Chapter 15

1.2K 69 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

     *Ina mai bada hakuri na rashin jina da bakuyi ba kwana biyu, amma yanzu naji sauki saboda haka zaku dinga jina akai akai.*

QUOTE:- "There's no substitute for a great love who says, 'No matter what's wrong with you, you're welcome at this table.'"

     _I dedicate dis page to all d Members  of *ZYNAH FAN'S CLUB* i luv u all 😍_

                1⃣5⃣

*WASHEGARI*
       Tunda *ZYNAH* ta tashi daga barci tayi wanka da alwallah  tayi walha sannan ta hada kayanta  wuri  daya, seda ta tabbata bata manta da komai ba sannan tasa  kayanta gown ne da veil red nd black. Tana gama shirinta ta duba wayanta taga goma saura, fita tayi ta duba dakin Uncle  Yusuf ko ya shirya taga shima ya gama shiryawa tace " Uncle na gama, zamu iya  tafiya" ,"a'a *BEAUTY* bari muci abinci" ,"Ni bana jin yunwa" ,"Toh ni ina jin yunwa, yaya kenan" ta zauna a kujeran dakin tace "shikenan se muci abincin" yayi murmushi sannan ya musu order din abinci aka kawo musu burger ne da coffee, nan suka zauna suka ba cikinsu hakkin shi, sun gama komai da komai suka fito da kayansu sukayi settling sauran bills dinsu sannan suka fito suka  samu  taxi  ya kaisu tasha. Suna zuwa tashan sukaci  sa'a sauran passenger biyu motan Kano ya cika, nan suka shiga driver yazo suka daga se Kano na dabo tumbin giwa ko dame kazo an fika (ina kanawa ga kirarin ku nan😜).

**********
     *ASHRAF* da Minal ne zaune a garden din gidansu ga sketch board dinshi a gabanshi da pencils da colour paints  ya daidaita kanshi tareda maida hankalinshi kan drawing dinda yakeyi, Minal kuma ta zauna tana kallon abinda yakeyi at d same time kuma tana chatting  a wayanta. Sun dauki kusan awa daya a haka kafin ya gama . Sannan ya juyo wurin Minal yana  mata murmushi yace "Minal look here" nan ta maida hankalinta kan abunda yake nuna mata. Gurl dinda yasaba draw yau ma itace amma wannan karon ba ita kadai bace, ya zanata ne tana zaune a garden da dora kanta a kafadan wani shikuma yasa head phone a kanshi da alamun waka yakeji nd as always yauma bayanta kawai yagani bega fuskanta ba. Seda Minal tagama nazarin drawing din sosai dan view din ya mata kyau sannan tace " Hamma na wat a gud nd perfect drawing ,gaskiya yayi kyau, i luv it" murmushi yayi amma be tanka mata ba har seda yaje wurin tap dinda ke garden din ya wanke hannun shi sannan ya dawo ya zauna kusa da ita yana kallon ta sannan ya kirata kaman wanda yake rada yace "Minal" tace "na'am  Hamma na" ya kalleta yana murmushi, shidai Allah ya dora mishi son wannan kanwa tashi, kodan sunfi kama ne oho...yace mata "kinsanta" ya tambaya a yayinda ya maida kallon shi kan sketch board din. Ciki da mamaki take kallon shi dan batasan inda ya dosaba tace "banga fuskanta bare in santa" ,"hakane, nima ban santa ba, amma i'm eager to know her" kallon shi tayi tace "baka santa den hw comes tayi stick in to ur memory har kayi drawing dinta" numfashi ya sauke sannan yace " she is my *Dream Girl* she has being showing up in my dreams for d past three days now but she refused to show her face to me" cike da tausayi ta kalli shi tace "nd u've start to feel sumtin for her i guess" a raunane ya kalleta yace "I guess so too, dats y i call u her saboda inaso kibani shawara u ar d only one i can confined in dan Sameer mashirmaci ne dana fada mishima dariya ya dingayi yana cemin wai kila aljanah ce dats y i  decide to call u" numfashi taja sannan tace " baka taba haduwa da yarinyar da kaga ta maka ba ko kaga kana sonta"," well, na taba haduwa da wata beautiful young gurl last Sunday a airport da naje dauko Abba", kallonshi tayi tace "and" yace "and to tell u d truth i like d gurl nt luv bt lyk" dariya tayi da jin furucinshi ta girgiza kai sannan tace "wat if she's ur *Dream Girl*" ," at first i think so but daga baya senayi tunanin dai aljanah ce kaman yanda Sameer ya fada" dariya tayi tace "lets not hope so for now,  amma i  believe wata rana she will definitely show her face, zata bayyana hummm","ok, lets hope so" da haka suka gama zancen su suka dauko wani zancen.

