Chapter 36

1.1K 62 2
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Some people are so lucky that even after hurting they get so much love and some are so unlucky that even after giving so much love they always get hurt."

                3⃣6⃣

     Su na fita daga dakin ba dadewa Humaira ta tashi daga barci, zama tayi kan gado tana tunanin *ASHRAF* dan koda ta kwanta seda tayi mafarkin shi, hango wayan *ZYNAH* tayi akan desk dinda take karatu,mikewa tayi taje ta dau wayan ta bude tashiga gallery tana kallon hotunan *ASHRAF* dukda ba wani wayane dasu ba, bude wayanta tayi ta tura hotunan sannan ta dauki numbern *ASHRAF* dayake tasan sunan da *ZYNAH* tayi saving dashi, seda ta gama copying din number din sannan wani zuciyar yake ceme ta "abun nan da takeyi hanya ya dace, wacce bstfrnd dinta keso shi itama ta fada tarkon sonshi", se wani zuciyan kuma yace "toh ai bani nasawa kaina sonshi ba, Allah ne ya doramin sonshi kuma ba yanda na iya dole one way or d other in samu hanyar da nabi na mallake shi".  Haka tayita sake sake a zuciyar ta har taji karan murda kofa wanda ya tabbatar mata da *ZYNAH* ce, a jiye wayan tayi a daidai lokacin da *ZYNAH* ke shigowa, tace "bestee na barki kadai koh", Humaira ta kalleta tace "a'a ai banma dade da tashi ba, daga ina", "wlh nida *ASHRAF* muketa hira tun dazo, yaki barina na shigo gida, seda nace mishi sallah zanje nayi",  Humaira a zuciyarta tace "kedai kenan", amma a fili cewa tayi "wai ni in tambaye ki, wannan relationship din tsakanin keda *ASHRAF* na wa da kanwa ne koh na budurwa da saurayi", murmushi *ZYNAH* tayi tareda zama sannan tace "za'a iya cewa duka, meyasa kika tambaya?", "saboda narasa gane takan ku, shi yaki yafito fili ya gayamaki yana sonki, se wasa da hankalinki yake kikuma kinata biye mishi gashi kema har kin fada tarkon sonshi", dariya *ZYNAH* tayi ta mike tana kokarin cire kayanta jikinta tace "maybe he's waiting for d ryt tym saboda he doesn't want to rush tins, bt as for me i will wait for him no matter hw long it will take", "himmmm ke a ina kika tabajin an jira na namiji, ba namiji bane yake jiran mace ba", itadai *ZYNAH* gudun dogon zance yasa tace "kinga an kira sallah magrib bari muyi sallah se muci gaba da hiran", sannan ta fada bathroom dan tayi wanka.

     Da daddare bayan isha duk suka hallara a dinning gaba dayansu harda Abba da Uncle Yusuf dayake shima anje an kirashi, sun fara ci sukaji sallaman *ASHRAF* wanda rabonshi da yazo ya zauna aci abinci gabadaya harsun manta, zuwa yayi yaja kujeran kusada Uncle ya zauna ya dauki plate ze zuba abinci, Abba ne ya kalleshi yace "yau kuma meka tuna kazo nan?", murmushi kawai yayi sannan yace "kawai dai yau ina sha'awan zama naci abinci anan ne", kada kai kawai Abba yayi yaci gaba da cin abincin shi, Ammi tace "zaka fada gaskiya ne, miskilan yaro kawai", dayake yaje ya bata lbrn *ZYNAH* kuma ya fada mata ita yakeso amma be fadawa *ZYNAH* ba tukun se nan gaba, Minal ma kallonshi tayi dan tasan dalilinshi na zuwa cin abincin yau, Gimbiya kuma duk sanda tayi nasarar dago kai, toh se sun hada ido da shi. *ZYNAH* ta riga kowa tashi da sunan ta koshi, wanda tana tashi ya ajiye spoon shima wai ya koshi, gabadaya wurin kallonshi akeyi saboda ko spoon biyar be ciba, ganin yanda ake kallonshi yasa yagane ya tafka shirme, se yayi sauri ya wayance yace "abincin yayi yaji shiyasa, bazan iya cin dayawa ba", ba karya abincin da yaji amma tun farko besan da yaji ba seda sarauniya tace ta koshi. Ganin tayi hanyar daki yasa shima yayi waje, dakin shi ya shiga, yana shiga ya dauko wayanshi ya kirata, murmushi tayi tace "wannan anyi jarabbabe, sekace ba dazunnan muka rabuba", dauka tayi tace "hello", yace "meyasa bakici abincinki sosai ba, ni na takura miki koh?", "a'a wlh baka takuramin ba, kawai dai na koshi ne", yace "Ok, zanje wurin Sameer yanzu ina dawo zan kiraki karkiyi bacci", "toh ba zanyi ba", sallama sukayi suka kashe wayan. Bashi ya dawo ba se karfe goma, koda ya kirata tayi nisa a barci saboda haka bata dauka ba, Humaira kuma tana ganin call din amma takasa dauka tace mishi tayi barci.

ZYNAHWhere stories live. Discover now