Chapter 12

1.1K 74 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

QUOTE:- "Just because the past didn't turn out like you wanted it to, doesn't mean your future can't be better than you ever imagined".

     _I dedicate dis page to my other half, my partner in crime nd lastly my one nd only trublsum  sisto *Halima aka me hancin shovel*😅 Allah ya nuna min aurenki musha budiri.😜

               1⃣2⃣

     Layi na  kaiwa kansu suka shiga Admin office din suka karba admission letter dinta sannan suka wuce bank dinda ke cikin school din biyan kudi. Koda suka shiga bank din akwai layi, Uncle Yusuf ya duba agogon  hannunshi kirar  Rolex yaga uku da rabi harda en mintina se yace mata " Kinga *BEAUTY* zumu wuje gobe in mun dawo se mu biya  kudin amma yanzu  lokaci  ya wuce" ta bata  fuska kaman tayi kuka tace " Uncle dan Allah mujira" be damu da yanayin ta ba yace "kalla tym,kuma laifin waye,nake ne,ke kika saura kina bacci har lokaci ya wuce, yanxu zaki  wani ce mujira a Karfe  nawa  kikeso  layi  yazo  kanmu" narai  narai tayi da ido kaman  tayi kuka tace "toh shikenan  Allah ya kaimu goben" ya amsa mata da "ameen" sannan suka fito ya juya wurin  Ashanty data  makale  mai kaman chewing gum (taga fyn boy lol) yace "Toh madam Ashanty mu zamu wuce amma gobe zamu dawo saboda akwai sauran aiki a gaban mu. So, se munzo gobe kenan ko" fuskan ta dauke  da murmushi  ga baki yaki rufuwa  kaman gonan  auduga tace "Allah ya kaimu, amma dan Allah in kunzo gobe kamin  waya maybe  u will need my help in one way or d other, tunda ni school din ba bako na bane","ok zan nemeki se goben, bye","bye" suka wuce, basuyi nisa sosai ba ya juyo  yaga  har yanzu tana nan inda ya barta  bata ko motsa ba ,se ya daga mata hannu tareda kashe mata ido daya aikuwa tayi suman tsaye tana kallon bayanshi harya bace mata.

     Suna zuwa bakin  titi  suka samu taxi suka shiga tareda fada mai inda ze kaisu, sun fara tafiya *ZYNAH* ta kalli Uncle dinta tace "Uncle it seems u ar  fond of dat Ashanty,ko itama zaka mayar da ita girlfrnd dinka","uhmmm nima  tunanin da nakeyi kenan after all  she's  beautiful,ko baki ganta ba doguwa ga kyau ba laifi gata  da dan haske kinga  yakamata in samu budurwa anan garin, ko me kika gani","nidai Uncle a tunani na ka kyaleta saboda she's still a student,yanzu take 300 level karka raba mata hankali gida  biyu" yayi  shiru ya tunanin  maganan niece dinshi can yace " shikenan zanyi  yanda kikace" taji dadi sosai ganin  ya karbi shawaran ta hannu bibbiyu tace " dats my Uncle" tareda bashi high five. Haka sukaci gaba da hira har suka kai hotel dinsu suka biya  me taxi suka wuce ciki kowa yayi dakinshi.

