Chapter 22

1K 68 1
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

            *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITERS ASSOCIATION*

QUOTE:-" Some people make themselves miserable and everybody else miserable when they can rather make themselves happy and everybody else happy".

     _I dedicate dis page to my loved ones.😍_

                 2⃣2⃣

     *ASHRAF* kasa barci yayi saboda tunanin da ya addabeshi na *ZYNAH* besan meyasa ba amma da ya rufe ido ita yake gani, tambayan kanshi yayi "wats dis strange feeling all abt?, i've neva felt dis wit any other gurl?, den y her? haka yata tambayan kanshi questions amma ba wanda ze bashi amsan su (nikuwa nace yaro ka fada tarko), bashi yasamu barci ba se around 2:30 na dare sannan sarkin sata yayi gabadashi, yauma yayi mafarkin dayasaba, wannan ma same girl dince amma dis tym around kwance take tana barci hannu ta da kafafunta duk tayi lalle kaman amarya. Kiran sallah ne ya tashe shi, tashi yayi tareda addu'an tashi daga barci ya shiga bathroom yayi alwallah yawuce masallaci yayi sallah, a masallaci ya hadu da Sameer yace mishi "da wuri zan tafi school fa" Sameer ya kalleshi yace "base 10 kakeda lectures ba" ,"eh akwai abunda zanyi ne shiyasa" ,"ok, ba matsala, se mun hadu a school kenan danni se 12 zan shigo" ,"shi kenan toh se mun hadu" Sameer ya shiga gida shima *ASHRAF* ya wuce gida. Koda yaje gida be koma barci ba,(dukda besamu isasshen barci ba), wutan dakinshi ya kunna yadauko sketch board dinshi da komai daze bukata ya fara drawing(da asuban fari sekace masifa), bashi ya gama ba seda gari ya waye sosai sannan,ya tattare wurin, ya shiga wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya dasuka bala'in mishi kyau, ya dau comb ya taje kanshi sannan ya feshe jikinshi da turare. Se dadi yakeji,kowa ya ganshi yasan yana cikin nishadi badan komai ba sedan zeje school kuma yanasa ran zega *ZYNAH* koma dama itace dalilinshi na son zuwa da wuri. Ya gama abunda zeyi ya fito, yasan en gidan basu gama tashi ba saboda haka yayi tafiyarshi.

     Ita kuwa gimbiyar barcinta take sharba dan lectures dinta se 9:30, ba ita ta tashi ba se around 8:30 tayi wanka, tasa english gown black da red veil tayi kyau abonta, ta zauna tasha golden morn kafin tym dinda zata tafi yayi. Ashanty dake zaune a dakin tana chatting tace "na lura bakyason cin abinci sosai, se kayan zaki" murmushi tayi tace "uhmm" kawai, saboda tun a gida in suna cin abinci basa magana. Tana gama sha ta duba agogon hannunta taga 9:10 ta sauke ajiyar zuciya dan tasan tafiyar 20min ze kaita class, sallama tama Ashanty tasa takalminta ta fita. Shi kuwa gogan tun karfe takwas ya kai school, yaje ya tsaya ta inda sukayi karo da *ZYNAH* jiya, yanata sa ran ganinta amma shiru babu ita ba alamun ta, se addu'a yakeyi Allah yasa ya ganta, agogon hannunshi ya duba yaga 9:15 yace "ya Salam, tym na wucewa,Allah ka bayyana min ita, kafin in shiga lecture hall" ai kuwa bagama rufe baki ba ya hangota tana tafiya a hankali kaman me tausayin kasan, wani ajiyar zuciya ya sauke tareda cewa "alhamdulillah" ya matsa ta jikin bangon wurin saboda kar ta ganshi, kallon ta yakeyi har ta bace mishi sannan yafito yace "nw i can concentrate in class" tareda wucewa yanata zuba murmushi. Coffee shop ya fara zuwa yasha coffee dan besa komai a cikinshi ba a gida, yana gama sha ya wuce class kafin lecturer dinsu ya shigo. Ita ma *ZYNAH* class ta shiga taga har an cika, daga kanda zatayi ta hango Shaheeda tana daga mata hannu tareda nuna mata wurin zama, direct wurin Shaheeda ta nufa ta zauna suka gaisa, ba dadewa lecturer dinsu ya shigo suka fara lectures.

