Chapter 13

1.2K 72 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

QUOTE:- "You know when you're in love when you can't fall asleep because reality is finally better than your dreams."

     _I dedicate dis page to a frnd who is ready to sacrifice  nd devote her tym just so she could help me b more successful  while writing  dis novel *Meela Adeel* my habibty her comes ur page,wit much luv 😍_

                1⃣3⃣

     "Guy wani rumours naji dana shiga site din school dinmu wai dis tym around kai za'a bawa president din department  dinku while wannan figaggiyar yarinyar nan Rahma itace vice dinka". Sameer kenan yake  fadama *ASHRAF* abunda ke shirin faruwa bayan  ya gama yi mai dariya akan  wai yana mafarki  da aljannah. Cike da mamaki *ASHRAF* yake saboda labiran da yaji yanzu danshi iya saninshi ba'ayi  vote ba tunda se anyi vote sannan kuma shi bece ze fito takaran  presidency  a department dinsu ba not to talk of ace harya  ci, abunda ya matukar daure mai kai kenan, cike da mamaki ya kalli abokin  nasa wanda  shima shi yake kallo sannan yace "Yaushe na fito takara har akayi vote har naci da ni bansani ba?" ,"ka manta sanda KB yace yanaso  kazama president  dinsu saboda yanda yake sonka  har yakeso  yayi  abota  da kai amma baka bashi  face ba" ," wen will dis f*cking KB stop getting on my nerves, ana dole abota, y would he want me to b d president" yana magana ne ranshi a bace" Sameer yace "cool guy, karka dau abun da zafi" ,"bangane kar indau abun da zafi ba, nasan he's  doing all dis just to get closer to me nd i will neva give him dat chance".

     Ajiyar zuciya Sameer ya sauke sannan ya kalli abokinshi  tareda dafa kafadan shi sannan yace "Bros calm down nd  listen to me" *ASHRAF* yayi shiru amma daka kalli shi kasan har yanzu ranshi a bace yake, ganin haka yasa Sameer ya dauko mishi bottle water a fridge me sanyi ya bude mishi sannan ya mika mishi, karba yayi tareda kafawa a baki wanda tunda ya kafa be cire daga bakinshi ba saida ya shanye rufan tas sannan  ya mukurkushe roban da hannunshi tareda  seta dustbin ya wurga roban ciki yana  sauke numfashi alamun yasamu  relief (niko nace  tirkashi  dama haka *ASHRAF* keda sauri hasala  lalle kuwa akwai rigima😳). Seda Sameer ya tabbatar ya nutsu sannan yace " Y won't u give him a chance to become ur frnd? atleast ina lefin  me sonka" wani kallon ko wannan  yafara zuka ne (lol) *ASHRAF* yama Sameer kafin yace " kanada lafiya, kasan  abunda kake fada, mutumin  da besan inda yake mishi ciwo ba, be son karatu se aukin  bribing lecturers saboda his dad is filthy rich nd dey  don't give a darm, yaron da ba abunda  baya sha nd wurin neman mata he's an expert, duk school an sanshi  to d  extent dat akayi  naming dinshi  baddest boy in school, shine zakace inyi  befriending dinshi saboda me?, in an ganni dashi acemin me, uhm".

     Cikin sanyin murya Sameer yace "kaga ni ba abunda  nake nufi ba kenan, ni gani  nayi  in ka ja shi a jiki u will b able to change him in ur own ways, bt since u don't want dat i  won't force u" cikin halin ko in kula da maganan Sameer yace "ni yanzu ba wannan ne matsala na ba, ka san yanada fans sosai kuma saboda haka cikin sauki zesamu en goyon baya subani wannan post din, ni yanzu tunani abunda zan mai da zesa ya janye ra'ayinshi  cikin ruwan sanyi nakeyi"," babu wani abunda zaka mai illa ka kirashi so dat u two can have a man to man talk" ," I don't have his number"," I will get it for u" saboda *ASHRAF* ya nutsu yasa Sameer yakara da cewa "muje mu buga golf,da zan shigo naga  Hamma Haydar zeshiga game room nace mai nima ina  zuwa","tafi  kai kadai shima fada mukeyi dashi","shikuma me yayi","cikin  maye ya shigo gidan nan jiya yazo yazube  a  parlour  yana  bacci nina kai shi dakinshi,da safen ina mishi magana yana nunamin shi a kyaleshi abunda  yaga  dama  shi  zeyi" ,"Hummm toh  Allah ya kauta, nidai na tafi dan na dade  ban buga golf ba","adawo  lfy". Sameer ya mike yafita  yayinda *ASHRAF* ya kwanta  tareda zubawa yarinyar da yayi draw ido yana zancen zuci,ya dade yana kallonta sannan a fili yace "y won't u show urself to me" tareda lumshe ido kaman me bacci amma a zahiri  ba bacci yakeba.

