Chapter 24

1K 61 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITERS ASSOCIATION*

QUOTE:-"Some people pass through our lives in a shorter time frame than we had hoped to teach us things they never could have taught if they stayed."

     *Ina mai ba fans hakuri akan rashin jina da bakuyi ba kwana biyu saka makon rashin lfyn da nadanyi. Amma yanzu ina mai tabbatar wa fans cewar na samu sauki (Alhmdllh) kuma zaku dinga jina akai akai In Sha Allah. Much luv💋*

     _I dedicate dis page to my frnd whom i so much care for *Raheenat* her is a page for u.😍_

                 2⃣4⃣

     Yau kusan wata daya kenan da faruwar wannan al'amari wanda KB yayi shiru ya fita daga harkar *ASHRAF* kaman ba abunda ya faru wanda yasa *ASHRAF* da Sameer mamakin KB kenan dukda ba alamar shiryuwa a tattare dashi amma kyalesu dinda KB yayi be rama ba yasa suma suka saki jiki sukaci gaba da harkokinsu whereas *ZYNAH* tana nan tana karatunta itama amma ta dan rame (dama abu ba jiki ba) saboda karatun medicine ba easy bane haka zalika  zaman hostel shima ba sauki bane a wurinta dan ayyukan da batayi a gida yanzu tana yinsu, irinsu wanki da girki dukda ba wani girki ta iya ba banda indomie da taliya se white rice ba abunda ta iya kuma, da batason cin abinci amma yanzu dole tasa tasoma ci. On d other hand kuma SMART na nan yana bibiyar ta duk inda zata yana wurin sannan ya samu wata a hostel dinsu ya biyata kullum in *ZYNAH* ta koma hostel itace me kawo masa labari, wannan bidirin duk *ZYNAH* batasan anayi ba. Tun wannan ranan da suka rabu da *ASHRAF* bata sake sashi a ido ba amma kullum dashi take barci dashi take tashi wanda shikuma *ASHRAF* a kullum baya barin school se ya tabbata yasata a ido koda sau daya ne amma be taba tunkararta ba.

     Yau ya kasance alhamis, tun safe da *ZYNAH* ta tashi takejin matsanancin ciwon mara amma ta daure saboda bataso tayi missing  lectures. Koda taje lecture hall dinma bata tsinta komai ba dan kuwa ciwon da maranta keyi baze bari tayi concentrate ba. Shaheeda ta lura da yanayin ta amma tayi shiru saboda lecturer din is strict bayason surutu, yana gamawa ya fita Shaheeda tayi sauri tajuya wurin *ZYNAH* tace "babe lfy, kinata rike kasan cikinki ga zufa kina tayi" da kar take iya magana tace "Shaheeda  plss take me back to d hostel, mara na, ciwo" cike da tausayi Shaheeda tace zaki iya tafiya?" kai kadai ta iya daga mata sannan Shaheeda ta taimaka mata ta tashi, tana rike da ita suna tafiya a hankali har suka kai hostel din suka shiga daki Ashanty kadaice a ciki, suna shiga *ZYNAH* ta zauna ta cire kayan jikinta tasa marasa nauyi sannan ta dauko menstrual pain reliever tasha, Shaheedah ta korowa Ashanty cewar *ZYNAH* ba lfy ta mata sannu cikeda kulawa, tana gama shan maganin ta kwanta rikeda mara tana sauke numfashi, duk wanda ya kalleta yasan tanajin jiki, ba dadewa barci ya dauketa Shaheedah tawa Ashanty sallama ta wuce tareda alkawarin zata dawo da yamma ta dubata.

     Tashi tayi saboda wani azzazaben ciwon da taji, hannu bibbiyu tasa akan maranta, tun tana birgima a kan gado har ta sauko kasa kan carpet ta kwanta dukda sanyin wurin, ga fuskan ta nan hawaye duk sun wanke shi addua kawai takeyi duk abunda ya fito daga bakinta karantawa  take ga ba kowa a dakin. Tana cikin wannan halin sega Ashanty ta shigo, a rude ta nufeta ganin halin da take ciki. Kiranta ta shiga yi amma inaaa *ZYNAH* ta riga ta fita daga hayyacinta batamasan wake kanta ba, Salati Ashanty ta ringayi ta tashi zata fita neman taimako sega Shaheeda nan Ashanty ta labarta mata halin *ZYNAH* ke ciki itama ta shiga dan ganema idanunta amma abinda idonta ya gane mata seda ta zubda kwalla. Kallon Ashanty tayi tace "mu kama ta mu kaita hospital" ,"a'a zauna nan bari nasamo mota a kaita tunda bazata iya tafiya" kai kawai Shaheeda  ta kada Ashanty ta fita da saurin ta, wajen wata course mate dinta kuma kawarta taje dayake kawar nada mota, rokonta tayi tace dan Allah ta taimaka ta kaisu hospital, nan dai kawar ta yarda sukaje suka dauko *ZYNAH*, Shaheeda  da Ashanty  na rike da ita suka sata mota, ko kafin sukai hospital din harta sume musu a mota Allah ya taimake su hospital din a nan cikin school din yake. Suna zuwa akayi sauri aka karbeta sukayi emergency da ita, su Ashanty kuma suka tsaitsaya anan Shaheeda banda kuka ba abunda takeyi Ashanty na lallashinta.

ZYNAHWhere stories live. Discover now