Chapter 45

992 71 3
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

            *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"One of the worst feelings in the world is when someone you care about starts treating you differently because of just one little mistake you made."

     _I dedicate dis page to *ZYNAH FAN'S CLUB* members, tnx for d comments nd support so far, luv u to moon habibties😍😘_

              4⃣5⃣

     Tana shiga daki ta kulle kofanta ta zauna kasa ta shiga rusa kuka me cin rai, seda tayi kukan sosai sannan ta tashi da kyar tana ganin bibbiyu ta cire kayan jikinta ta shiga bathroom ta dade sosai a bathtub tana gasa jikinta sannan tayi wanka tayi alwallah tayi fita, sallan magrib da isha tayi ta zauna ta ringa karanto addu'oin Allah ya yaye ma Islam kiyayyar da take mata, ta kai karfe goma a wurin sannan ta tashi tayi shafa'i da wutiri sannan ta kwanta, tana kwanciya ta dau wayanta ta bude, missed calls da messages tagani na *ASHRAF* dana Humaira wanda batamasan sanda suka kira ba, messages din ta fara bude wa inda ya turo mata messages na kwantar da hankali kaman haka

_Life isnt about getting and having, its about giving and being. So cheer up babe._ 

_Everyone wants happiness, no one wants pain, but you can't make a rainbow, without a little rain. Forget wat happened nd move on its part of ur test._

  _Life is like a book. Some chapters sad, some happy, and some exciting. But if you never turn the page, you will never know what the next chapter holds. *DAMSEL* try to open d next chapter, remember tomorrow is a new day, no one knws wat tomorrow might hold.  *I Luv u angel* spl tyt. 😘_

Itama Humaira texts na  kwantar da hankali ta turo mata tana gama karantawa ta shiga gallery tana kallon hotunan da suka dauka da Islam, hawaye taji a kuncinta tasa hannu ta goge tana ci gaba da kallon hotunan, batasan sanda ta fara magana a fili ba tana cewa "Islam y u above all, u wer d last person i will believe will do dis to me, i luved u so much bt u neva seem to see dat, all u could think of is to betray me in such a way dats will hurt me so much, Islam  i neva tot u wer dis wicked", nan ta dinga maganganu tana kuka da ta gaji ta kwanta tana sauka numfashi da haka wahalallen barci ya dauke ta.

*WASHEGARI*

     Ba ita ta tashi daga barci ba se wuraren karfe tara, da sauri ta shiga bathroom ta dauro alwallah tazo tayi sallan asuba tazauna tana addu'oin ta, ta kai minti talatin a wurin sannan ta tashi ta shiga bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin top da high waist skirt, parking gashin ta tayi sannan ta koma ta zauna kan gado dan batajin zata iya fita, ciwon kai ne ya sata gaba gashi bataci abinci ba ballantana tasha magani, knocking taji anayi da kyar ta iya tashi ta bude kofan, Humaira ce tsaye itama jikinta duk tayi laushe tace "swthrt  wats wrong wit u, kuka kika dinga yi ne", shiru *ZYNAH* ta mata ta koma kan gado ta zauna, karasowa ciki Humaira tayi ta zauna kusa da ita tareda riko hannunta tace "swthrt u need stop dis act nd move on, kulle kanki a daki da kikayi kina kuka will nt help so plss it's high time u stop, itama Islam tayi regretting each nd every action da tayi, a dakin Basma duk muka kwana, itama kukan ta dinga yi da kyar muka lallashe ta", kallon Humaira *ZYNAH* tayi tace "se nace miki, kuka nayi", "ai ko baki fada ba kowa ya ganki yasan kinyi kuka, kalli idonki yanda ya kumbura kuma yayi ja, kalli yanda kika rame a dare daya, ai kowa ya ganki yasan ba kalau ba", shiru *ZYNAH* tayi dan batasan me zatace ba, ganin shirun yayi yawa ne yasa Humaira tace "Momsie wai kizo, da taga zan shigo nan tace in kiraki", "tana ina?", "tana parlour Ammi", tashi tayi ta dauko mayafi tasa a kanta sannan suka fito,   ba kowa a parlour Ummi saboda haka suka fita zuwa part din Ammi, da sallama suka shiga duka en gidan na parlourn har da Islam,  kowa a wurin seda *ZYNAH* ta basu tausayi saboda yanda ta rame har wani duhu ta dan yi(taga tashin hankali),  gaishe da su tayi suka amsa sannan ta zauna a kasa kusa da kafan Momsie tace "Momsie wai kina kirana", shafa kanta Momsie tayi tace "naga baki fito bane, gashi za'aci abinci, ya naji kanki yayi zafi, kuka kika dingayi ne jiya", "a'a Momsie da ciwon kan na tashi", Ummi tace "Allah ya sawwake , ci abinci kisha magani", daukan abincin Abba da Daddy Minal tayi ta kai musu part din Abba, Basma kuma ta dau nasu *ASHRAF* takai part dinsu, sukuma zama sukayi sukaci nasu wanda daga *ZYNAH* har Islam ba wani cin abincin suke ba, Haidar  ne ya shigo yace "Abba yace in an gama breakfast duk a zo parlour shi kowa da kowa", amsa sukayi da "sunji", sannan sukaci gaba da cin abincin su, suna gamawa Ammi taba *ZYNAH* maganin ciwon kai sannan duk wuce zuwa kiran Abba.

