Chapter 47

1K 65 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"There are moments in life when you miss someone so much that you just want to pick them from your dreams and hug them for real."

     _I dedicate dis page to *Mzz Daddy's Novels* i hrt u members❤😍_

                4⃣7⃣

     Fahad koda yakai parlourn Abba kasa shiga yayi dan besan daga ina ze farawa Abba bayani ba, yayi kusan 15min a wurin sannan dayaga tsayuwan ba solution bane yayi karfin hali ya kwankwasa, "come in", akace daga ciki ya murda handle din kofan ya shiga sallama dauke a bakinshi, amsa mishi Abba da Daddy sukayi, ya nemi wuri a kasa ya zauna tareda sunkuyar da kai kasa yana wasa da azufarn hannun shi, Abba ya kalleshi yace "Fahad ya akayi, da magana ne", "eh Abba daman nazo ne akan maganan nida *ZYNAH*", sekuma yayi shiru, Abba da Daddy suka kalli juna sannan Abba yace "me yasami kai da *ZYNAH* ince dai ba wata matsala koh", "a'a Abba ba matsala dama nazo ne dan na gaya muku na hakura ni banzan iya aurenta ba", cike da mamaki Abba da Daddy ke kallonshi, Abba yace "kan ka daya kuwa Fahad, ko dai kaje ka sha kwayoyin ka ne zakazo kace bazaka iya aurenta ba, karka mai damu mutanen banza mana, kaida kanka kazo kace in nema maka aurenta a wurin iyayenta, na maka gata na nema maka kuma zakazo kace kai bazaka iya aurenta", duk wannan maganan da Abba yakeyi Fahad kanshi na kasa gumi se karyo mishi yakeyi, Daddy yace wa Abba "a'a tsaya bazamuyi haka ba, kila yanada dalili", juyawa yayi wurin Fahad yace "Fahad meyasa bakaso ka aureta kuma, ko ta maka wani abunne", girgiza kai yayi yace "a'a ba abunda tamin", Daddy yace "toh meyasa ka canza ra'ayin ka", kallonsu yayi sannan ya sauke kanshi kasa yace "saboda tanada wanda takeso, kuma na gida ne", Abba da Daddy ne suka kalli junansu sannan Abba yace "na gida, waye shi?", kanshi a sunkuye yace " *ASHRAF*", Daddy yayi mamaki sosai ganin *ZYNAH*na da saurayi amma bata taba fada mishi ba, ko mahaifiyarta bata fadawa, nan basusan cewar ita da kanta *ASHRAF* be dade da propose mata ba, Abba ne ya gyara zamanshi tareda cewa "lallai kuwa biri yayi kama da mutum, ashe shiyasa ya takura min se na kawota gidannan", Daddy kallon Fahad yayi yace "toh kai yanzu kana nufin zaka hakura kenan, kabarwa kaninka", "eh abunda zanyi kenan", Abba ne ya kallo shi sannan yayi murmushi yace "am proud of u son, ka nuna min kayi hankali yanzu wanda ko bayan raina zaka iya rike mun gidana, tunda kace kai ka janye, ba damuwa Allah ya maka albarka", juyawa Abba yayi ya kalli Daddy yace "toh kai mezaka ce, kaba *ASHRAF* er ka kokuwa", murmushi Daddy yayi yace "nabashi mana, ai bazanki bashi ba", murmushi Abba yayi yace "nagode da wannan karramanin da kakeyi, Fahad tashi kira mun *ASHRAF* da *ZYNAH*, tashi yayi jikinshi ba kwari ya fita daga parlour.

