Chapter 62

1.4K 62 3
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


              *ZYNAH*



(An Interesting Luv Story 2017)


By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)


*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*


QUOTE:-"Life becomes romantic when someone start looking silently but life becomes more romantic when someone start reading those eyes."

_Second to d last page_



                6⃣2⃣

     Basu suka tashi ba se wuraren bakwai, nan ma hasken rana ne ya tada *ASHRAF* ganin sun makara yasa yayi sauri ya tashe ta, tare sukayi alwallah ya jasu sallah, sukayi adduo'in su sannan ta koma dakin ta, wanka tashiga tayi ta fito ta sa kaya atampa vilisco sky blue me touches din pink a jiki sosai tayi kyau kallan kanta tayi a mirror tayi murmushi tace "Ashe native na min kyau", jin alaman bude kofa ne yasa tayi sauri ta sunne kanta kasa dan ko kadan batason hada ido da *ASHRAF*, da sallaman shi ya shigo ta amsa mai yayi murmushi yaje ya rungumota ta baya ya dora kanshi a kafadanta yana kallonta ta mirror yace " only one kinga yanda kikayi kyau kuwa", murmushi tayi yace "amma sumtin is missing, come wit me", hannunta yaja ya kaita dakinshi gaban mirror ya tsayar da ita sannan ya bude drawer ya dauko wani diamond necklace me shegen kyau da tsada ya sa mata sannan yana kallonta ta cikin mirror yace " perfect", murmushi tayi tace "thank u", yace " don't thank me again from nw on, banaso", kada mishi kai tayi sannan ta koma kan kujera ta zauna ya bita da kallo, ganin yanda take tafiya yasa tausayinta ya kamashi yaje ya zauna kusa da ita tareda riko hannunta yace " *DAMSEL* look at me", kin dagowa tayi yace "plss rashin kallon na da bakya yi yana damuna senaga kaman har yanzu fushi kikeyi dani saboda abunda ya faru jiya", girgiza kai tayi tace " ni banyi fushi ba", yace "if u want me to believe u den look at me at least for once", kasa dago kai tayi yace " plsss only one", ganni yadda yake mata magiya yasa da kyar ta dago ai kuwa suna hada ido ta mayar da kanta kasa tareda shigewa jikinshi shikuma ya rungumota cike da saukin so.