     Suna gama lectures dinsu na ranan, *ZYNAH* tace zata library dan tanaso tayi aiki akan research dinda akace suje suyi kan _HUMAN ANATOMY_, Shaheeda ma binta tayi sukaje tare dan *ZYNAH* na burgeta koba komai taga alaman kwanyanta na ja. Suna zuwa library din suka shiga, da mutane aciki wasu na karatu wasu na hira, can lungu sukaje suka zauna inda kusa dasu KB ne zaune yasa yarinyar mutane gaba yana tsarata yana mata dadin baki. Yanda suka zauna yasa yake ganin gefen fuskokin su amma yafi kurawa me jan veil ido har wacce yakewa magana takalla inda yake kallo dan taga me yake kallo. Ganin wacce yake kallo yasa haushi ya kamata tace "KB wai kai wani irin dan akuya ne, ni ka kawoni nan kanamin dadin baki, kaga waccen koma ka kyalle ni ka zuba mata na mujiya,in banda kai maye me zaka ci da waccen karaman yarinyar" haushi da takaici duk ya turnukeshi besan sanda yakai mata mari ba yace "ke dan Allah wawiya masa ki bani wuri, dan naga kyakyawar mace na kalleta nayi laifi, ai kowa ma nason abu me kyau,shashasha kawai" dafe da kuncinta tace "KB ni ka mara" yace "an mark din" ba tace komai ba tayi kwafa ta wuce. Duk wannan abunda daya faru a gabansu *ZYNAH* ya faru, dama gata matsoraciya tace "Shaheeda let's get out of here" Shaheeda ta mike zasu fita, KB yayi sauri ya tare gabansu tareda cewa "bby ji mana, Dan Allah minti daya" Shaheeda ta tsaya *ZYNAH* tayi sauri tace "let's go" tareda jan hannunta sukayi sauri suka fito, suna fitowa sukaci karo da *ASHRAF* da Sameer shima kallonshi kawai tayi ta wuce janye da hannun Shaheeda.

     Binta yayi kallo amma se kuma yaga KB ya fito yana neman hanyarda sukabi, dam *ASHRAF* yaji gabanshi ya fadi ganin KB ya fito daga inda *ZYNAH* ta fito, sannan yanayin da suka fito da yanayin da shi KB din ta fito yasa yasan da wani akasa. Muryan Sameer yaji yana cewa "a KB kwana biyu, lfy na ganka haka" ,"wlh lfy lau, akwai abunda nake nema ne, inazuwa" yayi gaba batare da yaji me Sameer din zaice ba. *ASHRAF* ne ya kalli Sameer yace "da matsala" Sameer ya kalleshi yace "bangane da matsala ba" ,"kaga wa'anda suka fito da farko mata biyun nan" ,"eh, meyafaru" ,"toh me jan mayafin nan itace yarinyar da nake baka lbrn ta, itace wacce muka hadu a airport, itace wacce muka hadu jiya" ,"ar u sure" ,"yes am sure of it, nd it seems lyk dis f*ckin  KB is up to sumtin" Sameer da kanshi ya gama daurewa yace "guy calm down" ,"hw do u expect me to calm down" shi Sameer mamaki reaction din *ASHRAF* ke bashi yace "guy u ar over reacting, calm ur self down, or d u luv her?" *ASHRAF* da idonshi ya gama kadawa yace "yes, yes i luv, i luv her from day one, i luv her from d very first day i saw her, nd i won't sit nd watch dat son of a b*tch ruin in her precious life" yana fadan haka ya juya yabi hanyarda KB yabi batare da wani tunanin ba, shi kuwa Sameer da yaji maganan abokinshi  kaman saukan aradu se ya tsaya a wurin kaman statue yana tunanin hanya *ASHRAF* ne yayi wannan maganan koko waninsa ne. Dago kanda zeyi se yaga ba *ASHRAF* wurin bashiri  shima yabi bayansu.