     Humaira da Basma ya hango zasu fita yace suje sucema *ZYNAH* Abba na kiranta, amsawa sukayi da toh sannan suka juya suka koma ciki dan su kirata. Dakin *ASHRAF*   Fahad ya shiga tareda sallama, yana shiga *ASHRAF* yaja pillow ya rufe fuskanshi saboda baya son Fahad ya gane halin da yake ciki, murmushi Fahad yayi yace "in ka gama boye fuskan kaje Abba na nemanka", Fahad na fita *ASHRAF* ya tashi ya shiga bathroom ta wanke fuskanshi sannan ya fito ya nufi bangaren Abba amma kowa ya kalleshi yasan yana cikin damuwa, kusan a tare suka kai shida *ZYNAH*, zama sukayi a kasa Abba yace "yanzu Fahad yazo min da wata mata, inaso na tabbatar koda gaske ne, kai *ASHRAF* fadamun gaskiya akwai soyayya tsakanin ka da *ZYNAH*, dagowa yayi yace "Abba...", be karasa ba Abba ya katse shi yace "eh koh a'a", kasa yayi da kanshi sannan yace "eh", Abba yace "toh Alhmdllh, inaso kasani *ASHRAF* yau Fahad ya sadaukar da soyayyan da yakema *ZYNAH* saboda kai, saboda haka ka riketa amana kana jina", "Insha Allahu Abba", "ke  kuma *ZYNAH* Allah yayi albarka dan kin cika er halak saboda duk da kinada wanda kikeso amma baki nemi ki bijirewa maganan mahaifinki ba, wannan yana nuna cewar kinsan darajar iyayenki, Allah yayi miki albarka", "Ameen suka amsa sannan aka sallamesu suka bar falon cike da murna ban da Fahad da karfin hali kawai yakeyi.

     *ZYNAH* daki ta wuce saboda taga alaman Fahad da *ASHRAF* sunaso su gana, saboda haka ne yasa bata tsaya ba, *ASHRAF* ne ya riko hannun Fahad dake nema ya kara gaba ya tsayar dashi, juyowa Fahad yayi *ASHRAF* yace "y did u do dis?", "bcos u ar my brother nd i can't wait nd see my brother suffering bcus i took wat doesn't belong to me, am nt in d ryt position to own *ZYNAH'S* luv bt u ar, so plsss take care of her cus she deserves to b happy", *ASHRAF* dake hawayen farin ciki  yace "hw did u knw i luv her, hw did u find out", "i heard ur conversation wit Minal earlier, look don't worry abt me nd move on wit ur luv story", murmushi *ASHRAF* yayi yace "thanks bro, u ar d bst", rungume juna sukayi sannan Fahad yace ze dan je ya kwanta, daki ya tafi amma barcin yaki zuwa se juyi yakeyi akan gado, ganin ba iya barcin zeyi ba yasa ya tashi da dauko  codeine  dinshi da ya boye a cikin drawer ya fito ya nufi garden. *ASHRAF* yana shiga daki ya dauko wayanshi ya kira *ZYNAH* sukasha hiransu, kowannensu naba dan uwanshi lbrn halin da ya shiga a lokacin da sukaji wai da Fahad aka hadata, tana tsaye a jikin window ya hango wucewar Fahad, excuse  tabama *ASHRAF* tace tana zuwa taza kirashi, tana kashe wayan ta fito zuwa garden dan taje tama Fahad godiya wanda yana nan zaune yana kwankwandan codeine, ganinta ne yasa yayi sauri ya boye a bayanshi cike da kunya yace "ban bata jin ina kunyar shan kayan maye ba se yau, ban taba nadaman shansu ba se yau, kuma ban batajin zan dai sha ba se yau, dan wlh ganina da kikayi ina sha ba karamin kunya naji ba, kuma Insha Allahu daga yau na bari", murmushi tayi tace "Alhmdllh tunda ka bari amma ka tabbata baka karasha ba", "ai tunda nace miki na bari na bari kenan", murmushi tayi tace "toh Alhmdllh, dama na zo ne in maka godiya, na gode sosai da ka iya ka tunkari su Abba da maganan mu, kaima Allah ya baka mata ta gari, me sonka", "Ameen" ya amsa mata yana kallonta sannan ta mishi sallama tashiga gida. Su Ammi sosai sukaji dadin abunda Fahad yayi saboda ya nuna musu yayi hankali yanzu kuma ya rike girman shi a matsayinshi na babban yaya.

