Chapter 49

1K 65 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:- "Everyone makes mistakes in life but it doesn’t mean they have to pay for them for the rest for their life. Sometimes good people make bad choices. It doesn’t mean that they are bad… it means they are human.,"

               4⃣9⃣

     *ASHRAF* ya dade a motan zauna yana tunanin kala kala dan shi yasan ganin KB a wurin ba alheri bane, ganin ba wani solution yasa ya fito daga motanshi ya shiga cikin gida, wanka yayi ya kwanta amma seya kasa barci saboda yunwa dan se yanzu ya tuna beci komai ba tun safe banda kayan drinks da ruwa daya dinga durawa cikinshi, wayanshi ya dauka yakira Minal dan yasaba ita yake kira in yana jin yunwa, ganin bata dauka wayan bane  ya tuna amarya ce fa, kilama tayi barci saboda gajiya, har ze kira Basma sekuma ya fasa ya kira *ZYNAH*, dauka tayi tace "Mine bakayi barci ba", jin yanayin muryanta ya tabbatar mai da tasoma barci saboda haka yace "na kira ne to wish gudnyt nd slp tyt ok", cikin barci tace "nd u too, bye", "ok bye, luv u dear", "luv u more", tana fadan haka ta kashe wayan ta koma barci. Ganin yunwa ze illata shi yasa ya tashi ya nufi part din Ummi, shiru part duk en biki anyi barci amma basu kulle kofa ba, kitchen ya shiga ya soya kawai sannan ya hada lipton ya koma dakin shi, seda ya cinye sannan ya kwanta da haka barci ya daukeshi.

*WASHEGARI*

     Tun wuraren karfe tara akasa amarya da ango gaba ana musu nasiha saboda jirgin twelve zasubi, kuka kam Minal tayi shi kaman danshi aka aiko ta duniya, Abba, Daddy, Ummi, Ammi duk seda suka mata nasiha inda shima uncle ba'a barshi ba, iyayen Uncle sunji dadin auren da dansu yayi kuma gidan mutunci, sha daya aka fito da amarya dan tafiya wanda tareda Ammi da Momsie da Anty Hadiza da wasu tsofaffi biyu ne, zasu kaita, su *ZYNAH* kuwa se washegari zasu, kuka Minal takeyi duk ta kankame Ummi kaman zata koma cikinta, duk wanda yake wurin seya zubar musu da kwalla saboda yanda Minal take kuka, da kyar aka banbareta daga jikin Ummi wacce itama kukan takeyi sannan aka sata a mota wanda *ASHRAF* ne ze kaisu, dayan motan kuma Hamma Fahad ne wanda su Ammi ke ciki kenan da haka aka fita da ita daga gidan iyayenta zuwa gidan mijinta.(Allah ya bada zaman lfy Minal😍). Seda suka kaisu Kaduna suka jira jirgin su ya tashi sannan su *ASHRAF* suka wuce inda sukata tsere a hanya ba wanda yakeson yaga dan uwanshi ya wuceshi har magana ake musu su rage gudu amma inaa maza sun rike gear se yanda sukayi dashi.

     Karfe biyu da en mintina jirginsu ya sauka a murtala Muhammad airport, yau ga Minal a Lagos duk da ta taba zuwa wurin Doc Jamal amma wannan zuwan daban yake a wurinta saboda zuwane na zaman dindindin, aure kenan ba inda baya kai mutum, gidan Momsie suka wuce direct dan se gobe zasu kaita kafin sannan su Uncle suma sun karaso, suna zuwa gida Momsie ta bude mata dakin *ZYNAH* ta sauka a wurin, wanka tayi tayi sallah sannan aka kawo mata abinci sosai taci dan rabonta da taci abinci ta koshi tun sanda aka fara events din bikin, tana cikin cin abinci wayanta yafara ringing, ko bata duba ba tasan Uncle ne dan ringing tone dinshi daban ne, kin dauka tayi harse da tagama cin abincin sannan ta kirashi, kashe wayan yayi ya sake kiranta yace "hello wifey na kiraki baki dauka ba", "abinci nakeci kuma banson na barshi shiyasa", yace "ok, yanaji muryan ki yayi kasa, ko kukanne har yanzu", girgiza kai tayi kaman yana gabanta tace "kaina kemin ciwo amma yanzu zanje na karbo magani wurin Adda Hafsa", "sorry wifey, kukan da kikayi ne, ai Juwairiya ta bani lbrn kukan da kikayi", murmushi tayi tace "wato Juwairiya bazata daina surutu ba, abinda ba'a tambayeta seta fada", dariya yayi yace "toh ai ita surutunta me ma'ana ne, ba kaman wasu ba da zakiga shirme kawai suke fada", da haka sukata hira setaji har ya dan debe mata kewan gida, nan yake fada mata suma Karfe shida jirginsu ze tashi by nine ze sauka Lagos din shida abokanan shi.

