Chapter 63

2.3K 103 14
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻



                *ZYNAH*


(An Interesting Luv Story 2017)


By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)


*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*


QUOTE:-"Life is always up and down, so why are you worried when you are at the bottom; the next place is up."


_I dedicate dis page to all my fans, tnx for d unconditional luv so far😘, I luv u lodi lodi😍._


_Last Page_
        🔚


               6⃣3⃣

*BAYAN WATA BIYU DA SATI BIYU*

     *ZYNAH* ta koma school amma Friday take dawo wa ta koma sunday da yamma *ASHRAF* be damu ba saboda yasan muhimmacin karatun kuma takusa gamawa shiyasa ba takura take karatun ta. Shirye shiryen bikin Basma akeyi nan su Abba sukasa Fahad gaba suna tambayarshi me yake ciki har yanzu shiru ba maganan budurwa, sosa kai yayi yace "Abba ina da wacce nakeso", Abba yace wacce ce muje mu nema maka aurenta a hadaku da Basma", kanshi a kasa yace " Humaira ce Abba", Abba yace "wace Humairan", " Humaira dai kawar *ZYNAH*", Ammi na jin haka ta tashi tace "sam ban yarda ba, dana baze auri wannan yarinyar ba dan ban  yarda da ita ba", Abba ne yace " kwantar da hankalinki, muduka musan tayi laifi amma ai ta amsa laifinta kuma ta bada hakuri, maganan ya wuce", nan Abba da Ummi suka mata nasiha tace "toh shikenan", amma badan ranta yaso ba.  Nan Abba ya kira Daddy ya shaida mishi Daddy yace ba matsala za'a samu mahaifiyar ta a ji, nan Daddy yama Momsie bayani, washegari taje gidan su Humaira ta fada wa mahaifiyar ta tace shikenan zatawa Humaira magana taji ta bakin ta. Humaira na dawowa daga skul mahaifiyar ta ta shaida mata sakon Fahad inta amince a hada aurensu  da Basma, nan tace ta amince mahaifiyar ta tasamata albarka sannan ta kira Momsie ta shaida mata.



      *BAYAN WATA DAYA*

      An sha biki na gani na fada an kai Basma gidanta dake Abuja unguwan su daya da *ZYNAH* gida uku ne tsakanin su, Humaira kuma Zaria zata zauna gidan Abba dake a filin mallawa yaba Fahad saboda auren nasu yazo a kurarren lokaci, anyi shagalin biki lfy amaree sun tare, angwanai sunci angwacin su hankali kwance, Haydar ya dawo hutu ya pasa kai shidai a mai baiko da Islam, ai kuwa Daddy yace ya kwantar da hankalinshi indai Islam ce ya bashi,Islam waec result dinta ya fito ta samu admission a LASU (Lagos State Univerty) tana karatan social science, ginin hospital din *ZYNAH* saura kadan a gama, *ASHRAF* ya siya mata wani filin a nan Abuja zasu bude wani branch a wurin, Minal ta haihu inda ta samu namiji me kamada ubanshi sunsa mishi suna Muhammad sunan Daddy amma suna kiranshi da Ameer.



     *BAYAN WATA DAYA*

     An bada hutun school *ZYNAH* da *ASHRAF*  sun ci gaba da zamansu kaman yadda suka saba, kwana biyu kenan *ZYNAH* tana fama da ciwon kai, ga kasala da bacci, yau ta tashi da matsanan cin zazzabi, da amai ko ruwa tasha seya dawo, lokaci daya ta zabge da kyar *ASHRAF* ya labbata sukaje asibiti inda gwajin farko a shaida mishi tana dauke da cikin wata daya da kwana goma, ai murna wurin *ASHRAF* ba magana, nan ya rungumeta  yace "kin biyani only one", sannan ya sake ta yayi sujjudal shakur yana godewa ubangijinshi akan kyautar da yamishi, a haka suka koma gida ya shiga lallabata kaman kwai kome takeso ta samu, wani sabon soyyaya yake zuba mata, ita kuma se shagwabe mishi takeyi, duk da an koma school amma *ZYNAH* bata koma school ba seda cikin ta yayi wata biyar lokacin taji sauki sosai komai tana iya ci, lokacin da cikin ta ya kai wata takwas sukayi exam aka basu hutu kuma har yanzu ita take leading a ajinsu. *ZYNAH* tayi nauyi sosai yanzu cikin wata goma kenan amma haihuwa shiru hankalin ta duk yabi ya tashi *ASHRAF* ne ma yake dan kwantar mata da hankali, ganin cikin ya kai wata goma yasa su Ammi suka ce ta je gida haihuwa  da kyar *ASHRAF* ya yarda ta koma, wasa wasa seda cikin ta yayi wata goma sha daya sannan ta haihu, tasha wahala wurin haihuwa tareda *ASHRAF* suka shiga labour room cikin ikon Allah ta sambado yaranta maza en biyu kyakyawai dasu kaman babansu, ido da baki kawai suka dauko nata, anyi suna kaman ba gobe, *ASHRAF* yayi barin kudin nan yara sukaci sunnan Abba da Daddy wato Sagir da Muhammad ana kiransu Affan da Irfan.