**********
     Mutanen Kano sun isa Kano lfy, suna sauka a inda akace su sauka suka tarar da driver din Granny yana jiransu. Ya kaisu gida wanda yake cikin Na'ibawa yar akwa gidan kasa ne me kyau, tun kafin driver ya gama daidaita parking dinshi *ZYNAH* ta fito a guje tana kwala wa Granny kira "Granny Granny Granny" ,"kishiyar tawa har ta karaso" dariya tayi ta rungume Granny tace "Oh my lovely Granny i missed u so much" ,"Toh baturiya ni dagani kafin ki karairaya ni ina fama da jiki" tashi tayi daga jikinta tana dariya wanda yayi daidai da sallaman Uncle a parlourn. Granny da fara'arta ta amsa mai sallamanshi ya duka har kasa yana kwasan gaisuwa tana amsa mishi tareda tambayanshi ya aiki da suransu duk ya amsa da lfy lau. Sun gama gaishe gaishe tace "Dan nan kuma kan kujera ka zauna" ya kuma kan one sitter dinda ke parlourn ya zaune me aikinta ta kawo musu lemon kwali da ruwa da kayan motsa baki suka fara sawa cikinsu kafin abinci ya kammalu. Suna zaune suna wasa da hira cikin barkwanci Idi driver tareda me aikinta suka shigo musu da kayansu aka kai na Uncle guest room ita kuma *ZYNAH* tace dakin Granny zata kwana saboda haka nan aka kai mata jakanta. Seda sukayi sallahn azahar sannan sukaci abinci sukayi wanka Uncle yace shi barci zeyi  itako wurin Granny ta koma ta zauna suna hira.

*WASHEGARI*
     *ZYNAH* bata tashi da wuri ba saboda ta samu lafiyayyen gado kuma she feels at home ba kaman hotel da take jin ta duk a takure ba. Tana tashi tayi wanka da sauransu, wani arabian gown tasa yellow me black stones tasa veil ma black ta dauko takalmi da jaka duka black ta ajiye can bed sannan ta fita parlour, Granny ta gani zaune da yar aikinta suna hira taje ta zauna kusa da Granny tareda dora kanta a kafadan ta tace "Granny ina kwana" ,"Karfe nawa yanzu kike ina kwana ko dayeke yanzu kika tashi, kin tashi lfy" ,"lfy lau" ,"munyi waya da babanki dazu kina barci" ,"nasan ze sake kira". Me aikin ta shirya mata abinci kan dining tace "nagode" ta tashi zata tafi taci abinci Granny tace " wannan kwalliyan fa nazuwa inane" ,"inaso in zagaya garin kano yau, wai ina Uncle ne, banji motsin shi ba" ," Shima kawun naki ya fita, shida wani abokin shi, wai a garin nan abokin yake" ,"ni dai Idi ne ze fita dani" ,"toh  gama cin abincin,bari a mishi magana". Tana gama cin abinci taje tasa jakanta da takalmin ta tama Granny sallama tafito Idi ya fita da ita.

     _Kuyi hakuri da wannan banjin dadi ne amma zanyi cover up din  wasu abubuwan  a next page._

       _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHМесто, где живут истории. Откройте их для себя