi inda yanzu kudi yafara zauna mishi dan ba karamin salary yake dauka ba, Fahad har yanzu dai shiru ba lbrn budurwa wanda Ammi ta mishi magana har ta gaji amma sedai yace har yanzu ba samu wacce ta mishi bane. Sameer da Basma ma suma anso a hada bikinsu danasu *ASHRAF* amma saboda shima yanaso yagama gininshi dake kusa dana *ASHRAF* yasa aka daga saboda haka bayan bikinsu *ZYNAH* da wata uku suma za'ayi basu.

     .
_READER WATA BIYAR KENAN AMMA KB SHIRU BA LBRN SHI, KU BIYO NI A NEXT DAN JIN LBRN KB DA HUMAIRA YADDA ZA'A KARE._

     _Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now