Chapter 28

979 67 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An interesting luv story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"A successful man is one who makes more money than his wife can spend. A successful woman is one who can find such a man."

     _I dedicate dis page to *Meela Adeel, Aisha M Muazzam, Raheenat, Fatima Munnira, Xiexie nd Feedo*, tnx guys for all ur support, ur encouragement keeps me moving, u guys ar swthrts to me. Much luv Habibties😘._

                2⃣8⃣

     *WASHEGARI*
     Karfe goma dai dai Uncle Yusuf ya dira a garin zazzau, direct hospital din ya wuce dan dama ba wani kaya ya dauko ba. Yana zuwa aka nuna mishi dakin da take ya shiga ya ganta zaune tayi zurfi cikin tunani bata masan wani ya shigo ba. Jin kamshin turare yasa tadawo cikin hayyacinta tareda dago kai dan ganin waye tsaye a kanta. Uncle Yusuf tagani tsaye yana mata murmushi, batasan sanda ta fada jikinshi ba dan tsananin murya har seda yace mata " *BEAUTY* yi a hankali drip ne a hannunki", dagashi tayi tareda gyara zama shima yaja kujera ya zauna tareda kura mata ido tace "Uncle wannan kallon fa?" yace " *BEAUTY* kin rame, kuma da alamun damuwa a tattare dake" tace "Uncle ai rama ya zama dole saboda karatun medicine ba easy bane" yace ,"hakane, amma me ke damunki?" ta sauke ajiyar zuciya sannan tace "Uncle abu dayawa na damuna, amma before dat yasu Daddy?" ,"suna lfy, sun mace in gaida ke" ta zaro ido tareda cewa "sunsan ina hospital ne? " murmushi yayi tareda lakace mata hanci kafin yace "silly girl, basu sani ba, ce musu nayi akwai abunda zanzo inyi a Kaduna sannan nace zan biyo in gaishe ki, shine sukace suma suna gaida ke, kinga har dambu Momcy ta bani in baki" ,"oh i tot sun sani ne".

     "So tell me, wat d hell is bordering u da kika kasa boyewa har fuskanki ke nuna kina cikin damuwa?" ta kalleshi tace "alot Uncle, amma ina tsoron fadama" ,"saboda me bazaki fada min ba?" ,"saboda zaka iya kaje ka gayawa su Momcy, nd i don't want dat" ,"why?afterall dey ar ur parents, dey ar in d bst position to knw of ur problem" ,"yes Uncle i knw, amma dis case is different, dey can suspend me frm schooling here", kallonta yakeyi dan besan inda ta dosa ba, seda ya kare mata kallo saf sannan yace "don't tell u've done sumtin stupid" kallonshi tayi sosai dan bata tsamanin wannan kalman ze fito daga bakinshi sannan daga bisani tace "Uncle ba haka bane, zan fada ma duk halin da nake ciki, amma u will hav to promise me we will solve it together, no third party nd Daddy nd Momcy must nt here abt dis" seda yayi tunani kadan sannan yace "Ok, i accept ur conditions" tace "promise" yace "i cross my heart", sannan ta gyara zama tafara bashi lbr.

     Tun sanda ta hadu da KB a library, da binta da yayi har kaisu ga fada shida *ASHRAF*, da zuwan da KB yayi asibiti da maganganun da yamata duk seda da ta fadawa Uncle ba abunda ta bari. Seda ya numfasa sannan yace "yanzu kinaso ki cemin dis guy is after u da sunan sonki yakeyi, whereas bincike ya nuna ba gud guy bane?" ta kalli Uncle da kyau tace "Uncle believe me he is d baddest of all, babu halin banzan da be iya" ,"ke ya akayi kikasan ba mutumin kirki bane?" ta kalleshi tace "Uncle believe me he's a star a school din, cus he has money, dats y everybody luvs him, nd moreover Ashanty ta fada min komai a kanshi kuma nima naga alama" nade hannuwanshi yayi a kirji tareda da gyara zama sosai yace "in dat case, me zamuyi yanzu, u can't live d hostel cus u hav no where to go, nd u ar determined on ur studies, so ni a ganina u just hav to b patient nd endure for nw kafin musan abunda zamuyi" ,"ok shikenan Uncle, i will do as u say" yayi murmushi tareda shafa mata kai yace "dats my gurl" itama murmushin tayi sannan ta dauko wayanta tana dannawa.