      Shiru sukayi na kusan minti biyar sannan daga baya yace " only one me zakici", bata kai ga yin magana ba sukaji ana danna door bell, "wait for me here am coming", yace mata sannan ya fita, yana bude kofan yaga su Basma tsaye da kuloli a hannu sukayi dariya sukace " Hamma ina kwana", "lfy lau", Islam ce tace " hamma ka tsaya bakin kofa, bari mu shiga mu ajiye wannan coolers nawa da nauyi", tana magana tana kara daga cooler dinta sama alamun nauyi yace "ai base kun shiga ciki ba, ko daga nan ma zaku iya ajiye wa ku kara gaba", kallon juna sukayi saboda sun sallame  driver din da ya kawo su sun ce mishi se yamma ya dawo ya dauke su, Humaira ta daure tace " amaryar bata tashi bane", yace "bata tashi ba shiyasa banaso ku dame ta", shiru sukayi Islam har cin farce tana tunanin me zatace ya bari su shiga ta tsinkayo muryanshi yana cewa " ku miko min cooler akwai abinda nake", Basma tace "bari muzo mu taya ka", wani harara ya watsa mata ba shiri tayi shiru duk suka mika mishi cooler shikuma yana ajiye nan kusa dashi sannan yace " toh ku kaida Adda Hafsa ", yana fadan haka ya garkame kofanshi sukuma duk suka tsaya cirko cirko suna tunanin abunyi, dole taxi suka tare ya kaisu gida suna bakin cikin rashin shiga da basuyi ba, shikuma yana rufe kofan shi yace " haka kurum, ina cin angwanci kuzo ku takura min(ba sabanba😂), ajiye abincin yayi kan dinning sannan ya koma sama inda ya tarar gimbiyar har ta soma barci, yatsanta ya kama yasa a baki yana tsotsa nan da nan ta bude ido yayi murmushi yace "taso kiyi breakfast", kallon shi tayi tace " ba dai girki kayi ba", yace "a'a kawowa akayi", daga ta yayi suna tafiya tace " waye kawo", "Su Basma", cikin jin dadi tace " suna kasa ne", yace "a'a na sallamesu", nan da nan fara'ar ta ya washe yace " menene kuma, tafiyan su ne bakya so, in kira miki su", tace "a'a", yace " toh meyasa kika bata rai ", " saboda naso ganin su", ya kalleta yace "OK bari nakira miki su, tun da ni dodo ne cinye zanyi", da sauri ta karba wayan hannunshi tace " dats nt wat i mean", murmushi yayi suka sauka  ganin tayi hanyar kitchen yace "ina zaki", " plate zan dauko", "a'a dawo ki zauna", zaunar da ita yayi tareda bata peck a lips dinta yace " ina zuwa", murmushi tayi a zuciyar ta tace "so romantic", seda ya bude coolers din yaga romon kaza ne dayan kuma soyayyen potatoes da kwai, se kuma flask cike da ruwan shayi, kitchen yaje ya dauko plate daya boil daya spoon  daya fork daya se cup daya shima da tea spoon daya ya fito ya ajiye sannan ya koma ya dauko kayan shayi ya fito,tea din yafara hadawa sannan ya zuba potatoes a plate, romon kuma a boil ya zauna ya kalle ta yace "bismillah", kallonshi tayi tace " kai bazaki ci", "tare zamuci", tace " OK bari na karo spoon", dawo da ita yayi ya zaunar kan cinyarshi yace "spoon daya zamuyi amfani dashi, oya lets eat", nan ya fara feeding dinta da kanshi yana bata yanaci har tace ta koshi shima yace ya koshi, ta tashi tare suka kai kwanukan kitchen ya bari ta wanke yace a'a za'a wanke, fito wa sukayi yace su zagaya gidan ta gani daga nan abincin yayi digest.



     Sha daya da en mintina su Minal sukazo gidan dan su musu sallama har da su Basma aka dawo, su *ASHRAF* suna garden sukaji alamun ana danna door bell, tashi sukayi rike da hannun juna suka karasa cikin gida inda suka ga su Minal tsaye, da saurinta ta karasa wurin su tace "Adda Minal sanda zuwa", murmushi tayi tace " amarya bakya laifi, koda kin kashe sugaban kasa", dariya tayi tace "da kuwa na karasa ruyuwata a kurkuku", dariya sukayi gaba dayansu *ASHRAF* ya karaso yace " wato seda kuka dawo koh", Islam tace "sallama mukazo muyi muku", da sauri *ZYNAH* tace " ba dai yau zaku tafi ba", sukace "wlh jirgin 6pm zamubi, amma Basma se gobe dan ita Zaria zata", bude musu kofan yayi suka shiga suna ci daga hiransu shikuma daki ya wuce ya dauko laptop dinshi dan yakarasa wani project daya fara. Basu suka bar gidan ba se bayan la'asar kaman karsu rabu, *ZYNAH* duk ta ba kowannen su kayan kwalliya daga cikin kayan lefenta suka karba suna mata godiya sannan driver yazo ya dauke suka bar gidan ita da *ASHRAF* suka koma ciki cike da kewa. Zuwa yanzu ta saki jikinta da *ASHRAF* suna hira sosai, suna komawa tace mishi zataje tayi wanka yace toh sannan ta shiga dakin ta tayi wanka tasa evening gown peach colour ta kaman gashinta ta feshe jikinta da turare sannan ta fito ta shiga dakin mijin ta inda shima yayi wanka yasa wando three quarter baki da white top yana zaune gaban laptop dinshi, kallon ta yayi yace " matso zoki zauna nan", ya nuna gefen shi ta karasa ta zauna ya matso da ita jikinshi sosai sannan yace "look, ina neman mana garin da keda dadin honeymoon amma ni har yanzu banga wanda ya min ba in ba Paris ba", murmushi tayi tace " Mine ai base munje wani gari honey moon ba, anan ma se muyi honeymoon din mu", yace "a'a, zaba garin da kikeso", tace " Allah ba inda zani, ka bari muyi honey moon dinmu a nan", kallonta yayi sosai sannan yace "shikenan if dats wat u want", kashe laptop din yayi ya ajiye gefe sannan ya kwanta tareda janyo ta jinkinshi, yasa hannu yana shafa lips dinta yace " let's start our honeymoon nw", ai tuni jikinta ya fara rawa dan bazata manta da wahalan da tasha jiya ba, kissing dinta ya fara yi nikuma na fita na janyo musu kofa😉.


