Chapter 18

1.1K 82 7
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITERS ASSOCIATION*

QUOTE:- "Girl’s eyes are faster than GOOGLE in searching handsome guy but girl’s heart is slower than a turtle in forgetting a boy that she loved".

     _I dedicate dis page each nd every member of *BAIWA WRITERS ASSOCIATION*, luv yah all .❤_

                1⃣8⃣

         *Zaria 5:24pm*
*ASHRAF* da Sameer ne zaune a kasa a dakin Sameer suna buga PS, *ASHRAF* ne ya tambaye Sameer "karfe nawa kacewa KB yazo" (in baku manta ba KB shine wanda Sameer yazo yana gayawa Ashraf cewar yanaso a ba Ashraf president din department dinsu)  ,"5:30 nace mishi maybe his on his way, na tura mishi address dina" ,"Allah yasa yazo" ,"i knw he will definitely come, tunda ce mishi nayi kanaso ka ganshi". *ASHRAF* be sake magana ba sukaci gaba da game dinsu tareda zaman jiran KB, shiru shiru KB zezo bazezo ba har suka gaji da jira *ASHRAF* yace "Amma KB ya kai dan iska, in ana neman banza akasamu KB an gama" shidai Sameer murmushi yayi ya rasa abunda yasa bestee dinshi da KB basa shiri in fact  magana ma baya hadasu. Suna zaune har past 6 sannan wayan Sameer yayi ringing ya duba seda ya kalli *ASHRAF* yace "shine" sannan ya dau wayan yasa a load speaker  yace "Hello" ta daya bangaren akace "hello, gani a waje" ,"ok gani nan zuwa bari nazo na shigo da kai" ya kashe wayan *ASHRAF* kuwa tsaki yayi yace "mutum se girman kai" shidai Sameer girgiza kai kawai yayi ya fita.

    Basu wani dade ba suka shigo Sameer na gaba KB na baya ko kallon inda suke *ASHRAF* bayiba har suka zazzauna KB ya miki wa *ASHRAF* hannu suka gaisa sannan yayi gyran murya yace "KB ba komai yasa nace inason ganin ka ba illa akan wani rumours danaji wai ka hada kan en department dinmu kace musu karsu zabe kowa a matsayin president dinsu se ni, anyi haka ko ba'ayi" KB yace "anyi" *ASHRAF* yace "Gud, yanzu abunda nakeso da kai shine yanda kaje kayi poisoning  mind dinsu kaje kuyi magana dasu ku canza wanda zaku sa, cos i don't remember telling u i want to b president" wani kallo KB ya mishi kafin yace "in naki fa" *ASHRAF* yace "den u will have d worst president ever" wani murmushin rainin hankali KB yayi yace " *ASHRAF* dadina da kai girman kai da gajen hakuri, me lefi dan nace a baka president, it's a post everybody will luv to hold" cike da masifa da bacin rai da daga murya *ASHRAF* yace "well i don't to, dole ne inkanaso kai kaje kayi mana, me hadina da kai da zakace a bani, katashi ta tauye ma mutane hakkinsu kaki bari su zaba wanda ransu keso simply becos kana ganin kana da kudi zaka iya siyansu, well let me make one thing clear to u insu ka siyesu da kudi to ni baka isa ba dan duk wani abunda kake takama dashi nima inayi" shima KB ranshi ya baci matuka yabude baki zeyi magana ya kasa saboda yanda ranshi yabace, seda ya kwantar da hankalinshi sannan ya kalli *ASHRAF* yace "ina lefin me sonka, me son ganin cigabanka, amma tunda ka nuna bakaso bazan takura ma ba zansan abunyi" *ASHRAF* yace "da yafi maka" ya dauka wayanshi ya kara gaba ko sallama be musu ba saboda yanda ranshi ya baci, KB ya juya wurin Sameer wanda yayi shiru kaman baya gurin yace mai "kama abokinka magana, ba'a rayuwa a haka" Sameer yayi ajiyar zuciya yace "yi hakuri, zan mishi magana".Tare suka fito KB ya shiga motanshi a dari ya bar wurin Sameer ya girgiza kai ya taka zuwa gidansu *ASHRAF* dayake basu da nisa unguwa daya ne duk cikin G R A suke.

_WAYE KB?_
     KB ďa ne ga Senate Usman Sani paki da Hajiya Surayya, KB ya kasance ďa daya tilo a wurin iyayenshi saboda haka suka shagwaba shi suka sangartar dashi, baya neman abu a wurinsu ya rasa komai yakeso suna mai sannan basu tsaya sun bashi tarbiyya me kyau ba saboda harkokin siyasa da sukasa a gaba, wannan sakacin nasu yasa yakara lalacewa, rashin ji ba wanda be iya ba, shaye shaye, neman mata, wulakanta na gaba dashi da rashin ganin girman mutum, gashi zukune babba ba abunda ya iya se siyan lecturers da kudi suna bashi mark suna passing dinshi, da haka ya kai 400level. Duk girman ABU ba wanda yake burge shi kaman *ASHRAF* saboda kokarin shi amma kuma shi *ASHRAF* ko kadan be kaunan KB saboda halayenshi.(Wannan shine brief history din *Kabiru Usman Sani paki*, muje zuwa).

ZYNAHWhere stories live. Discover now