Chapter 34

974 64 2
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Just cause you're sleeping with someone doesn't automatically make them yours! If there's no commitment then it's all fair game!!"

                3⃣4⃣

      *ONE WEEK LATER*
     A kwana a tashi ba wuya ga mai rai, gashi har anci sati daya da yin hutu, saura sati daya a koma dan hutun sati biyu aka basu, *ZYNAH* tunda ta dawo bata fita wai se ta wuta, toh yau Saturday kuma yau takeso tafara fita gaishe gaishe, kafin daya tayi harta gama abunda zatayi ta shirya cikin wani pink material gown da black veil me touches of pink a jiki, hand bag da flat baby shoe dinta ma black ne,  sosai tayi kyau dukda ba wani makeup tayi ba illa powder da lip gloss, hoto ta dinga dauka tana dorawa a watsapp story, snapchat, da instagram, fita tayi tashiga dakin Islam saboda Islam ta dauke ta hoto sosai amma kememe ta kwanta kaman me bacci kuma idonta biyu, ganinta a kwance yasa *ZYNAH* barin dakin dan a tunanin ta Islam bacci take. Dakin Momcy ta shiga ta sallameta sannan ta sauko kasa inda taga Daddy zaune dayake weekend ne yana gida, "Mamana se ina?", "Daddy zanje ziyara ne", "ok Allah ya bada ladan ziyara", "Ameen" ta amsa mishi dashi sannan tayi mai sallama, harta kai bakin kofa ya kirata take dawo ya dauko 5k ya mika mata yace "gashi kisha mai", "a'a Daddy daka barshi akwai kudi a hannuna", "ai nasan da kudi hannunki na baki, saboda haka karba ki kara", karba tayi ta mishi godiya sannan ta wuce. Parking lot taje taga motanta an wanke matashi se kyalli yake, karasawa tayi tareda shafa jikin motan tace "i miss u my dolly", shiga tayi ta bar gidan cike da jin dadi yau zataga gari.

     Tana fita bata tsaya ko ina se gidansu Humaira, taje ta gaishe da Ummin Humaira sannan ta wuce dakin Humaira wacce itama tagama shiryawa, fitowa sukayi tare sukama maman Humaira sallama suka fita, ziyara sukayi sosai, duka classmates dinta na secondary school seda sukaje suka gaishe da su. Sunje *AMARACHI ND SISTERS HOUSE OF FASHION* sukayi gyaran gashi da farce, sunje *ZEE MAMA'S BOUTIQUE* sukayi siyayya, sunje *SHOPRITE* nan ma sukayi shopping sosai, *ZYNAH* dai taki jin magana dan kayan zakinda ba'aso tasha shi ta dinga kwasa, suna fitowa suka shiga *SPUR* sukaci abinci, daganan suka biya *CINEMA* sukayi kallo, _WONDER WOMAN_ akeyi, suna gama kallon suka biya *ROSELLAS* suka siya ticket suka shiga, wasa kam sun sha shi dan har swimming seda sukayi, watsapp, snap chat, Instagram kam sun cika su da story, kowa yasan yau *ZYNAH* anje yawo, dan sub dinta har karewa yayi tayi renewal dinshi.

     *ASHRAF* na kwance a dakinshi, duk wani update da tayi shike fara gani, se yanzu ta kara shiga ranshi sosai,  dan she's pure nd natural, wani hoton yasa shi dariya, wani yarasa me zaiyi, wasuyi yayi commenting akai, wasu kuma yayi liking, in short a ranan *ZYNAH* had a lot of fun, basu suka koma gida ba se 7 na yamma, seda tafara sauke Humaira a gida sannan ta wuce gida itama, a gajiye ta shiga gida Momsie na daki dan in tayi sallan Magrib bata tashi setayi Isha, Islam kawai ce a parlour, *ZYNAH* na shiga Islam tace "i can see u had fun today cuz u've being posting necessary nd unnecessary pics", ko kala *ZYNAH* batace mata ba, dan yanzu abu kadan ke hada su  fada, abunda basayi da amma saboda halin da Islam ta tsiro dashi tasa yanzu ko inuwa daya basa zama tare (imagine ya da kanwa kenan fa, amma zama inuwa daya na neman ya gagare su). Dakinta ta shiga, ta ajiye kayanda ta shigo dasu, sannan ta cire kayan jikinta, bathroom ta shiga, ta cika bathtub da ruwa ta zuba shampoo sannan ta shiga ciki, ta dade zaune a ciki tana tunanin comment dinda *ASHRAF* ya dinga yi, "u ar lookn takeaway, u look gorgeous, u look beautiful, y d puppy face, ur smile is breathtaking", haka ta dinga tunowa tana murmushi ita kadai. Seda ta tabbata gajiyan dake jikinta ya ragu sannan ta fito, sallah tayi, tayi Isha gabadaya da Shafa'i da Wutiri, tana idarwa dakin Momsie ta shiga ta gaisheta "yaushe kika dawo?", "tun dazu, nasan kila kina lazimi shiyasa ban shigo ba", "kinci abinci", "eh naci zani in kwanta ne, dan nagani", "ai dole ki gaji, naga pics dinki ai, irin wannan yawo haka", dariya tayi tareda mikewa daga zaunen da take tace "seda safe", "Allah ya tashe mu lfy". Tana zuwa daki daga wayanta na ringing tasan ba kowa bane illa *ASHRAF* zuwa tayi ta dau wayan, hira sukasha sosai ta dinga bashi lbrn wuraren da sukaje, basu suka ajiye waya ba se karfe daya, wannan ma dan saboda baccin da takeji sosai ne.