     A bayan cafeteria KB ya cimma su *ZYNAH*, ba shiri ya tareta tareda cewa "Dan Allah ki tsaya kiji abunda zance plsss" tsayawa sukayi badan komai ba sedan hadasu da Allah da yayi, seda ya tabbata ya samu nutsuwa sannan yace "in dan ba zaki damu ba me sunanki" *ZYNAH* ta kalleshi daga sama har kasa sannan tace "mallam fada abunda ya kawo ka ni sauri nakeyi" sunan da ya tsana ta kirashi dashi "wai mallam" amma se kawai ya share yace " kinganni nan am a stright forward guy,saboda haka in zan fada abunda ke raina bana kwana kwana, shiyasa abunda ya kawo shine, yarinya sonki nakeyi, if u will give me d chance i will lyk to b ur boyfriend" kallon tara saura kwata ta mai kafin tayi dariya tace "am nt interested" taja hannun Shaheeda zasu wuce yakara tareta yace "naga alamun ke bakuwa ce a school dinnan, saboda haka zan baki assignment kije kiyi bincike waye Kabiru Usman Sani Paki aka KB" ta kalleshi ta buga tsaki sannan tace "i neva said i was interested in knwin who u ar, so please excuse me". Batayi nisa ba taji an damko hannun ta, daga kai tayi taga KB ne, cike da masifa tace "hey let me go, who gave u d write to hold my hand" ya kalleta yayi murmushin mugunta yace "yarinya in aso kisani na tsane mutum yace min mallam, na daya kenan, na tsane tsaki, na biyu kenan, na tsane ina magana mutum ya wuce ba tareda na bashi izini ba, na uku kenan, koma ke kinyi duka, saboda haka u will pay for all dis or else se school dinnan ya gagareki zama. Wannan karon ba *ZYNAH* kadai ba harta Shaheeda ta tsorata da lamarinshi,cikin sanyin murya kaman wacce zatayi kuka tace "pls let let me go, u ar hurting me" yace "i won't", murya sukaji yana cewa "let go of her" duk suka juyo, *ASHRAF* suka gani tsaya yana kallon su, KB yace "inna ki fa" yanzu kam kishi ya gama turnuke *ASHRAF* ganin yadda KB ya rike hannun *ZYNAH* yace "KB ka saketa" ,"me zakayi in ban sake ta"  tsabar takaici *ASHRAF* besan sanda yakaiwa KB naushi a hanci, ba shiri KB ya saketa se jini a hancinshi, jin abu na fitowa daga hancinshi yasa hannu dan yaga komenene, jinin da yagani ne yasa hankalinshi ya tashi, se kuma yayi murmushi ya yunkuro ze kaiwa *ASHRAF* naushi *ASHRAF*  ya kauce tareda kai mishi wani a ciki, be tsaya ba seda ya tabbata ya kai KB kasa yanata suburbuda mishi naushi ta ko ina, *ZYNAH* da Shaheeda se kokari suke su rabasu amma inaaa karfin mace da namiji ba dayaba, ganin sunkasa yasa suka fara ihun help suna neman taimako, kan kace me wurin ya cika da jama'a amma an rasa wanda ze rabasu. Sameer ne yazo wurin da saurin shi, yana hango *ASHRAF* yayi sauri ya karasa wurin ya daga shi daga kan KB shima KB aka dagashi suka tsaya sunama junansu kallon kallo tareda maida numfashi.   

        *INTER MISSION* 
THIS IS JUST D BEGINNING.

     _Short page, am sorry, i hav my reasons.keep following.....Luv u guy😍_ 

        _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu