Chapter 38

931 69 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

             *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"You will never reach your destination if you stop and throw stones at every dog that barks. Better keep biscuits and move on."

               3⃣8⃣

*BAYAN KWANA UKU*
     Cikin kwana uku nan kullum se Humaira ta raka *ZYNAH* school amma tun ranan da sukaga KB har yau basu kara sashi a ido ba, Humaira  kuma se jiran kiranshi takeyi amma har yau be kira, gashi intaje school da zarin *ZYNAH* ta shiga hall itakuma zata fara neman shi dan yanzu son *ASHRAF* ya gama kamata duk da taso ta hakura amma se taga bazata iya ba, itakuwa *ZYNAH* dadi takeji ta rabu da alakakai alhalin abunda basu sani ba shine mahaifiyar shi ce batada lfy cancer of d lung ya kamata sun fita da ita kasar waje, shiyasa ma be kira Humaira ba saboda number ta na cikin SIM dinshi na Naijeria amma har yau har gobe hankalinshi na kansu, Allah Allah yake sati biyu ya cika ayi discharge dinsu su koma gida. Yau yakama Friday Humaira tace bazata raka *ZYNAH* school ba zata huta ne a gida, sun wuce school gidan yayi tsit ba kowa se su Ummi dake daki suna barci, waya Humaira ta dauko ta boye number ta ta kira *ASHRAF*, yana zaune a library yasa project a gaba yanayi, dan yanzu kanshi yayi zafi saboda yana last stage na karatun shi saboda haka der exam is approaching, wayan shi ne yafara ringing ya duba yaga private number, ajiye wa yayi be dauka ba seda aka kira ya kai sau biyar sannan ya sauka, "hello", shine abunda ya fito daga bakinshi amma se akayi shiru, nan ya dinga maimaita "hello", ganin meshi beda niyyar magana yasa ya kashe wayan yaci gaba da abunda akeyi. Ya ajiye wayan ko minti biyar ba'ayi ba message ya shigo wayanshi kaman haka _I am a lover, Not a fighter. But i can fight for what i love by a secret admirer._ ,ajiye wayan yayi yanata tunani waye ze turo mishi wannan text din, *ZYNAH* abunda ya fado mishi a rai kenan, se kawai yayi murmushi yaci gaba da abunda yakeyi.

*LAGOS*
     Islam na can, zukancin se abunda ya karu, yanzu ba Daddy ba, Momsie da kanta ta hanata zama parlour da sunnan kallo, sannan ta karba laptop din, seda ta tabbata tayi formating duka videos dake cikin laptop din sannan ta maida mata, kuka kam Islam tayi shi harda zazzabi saboda wasu videos din na snapchat ne tayi saving dinsu a wurin, wannan abun yasa bata shiga harkan kowa a gidan, da ta tashi da safe zata wuce  school tana dawowa taza wuce Islamiyya, in ta dawo daga Islamiyya kuma tana daki zaune, abun duniya ya isheta, in kunga ta fito parlour toh abinci ko ruwa ne ya fito da ita, Kamal kadai ne take samun sauki a wurin shi, dan in yaganta cikin wani hali se ya tambayeta abunda ya faru sannan ya lallashe ta. Yau dai Islam ta dau alwashin nemo documents din filin saboda tayi abunda zatayi once nd for all ta huta, dan shi kadai ne zata iya huce takaicinta akai.  Dakin *ZYNAH* ta shiga ba tareda wani yaga shiganta ba, tsayawa tayi tana tunanin ta ina zata fara, wurin dressing mirror ta nufa tafara dude drawers din tana bincike, amma harta gama bataga komai ba, wurin gado ta kuma taci gaba da bincikenta harda daga kafita amma wayam ba komai, maryar da katifan tayi ta gyara wurin ta zauna tana mayarda numfashi, idonta ne ya sauka kan wardrobe din *ZYNAH* tayi murmushi tace "since d documents is nowhere to b found inside ur drawers den definitely it most b in ur wardrobes", tashi tayi ta nufi wurin wardrobe din amma kafin ta kai ga budewa taji Momsie na kwala mata kira, barin wurin tayi da sauri ta fito ta sauka kasa tana cewa "Momsie gani", "ina kike inata kiranki tun dazu", "ina toilet ne", "jekisa hijabi kizo ki rakani supermarket", ba musu ta wuce duk da ranta beso ba amma taci alwashin yau da daddare zata je ta dauko abunda take nema.