    
     *BAYAN SATI BIYU*

     *ASHRAF* bashi ya koma bakin aikinshi ba seda yayi sati biyu yana dirzar angwanci son ranshi, yau ya kama Monday kuma yau ze kuma bakin aikinshi, tun shida da rabi *ZYNAH* ta tashi ta wuce dakin ta tayi wanka tayi kwalliya cikin atampa super, fito wa tayi ta shiga kitchen ta hadawa mijin ta lafiyyen breakfast, bata dau lokaci ba tagama ta jera kan dinning sannan ta koma dakinshi taga har yanzu bacci yakeyi, agogo ta kalla taga 7:30 tace "akwai sauran lokaci tunda 9:00 ze shiga office", zuwa tayi ta kwanta a gefen shi tana wasa da hancin shi ya bude ido ya ganta, murmushi yayi ya janyo ta jikinshi tace " gud mrnn", yace "mrnn, kintashi lfy", tace " lfy lau, Mine tashi kayi wanka karka makara", tambayar ta yayi yace "karfe nawa" tace "to 8", yace " bari in kara bacci kadan 8 kitashe ni", ba musu ta kyaleshi ya koma bacci ita kuma se kallonshi takeyi, ganin barci na neman dauke ta ne yasa ta juya ta duba agogo taga 8:10 tace "me nakeyi har lokaci ya wuce haka", a hankali ta tashe shi tace " tashi Mine karka makara kaji", bude musu idonshi yayi sannan ya tashi, yace "muje muyi wankan tare", tace " dan Allah kaje kai kadai banson kayi latti, in ka dawo mayi tare", yace "promise", " yes promise", bathroom ya shiga kafin ya fito ta ciro mishi suit din da zesa ta goge mishi shoe dinshi yana fitowa ta tayashi shiryawa sannan suka sauka kasa ta zuba mai abinci tayi feeding dinshi, tanayi tana kallon lokaci shikuma duk yana lura da ita, har bakin mota ta rakashi tace "adawo lfy", yace " give me a proper gud bye, banson a dawo lfy", kallon shi tayi saboda tagane abunda yake nufi sannan ta daga kafanta ta kara  kanta tsayi ta bashi peck a goshi take "Allah ya kiyaye hanya", ta bashi peck a left chick tace " Allah ya bada sa'a", ta bashi peck a right chick tace "take care of ur self", sannan ta bashi hot kiss a lips tace " be back safe", murmushi yayi ya rungumota yayi kissing dinta yace "I Luv u, take care of ur self will am gone", tace " I will", koda ya shiga mota ya dade yana kallonta ita kuma tana daga mishi sannan yama motan wuta ya fice daga gidan ita kuma ta koma ciki, lattin da ba'aso yayi seda yayishi. Koda yaje office duk bayan 30min seya kirata har ya taso ya dawo gida wanda kafin ya dawo ta gyara ko ina yasa turaren wuta ta mishi girki tayi wanka tasa wando bump shot da karamin top, tama kanta all back biyu, tana jin karan tsayuwan motanshi tasauko da sauri yayi daidai da shigowanshi ajiye jakanshi yayi da gudu ta karasa wurin shi ya daga ta sama ya juyi da ita se dariya takeyi kaman karaman yarinya sannan ya direta ya rungumeta yace "did u miss me", tace " a lot", da haka suka haura sama ta samu yayi wanka sannan suka sauka ta
bashi abinci yaci suka kuma parlour suna kallo. Haka rayuwarsu yaci gaba cikin so da kaunar juna.


*BAYAN WATA DAYA DA SATI BIYU*


_Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now