     Gabadayansu zaune a parlour Abba maza da mata, Abba ganin duk sun nutsu yasa yayi gyaran murya sannan ya fara " auzubillahi minal shaidanil rajim, bismillahi rahmanil rahim, wassalatu wassalam ala man aflahal lisani nabiyi na Muhammadu rasulillahi (S A W),  wa ba'ad assalamu alaikum wa rahamatulahi ta'ala wa  barakatuhu", duk suka amsa mishi da "Ameen wa'alaikumul sallamu wa rahamatul lahi ta'ala wa barakatuhu", sannan yaci gaba da "ba komai yasa na taraku a nan ba illa magana ne da bata wuce biyu zuwa uku ba, amma dan uwana nan shi zefara muku nashi jawabin sannan in kara da nawa, Alhaji Muhammad bismillah", gyara zama Daddy yayi sannan yace "toh da farko dai zan fara da maganan filin da Islam ta dauka ta siyar, Islam"  ya kirata tareda kura mata ido tace "na'am Daddy", yace "abunda kikayi kwata kwata be dace ba, kin cuce er uwarki wacce kuka fito ciki daya da ita, amma da nayi tunani senaga ba laifin ki bane, laifina ne dakuna yarinta dake damun ki, da'ace bana nuna banbanci tsakaninku da kiyayyar da kike wa er uwar be kai wannan stage din ba, amma yanzu ba wani dogon bayani da zan miki illa ga er uwar ki nan, ki bata hakuri kuma ki nemi gafaranta yanzu", kallon *ZYNAH* Islam tayi tana hawaye tace "sister dan Allah da manzonsa ki yafemin, wlh bayin kaina bane, sharrin shaidan ne, kuma am nw a saint, i've repent", cikin sanyin murya *ZYNAH* tace "na yafe miki, Allah ya yafe mana gaba daya", duk suka amsa da "ameen". Sannan Daddy yaci gaba da cewa "toh ke kuma Mamana ki kwantar da hankalinki saboda fili dai har yanzu naki ne", dagowa tayi ta kalleshi ya kada mata kai yace "fake documents muka baki, saboda haka fake documents din Islam ta dauka, so in munkoma i will get ur land back for u", wani dadi taji wanda ta kasa boyewa har seda tayi hawayen farin ciki tace "thank u Daddy", yace "don't thank me cuz u deserve it, so ni a nan na kawo karshen nawa zancen, dan filo saura ya rage naka", murmushi Abba yayi sannan ya fara da.

     "dama ba wani abu bane illa a matsayina na mahaifin Fahad na samu mai mata kuma nitsatsiya, me hankali, wacce duk kun santa saboda ta gida ce, kuma mahaifinta ya ba Fahad ita halak malak, iyayen basuyi mamaki ba saboda sunsan da zancen amma yaran kowa jira yake yaji wa aka zabama Fahad, banda Fahad da se faman murmushi yakeyi, Abba ne yaci gaba da cewa "dani da Alhaji Muhammad mun yanke shawaran hada yayanmu a inuwar aure", dammm zuciyar *ASHRAF* dana *ZYNAH* ya buga dan sunsan ko ba'a fada ba *ZYNAH* ce tunda itace takai aure, Islam wazeyi tunanin yi mata aure a yanzu, Abba ne ya katse musu zancen zucin da sukeyi yace "saboda haka inaso dukkan ku nan ku shaida yau Alh Muhammad yaba Fahad er  sa *ZYNAH* a matsayin matarshi nan gaba", a tare *ASHRAF* da *ZYNAH* suka hada baki wurin cewa "Abba mata", kowa a parlour kallonsu yake Abba yace "eh mata wacce ze aura ba, da magana ne", girgiza kai *ASHRAF* yayi yace "babu", kallonshi *ZYNAH* tayi tana mamakin yanda za'ayi yace babu magana bayan akwai, taso su hada ido amma inaa yaki ya dago kai Daddy ne ya kalleta yace "Mamana da fatan zaki mun biyayya kaman yanda kika saba", "Daddy akwai..... ", bata karasa fadan abunda takeso tace ba *ASHRAF* yayi sauri ya dago yana mata alama da kartace komai, shiru tayi Daddy yace "ina jinki", tace "In Sha Allahu Daddy zan zamo mai yima biyayya bazan taba sabawa umarninka ba, nasan bazaka zabamin abunda ze cutar dani ba", murmushi Daddy yayi yace "nagode Mamana Allah ya miki albarka", *ASHRAF* ji yake kaman ana tsara mishi kai saboda wani matsanancin ciwon kan da ya taso mishi lokaci daya, shikuma Fahad dadi yakeji kaman wanda akama albishir da kujeran makka, bakin yaki rufawa kaman gonan audiga, Humaira kuwa dadi taji a ganin ta yanzu ne lokacin da yakamata ta mallaki *ASHRAF*, *ZYNAH* kam ba'ama magananta dan gabadaya kwanyan kanta ya kwance, Abba ne yace "toh Fahad seka rike amana, inka zalunceta Allah na kallonka kuma ze saka mata, Allah ya muku albarka gabaki dayanku", da haka aka rufe taro kowa ya watse.

     _Hmmm readers kunji wata sabuwa, comment plsssss, ur comments keep boosting my moral, much luv😘_

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now