*ZARIA*
     *ASHRAF* da *ZYNAH* ne a mota zasu gida yake cemata "naga text dinda kika turo min dazu, shine harda boye number", mamaki ne ya kamata tace "ni ba wanda ya turawa text", kallonta yayi yace "yanzu kinaso kice min bake kika turo text din nan ba", "bani bace", shiru yayi yana tunanin toh in ba ita bace waye?, da haka motan ya dauki shiru se slow music dake tashi kadan kadan har suka karasa gida. Zuwansu gida suka tarar da Fahad ya dawo weekend dayake sati uku kenan be samu zuwa ba shiyasa wannan lokacin tun Friday yazo, sosai *ASHRAF* yaji dadin ganinshi, rungume juna sukayi suna murnar ganin juna *ZYNAH* ta karaso inda suke, gaishe shi tayi sannan ta juya zata wuce *ASHRAF* ya dakatar da ita yace "big bro meet *ZYNAH*, nd u meet my elder brother", kara gaishe shi tayi shikuma tsayawa yayi yana Kallonta harseda *ASHRAF* ya dan taboshi sannan ya amsa gaisuwan ta itakuma tayi ciki, juyawa yayi wurin *ASHRAF* yana tambayarshi me takeyi a gidan *ASHRAF* yace  mishi a nan take da zama tana zuwa school ne, wani dadi yaji a ranshi jin ance a gidan take sannan suka canza hira. Humaira ta fara shirya kayanta saboda gobe ne tafiyanta, sosai take jin takaicin rashin kiranta da KB beyiba, gashi yanzu inta koma batasan yazatayi da son *ASHRAF* daya addabeta, hada kayanta takeyi jikinta ba lakka har ta gama sannan ta tashi ta koma kan gado ta zauna tana kokarin turawa *ASHRAF* sabon text, tana gama typing a karshen tasake rubuta _by a secret admirer_ sannan ta tura, se a lokacin ta dan ji dama dama saboda tasan ze gani kuma koda beyi reply ba baze dameta ba.

     Sameer ne a bakin gate din gidansu *ASHRAF* yana jiran yaga wucewar Basma dan yasan yanzu dai tana hayar dawowa daga school, hangota yayi ta hakimce a bayan mota ita da Husna, Juwairiya na gaba tana zubawa driver dinsu surutu dayake Basma ba'a bata mota ba tukun sabida haka driver dinsu Husna ke kaita school yake dawo da ita, motan na karasowa kafin drivern yayi horn Sameer ya karasa wurinsu, ya kwankwasa  mata, wining din glass din tayi tace "Ya Sameer ina wuni", murmushi ya mata yace "lfy lau, in bazan takuraki ba dan sauko", ba musu ta sauko driver ya shiga dasu Husna ciki sukuma suka tsaya jikin fence din gidan,  Kallonta yayi yace "Basma manyan mata, ya school", murmushi tayi tace "school alhmdllh ", "da kyau, kar in tsaya bata miki lokaci magana ce nakeso muyi wacce bata wuce daya zuwa biyu ba, dafatan zaki bani hadin kai", In Sha Allahu", "gud, Basma in zaki lura keda kanki zaki iya gane cewar ina dauke da dakon sonki tun ba yau ba, amma sena kasa fitowa in gaya miki, se yanzu na samu courage din, saboda haka yau nafito na fallasa miki sirrin zuciyata, dafatan bazaki bani kunya ba?", wani dadi taji a zuciyarta tace "ashe bani kadai ke dauke da dakon sonshi ba, soyayya kin min adalci nagode", jin tayi shiru ne yasa yace "kinyi shiru Basma, ko ban miki bane", "a'a bahaka bane Ya Sameer amma inaso ka bani lokaci inyi shawara", "shikenan zan baki, se yaushe zan dawo jin amsa daga gareki", "duk randa ka shirya", dariya yayi yace "ai ni ko yanzu ma a shirye nake", "shikenan kadawo nan da jibi", "shikenan Allah ya kaimu jibin, da fatan zan samu amsar da zata gamsar dani?" murmushi tayi tace "Allah dai ya kaimu", yace "ameen", sannan ya barta ta shiga gida.

     Uncle Yusuf da Minal dai har yanzu ana nan yanata fama da ita ta waya amma ita tsoron ta daya kar bayan wasu lokuta yayi sabuwar budurwa ya rabu da ita,  sosai ya rame saboda accepting dinshi da Minal takiyi a matsayin boyfrnd dinta, da ace zata ganshi ido da ido a lokacin dase ta tausaya mai dan sonta ya sashi gaba, ga aiki da sukeyi akan wani criminal dayaje yayi robbing bank ya kwasa kusan 500,000million, amma inaa Minal taki ta bashi hadin kai saboda tsoro, yau dai tace In Sha Allah inya kirata zatace mishi ta amince saboda *ZYNAH* tace mata baya bin mace sau biyu da sunan ta amince dashi amma ita ai nacin da yakemata baya kirguwa, daddare wayanta yafara ringing tasan shine saboda haka seda taja ajin ta kadan sannan ta dauka, seda suka gama gaisawa sannan yafara mata magiyan da yasaba, cikin kwantar da murya tace mishi "naji i will be ur girlfriend, amma kar nan gaba kazo rabu dani", ai besan sanda yayi ihun murna ba tareda cewa "ni na isa in rabu dake, nasha gaya miki a baya cewar ke kadai ce mace danaji inasonta tsakani da Allah kuma so bana wasa ba", murmushi tayi tace "nagode, Allah ya tabbatar mana da alherin da ke cikinsa, ya kori sharrin da ke tattare dashi", ya amsa mata da "Ameen my baby mama", daga nan sukaci gaba hiransu irin na masoya dasuka tsumu suka jiku acikin soyayya (lol).

     _Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now