     Karfe shida jirginsu Uncle  da abokanan shi ya tashi inda karfe tara suka kai kowa yakama gabanshi, koda Uncle yashiga gida be bari an ganshi ba se Minal da yakira yace mata yana gida tamishi sanda zuwa, *ZYNAH* ana can anata hada kaya inda *ASHRAF* shi so ma yake ta tafi saboda gani yakeyi kaman KB ze iya zuwa at any time,  dare yayi gidan ya dan yi shiru ya kirata yace tazo garden ta sameshi, mayafi tasa ta fito zuwa garden din nan ta ganshi zaune yana danna waya, zama tayi kusa dashi tace "B frnd yau kayi tsada", murmushi yayi yace "did u miss me", "off cos, u no i will always me u", "i missed u too, shiyasa na kiraki saboda inganki", nan sukata hiransu wanda basu suka tashi daga wurin ba se goma da rabi, daki tashiga ta kwanta amma ba barci takeyi ba, kallon Humaira da tayi barci tayi tace "bestee kenan, akwai saurin barci", sannan ta gyara mata comforter itama ta kwanta.

*WASHEGARI*

     Tun karfe takwas su *ZYNAH* suka gama shiryawa da kawayen amarya da wasu wa'anda dasu za'aje, a takaice dai sunkai su sha biyar, su *ASHRAF* dai sune suka kaisu airport, seda jirginsu ya tashi sannan suka dawo, sukuwa chapter sunka dinga yi a jirgin (tafiyan yawa dadi ne dashi), kafin karfe daya har sun sauka dan a gida sukayi azahar, ana yin la'asar aka fara shirye shiryen kai amarya gidanta dake Marple wood estate, wannan karon ma Minal seda tayi kuka amma be kai najiya ba, ana yin isha ba bata lokaci aka kai amarya gidan ta, tamfatsetsen gida Uncle ya siya wanda furniture kawai yasa se paint din da ya canza zuwa lemon da white dan tace kalan da takeso kenan, gidan duplex ne me parlour uku bedroom shida da kitchen biyu kowanne da store se dinning sannan ko wani daki akwai bathroom a cikin,  duk wanda yaga gidan seya yaba, haka aka fara watsewa aka bar daga amarya se kawayenta da kannenta, nan suka dinga hira suna zolayanta wai se kuka takeyi salon ta kamu da ciwon kai ta hana ango cin angwanci, daga sama *ZYNAH* tace "wai nikam mekesa amare kuka ne, sekace ba auren soyayya ba", kallonta Minal tayi tace "ki bari in yazo kanki seki san abunda ke sasu kuka", ai nan da nan tace "Allah ya ki yaye inyi kuka, sekace ban son shi, da dai ban son wanda za'a aura min shine zanyi kuka, amma ina son shi yana so na mena kuka", gabadaya parlour kallonta akeyi Basma tace "kuyi shaida tace ita bazatayi kuka ba, in kikayi kuka ranan se na miki tsiyan da keda kanki zaki bar inda nake, indai kika kuskura kikayi kuka", "toh Allah na tuba kukan me zanyi", nan dai sukata chapter har angwaye sukazo Uncle baki yaki rufawa saboda murna, ba bata lokaci akayi siyan baki sannan abokai sukama amarya da ango nasiha, abokanan ango suka tasa keyan kawaye dasu Basma gaba sannan Uncle ya rakasu ya rufe kofanshi  aka bar amarya da angonta.

     _Kuyi hakuri da wannan ba yawa,will type d next page soonest Insha Allah. Luv u guys unconditionally😍😘_

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now