Chapter 16

1.3K 76 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

QUOTE:- "You don't love someone for their looks, or their clothes, or for their fancy car, but because they sing a song only you can hear."

     _I dedicate dis page to my luvly frnd *Baby (Mzz Omo Alajah)* Allah ya raya mana Hanan (Ameen)._

               1⃣6⃣

     Idi driver ya zagaya da *ZYNAH* sosai har kofar Nassarawa,kofar Mazugal da sauran kofofin Kano ba wanda be nuna mata ba sannan ya nuna mata kwankwasiya bridge, daga nan ya kaita Shop rite da Jifatu store da sauran wuraren shakatawa. A takaice dai wuri daddaya ne be nuna mata ba. Basu suka dawo gida ba se yamma lis, a gajiye ta shigo parlourn da sallaman ta Granny ta amsa mata ta zauna gajab kan kujera tareda fadin "wash, nagaji" tana rike da kwankwaso, Granny ta kalle ta tace "ragguwa aikin me kikayi, koh ke kikayi tukun se haka" ,"kai Granny wlh nagaji, Kanon naku akwai girma ga jama'a ga uban hold up" ,"ka jiki ai kema garinku ne tundade garin ubanku ne kuma nan cibiyarshi take dan nan aka haife shi, kuma maganan go slow akwai garin da ya kai Lagos din  go slow ne", dariya takeyi sosai ganin yadda Granny ta daddage tana kare Kano tace "kaiiiii Granny maida wukanki an tabo Kano zaki balbale ni da masifa"," au nike masifa er nan" tana magana tana janyo carbin da ke ajiye kusa da ita a kan kujera, *ZYNAH* na ganin  haka  ta tashi tana fadin "a'a Granny ni bance ba, har yanzu Uncle be dawoba" ,"be dawoba" ,"lalle su Uncle anji dadin yawo bari na kirashi naji ko suna ina" nan ta dau wayarta ta bugawa Uncle ya dauka tace "Hello Uncle kana ina, ok , kun kusa gida kenan, toh se kunzo" dif takashe waya tace ma Granny "wai suna hanya sun kusa kaiwa gida","toh Allah ya kawosu lfy" ,"Ameen, ni zanje nayi wanka" ,"Allah ya raka taki gona" dariya kawai tayi ta shige daki.

     Muryan Uncle taji suna hira shida Granny ta fito sanye da hajibin da tayi Sallar Magrib dashi tana cewa "Uncle se yanzu, yau kasha yawo, ko ka tafi dani koh" ,"toh ai kina barci lokacin kuma banson na tashe ki" ," Ai nima naje yawun, driver ya kaini ba inda bamuje ba" ,"ai shikenan tunda ya kaiki, ki hada kayanki gobe zamu koma an kirani a office yau akwai wani case dinda zanyi representing dinsu a kai","kai Uncle gobe goben nan" ,"kinga *BEAUTY* dama can kwana biyu mukace zamuyi" ,"bt Uncle kaba"....... bata karasa fadan abunda zatace ba ya katseta da cewar "no buts we ar leaving tomorrow nd dat is final" fuska ta hade wai ita tayi fushi ta tashi taje ta bude fridge ta dauko Hollandia youghurt ta koma daki, Granny tace "er nan akwai rigima" murmushi kawai Uncle yayi dan beso ranta ya baci ba da ze iya kara kwana daya da  ya kara amma ba ze iya ba saboda aikin da ke jiranshi.

**********
               *Zaria*
     *ASHRAF* ne da Hamma Fahad da Sameer suke cikin game room dinsu suna buga snooker amma *ASHRAF* kwakwata hankalin shi baya wurin yana tunanin wani abu daban ne har su Sameer suka gane yanadai buga game din ne for d sake of playing amma hankalin shi baya wurin dukda kuwa best game dinshi kenan. Da ya gaji ma ce musu yayi "am out" ya ajiye stick dinshi ya bar musu dakin. Fahad ne ke tambaye Sameer "wai me ke samun guy din nan ne he looks doll kuma ni ban taba ganin ya bar game din nan ba da golf ne shine zance maybe he's sacred i  will win him" ,"nima bansan me ke damunshi ba, but will ask him sha" ,"please do dan ni game din ya fita raina yanzu". Da haka duk suka ajiye stick dinsu suka fito kowa ya kama gabanshi. Dakin *ASHRAF* Sameer ya shiga ya ganshi zaune yasa sketches dinda yayi a gaba yana kallo, Sameer ya zauna kusa da shi yace "guy me ke samunka u look doll nd it's obvious abu na damunka" tashi yayi yana tattare drawings din waje daya yace "forget it ba abunda ke damuna" ,"bangane ba abunda ke damunka ba bayan ur mood says it all" ,"nace ma i'm ok, in kuma zancen kakeso toh cigaba da tambaya" sanin halin *ASHRAF* na rashin son takura yasa ya kyale shi ya shiga toilet ya dauro alwallah ya fito shima *ASHRAF* yaje yayi alwallahn suka jera zuwa masallaci.

ZYNAHWhere stories live. Discover now