*BAYAN SATI DAYA*

     Su *ZYNAH* sun koma Lagos dan acan zaka karashe hutunta saboda hutun nada tsayi, inda kullum tana makale da waya a hannunta suna soyewa da *ASHRAF* dan soyayyar su ba abunda ya ragu sema abunda ya karu, Minal da Uncle ansa rana nan da wata biyar za'asha biki in da Momsie yabawa kudin da zata hada lefe kuma yace inta tashi tafiya tareda Minal zata, a Dubai zasu hado lefen, Granny ta dawo Lagos at last dan kafin su dawo Lagos seda suka biya Kano suka daukota da sunan kwana biyu kawai zata musu amma gashi anci sati sunki su mayar da ita se mita take musu, Sameer da Basma abu se cigaba yakeyi saboda har iyaye sun shiga maganan an san da zamansu, fili an samu an kwato inda Uncle yayi investigating  mutunin kuma ya gano dirty business yakeyi na siyan kaya hannun yara a wulakance ya maida su nashi, Islam da *ZYNAH* sun dawo kaman yanda suke da abu gwanin ban sha'awa a yayinda suka pape ita da Kamal kwata kwata ta daina shiga harkanshi, ko kulashi batayi inda ita da Haidar shakuwa me tsanani ya shiga tsakani.

*BAYAN WATA UKU*

     *ZYNAH* ta koma school inda soyayyar su da *ASHRAF* yana nan kullum sabowa fil da ita, anyi posting dinsu *ASHRAF* youth service inda aka turashi Abuja badan yaso ba yatafi sedan ba yanda ya iya,  *YOUNG ARTIST FOUNDATION* aka tura inda yarane matasa daga 14yrs zuwa 20, maza da mata ne a wurin wa'anda sukade talent din drawing da painting, Fahad ya gama service dinshi inda Abba yace yayi aiki a karkashin shi tunda accounting ya karanta, be musa ba ya amince dan a yayan Abba ba wanda yake taimaka mishi a fannin business dinshi kuma gashi ya fara manyanta, saboda haka yanzu shi yake kula da fannin lissafi inda duk wani kudi da ze shigo ya fita ta wurin shi yake shigowa kuma ta wurin shi yake fita, kuma yana aikinshi tsakani da Allah baya dubawa wai dan kudin mahaifinshi ne ya dinga damfarewa, Islam yanzu ana kokari dan last exam din da sukayi ita ta dau na biyar inda Daddy har waya da laptop ya canza mata saboda tayi kokari, Humaira dai tayi move on duk da kullum son *ASHRAF* kara shiga ranta yakeyi amma batada wani hanya da zata iya bi, gashi KB tun randa ya kirata har yau shiru, Minal da Uncle ana nan ana shirye shirye biki saura wata biyu, Sameer a Kano akayi posting dinshi inda yake service dinshi a wani construction company na gwamnati, Islam da Haidar se abunda yayi gaba, dan Haidar kafin ya koma school seda yaje wurin Abba waishi a duniya beda matar data wuce Islam saboda haka ayi musu baiko kafin ya koma school kar wani ya rigashi, Abba koranshi yayi yana cewa dan tsabar rashin kunya karamin yaro dashi waishi a mishi baiko, a ranan daga Ummi har Ammi seda sukaja kunne shi sukace saura inya koma school kar yayi karatu, *ZYNAH* yanzu tana karatun ta cikin kwanciyar hankali saboda ba KB, yanzu itada da Shaheeda suna 200level inda Ashanty take 400.

*BAYAN WATA BIYU*

     _Ina mai gayyatar ku zuwa wurin taron bikin star boy dinmu Uncle Yusuf da swthrt dinshi Minal wanda ze kama a rana kamar haka 15oct, 2017 karku bari a Baku labrin bikin saboda bikine na manyan mutane, gwara kuje ku kashe kwarkwatan idonku.😜_

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now