Chapter 32

1.1K 72 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Love is the rhythm of two HEARTS beating as one. Sometimes love means to stop where we are and start where someone needs us…."

              3⃣2⃣

     *BAYAN KWANA UKU*

     Sun gama exam lfy kuma *ZYNAH* ta fito da point me kyau wanda yasa lecturers sukata yabama kokarin ta, dan a department dinsu ita ta dau over all  student, ba karamin murna iyayenta sukayi ba, hatta *ASHRAF* seda ya hada mata small party, daga shi se ita, sekuma Sameer, KB kam shi ba magana dan cewa yayi zasuyi celebrating success dinta daga shi se ita wanda har tagama numfashi a doron kasa bazata mantashi, (toh, ta Allah ba takaba). Yau yakama asabar kuma a ranan su Momcy zasuzo Zaria daga nan su tafi da *ZYNAH* se kuma in an dawo daga hutu zata dawo wanda dawowanta zeyi daidai da komawarta gidansu *ASHRAF*. Sun sauka a Kaduna suka samu mota ya kawo su har kofar ABU kiran wayanta sukayi tace "gatanan zuwa".

     "ka make sure ka kawo min yarinyar nan guest house din yau, tunda na nuna inasonta itakuma ta nuna min tsana, toh kuwa zata gane kuranta, sena nuna mata cewar *Kabiru Sani Paki* baya neman abu ya rasa,komai yakeso seya samu", SMART ya amsa da "sure boss", wurin gate din school din yaje yayi parking motanshi, yana zaune ciki da yake ba mutane sosai duk an fara komawa gida, hango ta yayi tana zuwa yayi sauri ya fito daga motan tareda sa face cap dinshi seda ya kalli ko ina yaga ba kowa wurin sannan ya fara tun karar ta tareda ciro wani handkerchief a aljihun shi, yanata bin  ta abaya saura kadan ya isa yaji tayi ihu tana "Momcy!!" tareda daga hannunta sama, kallon inda take kallo yayi dan yaga wa take dagawa hannu, hango wasu mutane yayi wanda kafin ya dawo da idanunshi kan *ZYNAH* har ta karasa wurin su tareda hugging dinsu, "shittt" abunda yace kenan tareda komawa cikin mota da sauri yana kallonsu, steering ya daka sannan ya dauko wayanshi yace kira KB, "hello boss", "hello SMART ya akayi ka sameta", "no boss, saura kadan in aikata abunda zanyi, senaga wasu sun zo wurin ta wanda da alamun iyayenta", "damn it", abunda KB yace kenan tareda wullar da wayan a kan gado yana yamutsa gashin kanshi. Seda yayi 15min a haka sannan ya dau waya ya kira SMART, "hello SMART dawo kawai, der is nthn we can do nw", "okay boss". SMART na dawowa yace "kasan me, na yarda nayi losing dinta for nw, amma ai zata dawo in hutu ya kare, by den i would hav a greater plan for her", SMART yace "hakane boss", sallaman SMART  yayi amma yakasa samun nutsuwa, fridge dinshi ya bude ya dauko giya, seda ya kwankwade kwalba biyu sannan yana tangal tangal ya koma kan gadonshi ya zube ragwab akai yana gyatsa, ba dadewa barci ya daukeshi.

     "Momcy, daddy, i missed u sooooo much", Daddy yayi murmushi tareda shafa kanta yace "we missed u more swthrt", murmushi tayi itama tareda kara lefewa jikin Daddy, Islam kuwa tuni ta gama kumbura ganin yanda suke wani nan nan da ita, *ZYNAH* ce ta lura da yanayin Islam tace "Lil sis lfy?, meke damunki?, naga kina bata fuska", "ba komai kaina ne kedan ciwo", ehyya sorry", Momcy tace "kila gajiya ne, kinga *ZYNAH* dauko kayanki mu tafi", Daddy yayi saurin cewa "Islam bita ku dauko tare", Kara bata fuska tayi tace "Daddy kaina fa na ciwo", hade fuska yayi yace "zaki wuce ko kuwa se ranki ya baci", tana gunguni tabi bayan *ZYNAH* wacce se mamakin Islam takeyi ganin yadda ta canza da kuma ganin yanda Daddy da Momcy ke mata. Suna shiga Islam ta kalla dakin  tsaf sannan tace "sister is dis wer u leave", "yes, me kika gani", "ba komai, d room looks nyc", *ZYNAH* tace "greet my room mate", kallon Ashanty Islam tayi sannan tace "Hi", cike da mamaki *ZYNAH* tace Islam wani irin gaisuwa ne wannan, just hi nd dats all", "toh me kikeso nace?", yanzu kam ran *ZYNAH* yagama baci, cikin daga murya tace "Islam behave urself will u, yaushe kika canza gud habit dinki haka, in ni bazaki gaishe ni saboda kina ganin ban isa ki gaishe ni ba, itafa, ko dan kin ganta da karamin jiki, toh ta girme ni, so behave urself nd give her a proper greeting ryt nw", Islam kallon *ZYNAH* tayi daga sama har kasa sannan tace "nd who is talking", sannan taja trolley daya tayi waje, batare da takara magana ba. Juyawa *ZYNAH* tayi wurin Ashanty dake hada kayanta itama tace "Ashanty am sorry, i don't knw wat has gotten into her, she was nt lyk dis, she was neva lyk dis", murmushi Ashanty tayi sannan ta taso tazo gaban *ZYNAH* tareda dafa kafadanta sannan tace "u don't hav to make a big deal out of it, it's okay, after all i hav a sister who is just as naughty as she is", murmushi *ZYNAH* tayi tareda hugging din Ashanty tace "in dat case i will b going, sekuma an dawo school", Ashanty tace "yeah but will keep in touch ryt?", "sure", murmushi sukayi gaba dayansu sannan taja ragowan kayanta tayi waje tareda dagawa Ashanty hannu.

ZYNAHWhere stories live. Discover now