     Wanka tayi tareda alwallah tayi sallahn la'asar dayake  sunyi azahar a school sannan tasa evening  gown me spaghetti hands ta zauna a kan gado  tareda dauko waya har zatayi kira taji cikinta na kugi alaman yunwa, se alokacin ta tuna duk wannan budirin da suke tayi a school bataci abinci  ba banda  soft drink da cake din da Uncle ya matsa mata yace se taci wanda cake dinma  bata iya taci ba drink din kawai  tasha. Se ta tashi tasa wayanta charji ta dauki karamin veil tasa sannan tafita taje dakin Uncle Yusuf tasa meshi kan sallaya shima yanzu ya idar da sallah yace mata "Ya akayi *BEAUTY*" tace "Uncle yunwa nakeji","me zakici" tace "anytin" nan ya dauki intercom din dakin ya musu order din fried rice with chicken  da chips da exotic drink, cikin 10min aka kawo musu two plate kowa ya dau nashi amma *ZYNAH* duk wannan yunwan da takeji  bataci  ya kai spoon goma ba tace ta koshi amma ba laifi taci chips  din , dama Uncle yasan za'a rina yace seta kara ko five spoon, da kyar ta kara ya kira aka kwashe plates din ita kuma ta kuma dakinta ta dau wayarta ta kira Bestee  dinta ta video call suka sha hira suna fadama  juna  hw much dey miss each other, suna gama wayan  ta kira Islam  amma ba'a dauka ba, se da ta kira kusan so biyu a na ukun ne aka dauka tace "Islam ina kika  ajiye  waya  inata  kira","na shiga toilet ne, ya kike ya registration  din kun  soma" ," eh mun soma dazun ma munyi waya da Momsie  wai kina school","eh ta fada mun,wai kunyi waya da Daddy ma","eh munyi,so ya kike ba wani matsala a gidan ko","babu, zan kiraki  later  Momsie na kirana" bata jira me zatace  ba ta kashe wayan  a zuciyarta  tace "kece matsala  na dukda kinyi tafiya  amma har yanzu  Daddy beda  zance  se naki, i wish u neva  come  back"(wata  sabuwa inji en chacha). Itama *ZYNAH* ajiye wayan tayi tareda kwanciya  wanda  ko minti  goma  ba'ayi  ba  bacci  ya dauke ta  saboda gajiya.

**********
     Su *ASHRAF* sundawo daga open day inda suka sha complain kala kala akan Juwairiyya saboda shegen tsokana irin nata, sun dawo ya sauke  Sameer  gida sannan shima  ya karasa cikin  gida, yana shiga  direct part din Ummi ya shiga ya same ta a  kitchen itada Minal da yake rannan  girkinta ne yayi sallama suka amsa yace "Ummi naje school din dawowa na kenan","yayi kyau, me teacher dinsu tace?" ,"teacher dinsu Husna tace she's very intelligent  nd neat kuma tana da respect amma tana makeup in zatazo school saboda haka ta dena,nasu Juwairiyya kuma inji teacher dinsu wai tana  kokari amma  batajin  magana akwai ta da tsokana" Minal tace "Ai dama Husna akwai son kwalliya na mata magana har  na gaji" Ummi ta karba da cewar bari so dawo duk zan sasu a gaba in musu  fada sosai","Ummi ni  zanje na huta","kaci abinci ne","a'a amma banjin  yunwa","toh  a huta lfy" ya fita zuwa bangarensu,sukuma  sukaci  gaba  da aikinsu.

**********
     Yau ya kama Tuesday wanda  *ZYNAH* tun da asuba data tashi bata koma barci  ba gudun karta makara irin na jiya, by 8 duk sun shirya suka tafi school din,suna zuwa suka biya kudin saboda ba layi sosai, suna biya suka fito Uncle yakira Ashanty saboda ta nuna musu coordinator's office,ba jima se gata sukayi en gaishe gaishen su tayi leading  dinsu zuwa office din aka mata signature sannan akace  su dawo gobe saboda HOD dinsu baya nan kuma suna bukatan signature dinshi. Haka suka hakura amma ran Uncle ya baci saboda alla alla yake sugama abunda ya kawosu su koma saboda akwai aikin da ke jiranshi  amma dole su hakura. Haka suka koma hotel din dan su samu hutu itako *ZYNAH* waya ta dauko tana buga _Candy crush_ dan ita hankalin ta kwance ganin sunkusa gama abunda ya kawo su.

**********
     Sameer ne ya shigo dakin *ASHRAF* amma baya ciki sedai da alamun yanzu gama drawing ya tashi daga wajen, zuwa yayi kusa da sketch board din se yaga mace ce a garden tana zaune da littafi a hannun ta da alamun karatu takeyi sedai yanda ta yafa veil dinta yasa ba'a ganin fuskan ta. Yana cikin nazari hoton *ASHRAF* ya shigo dakin Sameer yace "guy nice drawing" murmushi kawai yayi tareda  cewa "She was in my dream again last night, i  think she's  trying to pass me an information" Sameer  yayi dariya yace "nd wat if ba mutum bace aljanah ce" *ASHRAF* ya harare shi yace" Allah ma bazesa  inga aljanah  ba" shidai Sameer bece  komai ba in banda dariyan  keta  da  yake mishi.

     _Kuyi hakuri da wanna ba yawa_ 

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now