     Tun da safe wuraren 8:00am su Ummi sukazo asibitin tareda kawo mishi duk wani abunda ze bukata. Hamma Fahad nacan yau weekend shiyasa yana planning zuwa gida amma baze fada musu ba acewar shi surprising dinsu zeyi. *ASHRAF* bashi ya tashi ba se around 9:30, Abba, Ummi, da Ammi ne a dakin dan su Minal basuzo ba tukun saboda ance su shirya su Husna da Juwairiya a kaisu Islamiyya dan ba'a son suga halin da yayansu ke ciki harse ya danji sauki. Kallon su yayi yace "Abba har kunzo?" juyowa sukayi gabadayan su suna kallonshi, Abba yace "munzo, ya jikin" ,"da sauki", nan su Ummi suka shiga mishi ya jiki ya amsa su da da sauki, sannan ya kalli Ammi yace "Ammi yunwa nakeji" da saurin ta dau plate ta zuba mishi abinci, fried potatoes ne da kwai sannan ta hada mishi tea me kauri ta ajiye gefe, toilet ta shiga ta dauko wani bowl tazo ta bashi brush ya wanke baki sannan ta dauko abincin ta bashi, be iya yaci sosai ba saboda bakinshi ba appetite, dole ya hakura da abincin dukda yunwan da yakeji. Doctor ne ya shigo dakin da sallamanshi tareda gaishe dasu Abba sannan ya karasa wurin *ASHRAF* yace "Sannu, ya jikin?" yace "da sauki" ,"bakajin pains koh kanaji?" ,"banaji sedai bakina ne da ba dadi" ,"dama wannan dole ne, sannu, bari na kira nurse tazo ta samaka last drip" ,"doctor drip kuma?, daga jiya zuwa yau nasha drip ya kai biyar" murmushi doctor din yayi yace "toh ai saboda lfyn ka ne" ,"toh doctor ba'a hutawa?, ku bari na huta anjima se a samin" ,"shikenan if dat is wat u want", har doctor din ya juya *ASHRAF* ya riko hannushi tareda cewa "i need ur help, inaso inje inyi tahara" hannu doctor din ya mika mishi tareda taimaka mishi ya mike amma wani kara *ASHRAF* ya sake tareda komawa ya kwanta rike da gefen cikinshi se faman gurnani yake yana juyi kan gadon.

     Doctor ne ya kalleshi tareda da cewa "lfy", Abba ya harzuka yace "ya zaka tambayeshi lfy, bacin kana ganin halin da yake ciki, koh ba kai kace kun maida kashin da ya goce mazaunin shi ba, toh yanzu me ya faru kuma" doctor ya kalli Abba yace "Alhaji calm down, sumtin is wrong sum where, bari zansa a mishi scan, In Sha Allahu zamu gano koma menene", nurse ya kira tareda fada mata alluran da zata hado, taje ta hado da saurinta tareda mai alluran, koh minti biyu ba'ayi ba da mai alluran  ya koma barci, su Ummi kam in hankalinsu yayi dubu toh ya tashi, ba abunda sukeyi banda hawaye da sallati.  Nurses ne suka shigo dakin da gadon daukan marasa lfy suka dora *ASHRAF* a kai suka fita dashi zuwa lab su Abba sukabi bayansu suka tsaya a kofar lab din. Hamma Fahad ne ya karaso gidan da murnan shi yau zega family dinshi, yana shiga suka gaisa da mai gadi sannan ya karasa cikin gidan, parlourn Abba yafara shiga tunda yasan yau weekend kila dukkansu suna parlourn amma se yaga akasin haka dan har dakin Abba ya leka amma shiru ba kowa, part din Ammi ya koma nan ma duk abu dayane yace "toh ina suka shiga ko lfy, kai jikina na bani ba lfy ba" da haka ya karasa part din Ummi amma nan ma shiru, dakin Minal ya kwankwasa tareda budewa, Basma yagani da hijab tana kokarin rataya jaka ita kuma Minal tana sa takalmi. Dariya yayi ganin Basma da hijab yace "lil sis hala an saukar miki da wahayi ne naganki da hajib" dan kuwa kowa yasan yadda Basma ta tsani ya hijab, ta gwammace tasa mayafi, ganin fuskansu duk yayi fayau yasa shima yayi shiru tareda tambayansu "yanaga gidan shiru bacin yau weekend, duk ina sukaje, kuma ina zaku?", cikin sanyin murya Basma tace "Hamma *ASHRAF* na asibiti bashida lfy" ,"wat, meyasa meshi" Minal tace "muma ganinshi mukayi......." nan ta bashi lbr, yace "kuzo muje asibitin" sukabi bayanshi.