**********
       *Lagos, 5:35pm*

     "Wai ni Islam meke damunki kwana biyunan ne, kwata kwata yanzu bakida kumari, u'r  looking doll nowadays, da safe da kin tashi zakici  breakfast ki wuce school, da rana in kin dawo da kinci lunch se kishige  daki bazaki kuma lekowa  ba har dare,abinci dare ma se an nemeki, dan hiran  daren  da  mukeyi  a parlour kin daina zama meke faruwa" Momsie ce ke neman ba'asi game da changes dinda tagani tattare da Islam (haka akason uwa ta gari, da zarin taga wani hali da batasan ýaýenta dashi  ba to ta tambaya kila  akwai  abunda  ke  damunsu,Allah yasa Mudace Ameen) dagowa Islam tayi ta kalli mamanta tace "do u want to knw d truth"," yes of course","Daddy ne matsala na Momsie, shine ne babban matsala na a gidan nan" baki bude Momsie ke kallonta " me kike nufi  da  babanki  ne matsalan ki"," Momsie nasan  u've notice tun ba yauba Daddy na nuna mana banbanci tsakanin  ni da Sister but i've always try to hide my feelings of being disappointed by my Dad amma even today da Sister batanan still beda wani magana se nata nd dats wat hurts me d most" ta karashe zancen ta hawaye ya  gangaro wa kan beautiful cheeks dinta.

     Goge mata hawayen Momsie tayi tareda bata cool bt warm hug,ita da kanta tasan tama Daddynsu magana ba sau daya  ko biyu  ba amma yakiji, gashi abunda take tsoro na shirin faruwa wato kiyayyar *ZYNAH* a zuciyan Islam. Seda ta tabbata ta samu nutsuwa sannan tace "don't worry i  will  talk  to ur Dad am sure he will stop, he's fond of ur sister badan komai ba but  saboda  sunnan Mamanshi ne da ita nd for ur information u ar nt a disappointment to anyone in dis house, so chill" kada kai kawai tayi badan ta gamsu da maganan Momsie ba. Mikewa Momsie tayi tareda cewa "do u mind joining me in d kitchen i  need to finish up wat i've started for dinner","No Momsie, i  need  to study for tomorrow's paper","Ok,good luck"sannan ta fita itakuma ta kwanta tareda rungume teddy dinta a yayinda different thoughts ke zuwa mind dinta tareda rudin shedan. 

**********
       *Zaria 6:05pm*

     *ZYNAH* ce da Uncle dinta suna kallon new episode na _Jennifer's dairy_ se dariya suka suna gama kallo *ZYNAH* tace " Uncle indan muka gama komai da komai zamu biya Kano wurin granny" ya kalleta  yace "Kiyi addu'a by thursdta mungama komai dan naga alaman school dinnan  sunada  renin  hankali, in mun samu by Thursday mungama komai se muje muyi mata kwana daya" cike da jindadi tace "yehhh dats my uncle" shidai murmushi  yayi saboda yana ganin yarinta tattare da *ZYNAH* sosai. Suna cikin haka aka kira sallah ta wuce dakinta  shi kuma  ya tafi  masallaci dan akwai masallaci a layin.

*WASHEGARI*
     Sunyi koman su da wuri suka tafi school din, koda sukaje be kira Ashanty ba saboda yanaso yayi amfani da shawaran da *ZYNAH* ta bashi. Wani saurayi suka tambaya yanuna musu inda zasu samu HOD din sukaje cikin ikon Allah suka samu ba kowa ya amshe  su hannu bibbiyu dayake mutum  kirki ne shi sannan yamata stamping files dinta yana cewa ta burgeshi karaman yarinya da medicine ai is nt an easy course ya nata jajanta  kokarin ta, da haka suka gama suka fito, me zasu gani Ashanty ce zaune tana jiransu  dayake  taga  shigowansu "Ina kwana" ya amsa da "lfy lau" itama *ZYNAH* ta gaisheta ta amsa tana murmushi tace "naga shigowan ku ne amma nayi  mamakin da baka kirani ba shine nace bari nazo naji  ko lfy" yana dan murmushin  sa yace "wayan  ba call card se naje waje zanyi recharge","Ok, toh yanzu meya  rage muku" yace "daki ya saura mu sama mata amma mun gama  komai" tace "perfect timing, dakin da nake a hostel dinmu room  of  4 ne ni da wata kawai  ne a ciki for nw, y  nt tayi joining dinmu" ya kalli *ZYNAH* yace "do u buy d idea" cikin jindadi ganin zata zauna da wanda tasani yasa  tace "y nt" haka dai sukayi komai  da  komai  na bukata ranan, Seda ya tabbata  registration ya kamallu sannan suka wuce bayan ya ci kama Ashanty purse dinta da kudi.

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now