*WASHEGARI KARFE BIYAR NA YAMMA*
     Daddy ne yashigo gidan da lawyer dinshi, parlourn Daddy suka zauna sannan Daddy ya dau waya ya kira Momsie yace yanaso su hallara a parlour dinshi harda Uncle Yusuf dasu Islam duka,  cikin mintin da be wuce biyar ba duk suka hallara a parlour, kowa mamaki yake me yakowa wannan zaman musamman da sukaga lawyer John Henry,  Daddy seda  yaga duk sun zauna sun nutsu sannan yafara da basmallah sannan yace "ba komai yasa na taraku a nan ba illa na siya wani fili tun ba yau ba wanda akalla zeyi 10plot, badan komai yasa nasiya wannan filin ba illa saboda *ZYNAH*", gabadayansu dagowa sukayi suna kallonshi, ganin haka yasa yace "ku kwantar da hankalinku, kar kuga nace saboda Mamana nasiya kuyi tunanin ko nayi sonkai ko wani abu,  a'a ba haka bane, dukkan ku shaida ne akan alkawarin da na dauka na cewar duk career dinda yaran nan suka zaba ni mai dafa musu ne harse sun cin ma burinsu", Momcy da Uncle Yusuf suka hada baki wurin cewa "hakane", yacigaba da "toh, wannan fili na siyeshi ne da sunan *ZYNAH* a lokacin da naga points dinda ta samu da sukayi exam wanda wannan ya nunamin she is determined, saboda haka ba siya mata fili me 10plot wanda ze isa a gida makeken hospital da sunanta", gabadayansu sunji dadin abunda Daddy yayi dan *ZYNAH* har hawayen farin ciki seda tayi banda Islam dake hawayen bakin ciki a boye, Daddy ne yaci gaba da "na siya filin da wuri ne, saboda kuma kunsan gina hospital ba karamin aiki bane sannan akwai cin lokaci, saboda haka na siya tun yanzu dan a dinga aiki da kadan kadan har Allah yasa a gama, wannan lawyern yazo ne dan yayi shaidan yau *ZYNAH* zatasa hannu akan takardun filin a matsayin yazama nata halak malak, duk yanda takeso tayi da filin matsalan ta ne, amma inaso kuyi shaida a matsayina na mahaifinta na sauke hakkokinta da Allah ya dora min, yanzu ba abunda nake fata illa yau naga ta kamomin wani tace Daddy ga mijin da nakeso na aura,  dan ni koda ace tana matakin karshe na karatunta tasamu miji aurar da ita zanyi inyaso ta karasa karatun ta a dakinshi".

      *ZYNAH* kukan farin ciki, Islam kukan bakin ciki,Momsie hawayen farin ciki, Uncle Yusuf ma murnan yake, tashi *ZYNAH* tayi ta fada jikin Daddy tana kuka tareda fadin "Daddy na gode, na gode Daddy", "shhhhhh, stop crying, me na kuka daina kuka kinji", share mata hawaye yayi sannan ya karbo files din hannu lawyer ya mika mata, signing tayi a kai sannan ta mikawa Daddy yace "a'a barshi a hannunki yazama naki ai", kallon Momsie tayi sannan ta mikawa Momsie "a'a kinsani da mantuwa, zan iya in manta inda na ajiye saboda haka rike kayanki", juyawa tayi wurin Uncle Yusuf shima yace ta rike kar yaje ya hada da files dinshi na wurin aiki.(hanya ba'ayi ganganci na na barin takardun nan a hannun *ZYNAH*). Lawyer ne yace "Alhaji i will lyk to hav d papers so as to photocopy dem nd bring it back", ba musu aka bashi inyaso in yayi photocopy seya kawo.

_Kuyi hakuri na tsaya ana kaina ke ciwo😰_

     _Mzz Daddy 💋_

ZYNAHWhere stories live. Discover now