     Ashanty da Shaheeda ne suka shigo asibitin dan duba *ZYNAH*, ganin Uncle Yusuf a dakin yasa Ashanty tayi freeze a bakin kofa, seda yace mata "a'a Ashanty manyan mata kwana dayawa" sannan ta dawo hankalinta, ta mishi murmushi tareda karasawa ta gaishe shi ya amsa Shaheeda ma ta gaishe shi ya amsa sannan suka zazzauna ya tambayesu ya karatu suka amsa da alhmdllh, nan suma sukama *ZYNAH* ya jiki ta amsa musu da sauki sannan se kuma dakin ya dau shiru kowa da abunda ke mind dinshi. Da *ZYNAH* ta gaji da shirun se tace "duk kunyi shiru lfy" Uncle Yusuf ya Kallota sannan ya kalli Ashanty   yace "Ashanty ta bamu lbr" tace "na'am" yace "nace ki bamu lbr, dakin yayi shiru" shiru tayi dan batasan me zatace ba gashi kallon da yake mata yanada influence dayawa a kanta, a zuciyarta tace "dama zaka dan fita daga dakin da ya fiye min", ganin tayi shiru yasa yagane cewar bazata iya sakewa in yana nan ba saboda haka ya tashi yace "bari indan zagaya waje, ina zuwa, kuna bukatan wani abu?", duk sukace a'a banda *ZYNAH* da tace ya siyo mata _BOUNTY_ ya kalleta tareda ja mata hanci yace "ke ÿar nan ba kya jin magana, me doctor yace miki?" tace "toh ai naji sauki, ni yamazo yayi discharge dina" ya kalleta ya girgiza kai yace "Allah ya miki sauki" sannan ya juya ya fita.

     A compound din hospital din su Minal suka hadu da Sameer wanda tun safe yaje gida dan shima ya dan huta, sun gaisa sannan duk suka jero zuwa cikin asibitin wanda yayi daidai da Uncle Yusuf ze fito, idanunshi ne sukamai harba da Minal wacce dukda ba makeup a fuskarta amma tayi kyau dan dama chan kyakyawa ce, zuciyar shi ne yafara harbawa da sauri da sauri wanda tunda yake be taba shiga wannan yanayin ba akan mace, har sunyi nisa amma se Fahad ya juyo jin kaman ana binsu da kallo, ganin Uncle Yusuf yasa ya nufa wurin shi tareda cewa "hey,  get ur eyes off my sisters okay", kallonshi Uncle Yusuf yayi sannan yace "sorry", tareda fita, shikuma Fahad ya karasa ciki, dakin da *ASHRAF* yake suka shiga amma basu ganshi ba kuma ba kowa ciki, fitowa sukayi suna dube dube Ammi ta hangosu taje ta samesu, suka gaishe ta amsa tareda fada musu halin da ake ciki, sosai suka shiga damuwa amma tace su kwantar da hankalinsu komai zeyi normal In Sha Allah. Zama sukayi a reception suna jiran sakamako, seda sukayi kusan 15 minutes sannan aka fito dashi aka kaishi daki duk suka taso suma suka shiga, Fahad sosai hankalinshi ya tashi saboda ganin halin da dan uwanshi ke ciki, zuwa yayi ya tsaya a gaban gadon yana kallonshi. Doctor ne ya shigo dan fada musu sakamakon test dinda aka mishi, zuwa yayi kusa da Abba tareda mika mai wani brown envelope, karba Abba yayi ya bude dan dubawa. Hoton scan dinda aka mishi ne, doctor ya fara da cewar "wannan hoton scan dinda muka mishi ne, wanda sakamako ya nuna cewar kashin nan dai shine yasamu matsala dukda an maida shi mazaunin shi amma baze iya tsayawa sosai ba saboda har yanzu ciwon sabo ne, amma yanzu abunda zamuyi shine zamu dora shi akan medication wanda In Sha Allahu muna ganin za'a samu dacewa, amma kuma for nw dole mu bashi walking stick wanda ze dinga assisting dinshi wurin tafiya", duka matan dake dakin kuka sukeyi hatta Fahad seda ya zubda kwalla, Abba ne yayi karfin halin cewa shikenan doctor "zamuyi duk yanda kace tunda lfy ake nema", nan doctor ya musu sallama ya fita tareda fada musu cewar su ragu daga dakin saboda yasamu hutu sosai. Dole Abba yasa Fahad ya kaisu Ummi gida tareda su Minal yace su bari se yamma su dawo, ba yanda suka iya dole suka wuce cike da jimamin halin da *ASHRAF* ke ciki.

    
     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now