     *BAYAN WATA SHIDA*

        Alhmdllh su *ZYNAH* an gama school kuma ta fito da first class upper, a gida tayi celebrating achievement din da ta samu Affan da Irfan sun girma sunyi wayo, Basma ta haifi er ta mace Ansa'u, Humaira ma mace ta haifa Afrah, Minal kuma tana dauke da ciki na biyu, an yi taron bude hospital a Lagos inda aka sama hospital din suna *ZYNAH MEDICAL CENTER*, ansa kwarrarun likitoci, inda branch dinsu na Abuja ma an kusa gamawa, yau asabar ya kama weekend *ZYNAH* da *ASHRAF* suna zaune suna zuba soyyayansu su Affan sunata guje gujen su sukaji ana dannan door bell, da kyar *ZYNAH* ta samu *ASHRAF* ya kyaleta ta tashi zata duba shikuma ya zauna yana jiran dawowan ta, bude kofan da zatayi taga KB tsaye a gabanta sanye da jallabiya fari kanshi sanye da hula, gaban ta ne yayi wani mummunan tsinkewa bakin ta na rawa tace "K K KB" ai *ASHRAF* najin ta ambaci KB se gashi a bakin kofa, kallon tsana ya dingawa KB sannan yace "me kuma kazo yi yanzu", sunkuyar da kai KB yayi yace " nazo neman gafarar ku ne, nasan nayi muku laifi amma dan Allah ina neman yafiyar ku, ku yafe mun, ba dan halina ba ku dubi darajar Allah da manzansa ko yafemin", kallon juna sukayi sannan *ASHRAF* yace "munji KB kuma mun yafe maka se fatan Allah ya kara shirya ka, ya shirye mu gaba daya ", yace " Ameen, nagode nagode", yana magana yana hawaye, gaba dayansu sun tausaya mishi, nan ya musu sallama ya wuce sukabi bayanshi da kallo cike da tausayi sannan suka koma ciki suna jimamin me yasamu KB yayi sanyi haka, nan kuwa horon da aka bashi a kurkuku ne yasashi nutsuwa. Suna zama ba jimawa message ya shigo wayan *ASHRAF* wai visa da passport dinsu ya fito na zuwa umara, se a lokacin yake gayawa *ZYNAH* murna tayi ta makalkaleshi tana jin dadi. Cikin sati biyu jirginsu ya daga se garin ma'aiki sedai muce Allah ya bada ladan ibada ameen.


*ALHAMDULLIH*

*NAN NA KAWO KARSHEN LITTAFINA MAI SUNA ZYNAH, KUSKUREN DA NAYI ALLAH YA YAFEMIN🙏🏻.*

*INNAYI KUSKURE KO NA FADA ABUNDA BA DAIDAI BA ALLAH YA YAFE MIN KUMA KU YAFE🙏🏻.*

*SAKON DA KE CIKI KUMA ALLAH YASA YA KAI INDA NAKESO YA KAI ALFARMAR ANNABI MUHAMMAD (S A W).*

*GODIYA DUBU GAREKI ASY KHALEEL, BA DAN KE BA DA BAN KAI INDA NAKEBA YAU, SOYYAYARKI DABAN YAKE ACIKIN ZUCIYA ZUCIYATA, LUV U LODI LODI HABIBTY😘.*

*MZZ ADAM, A B U, MARYAM B SANI, MARYAM FIZO, MEELA ADEEL, FATEEMA, SOPHIE,MEENEH PARROT, DEEJATOU, FATEEMA MUNNERA, AISHA M MU'AZZAM DA SAURAN DA BAN KIRA SUNANSU BA BAWAI NA MANTA KU BANE, KUNA NAN A RAI NA KULLUM DA KU NAKE KWANA DAKU NAKE TASHI, LUV U SOO MUCH PALS😘*

*MZZ DADDY'S NOVELS, ZYNAH FAN'S CLUB, MIEMIEBEE NOVELS GRP 2⃣, SOPHIE GRP, MUNNERA GRP 1⃣&2⃣, AISHA M MU'AZZAM GRP, KING BOY ISAH GRP, DANDALIN ASY KHALELE INA GODIYA DA HADIN KAN DA KUKA BANI, ALLAH YA BAR MU TARE😊*

*DUK WANDA BAN AMBACESHI BA BA WAI NA MANTASHI BANE*

_Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now