Chapter 25

955 63 2
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITERS ASSOCIATION*

QUOTE:- "When something bad happens, something good happens in return because no matter what you do somebody is looking out for you and you never know who that could be".

     _I dedicate dis page to *Fatima Ibrahim Munnira* swthrt her is a page for u wit much luv😍._

                   2⃣5⃣

     Kwance take da misalin 10:30 na safe sega Ashanty ta shigo, kujera taja ta zauna kusa da ita tace "ya jikinki?" ,"da sauki" cike da tausayawa Ashanty tace "sannu kinji, Allah ya baki lfy" murmushin karfin hali kawai *ZYNAH* ta iya mata sannan Ashanty tace "ga phone dinki na kawo miki, kinaso a kira wani a gida?" kai ta kada tace "karki kira kowa, hankalinsu  ze tashi, zan kira su amma ba yanzu ba" ,"bakya ganin hankalinsu zefi tashi in suka kira sukaji shiru, kuma kema baki kiraba?" ,"karki damu ba abunda ze faru" ,"toh shikenan, kinci abinci" ta kada mata kai. Dahaka sukata guntayen hiransu har wurin daya da en mintina sega Shaheeda ta shigo Ashanty tace "tunda Shaheeda tazo ni bari na wuce, maybe na dawo da yamma ko da daddare" suka ce toh tareda yi mata sallama ta wuce. Shaheeda ta zauna tana mata ya jiki ta amsa mata da sauki, suka dan taba hira, Shaheeda ta fada mata *ASHRAF* yace zezo, a fili tace "Allah ya kawo shi lfy" amma a zuciyarta wani ni'imtaccen dadi taji, jin ance *ASHRAF* zezo ganinta.

     Ya idar da sallah ya shiga motanshi ya kira Sameer, "Hello Sameer kana ina Zanje hospital din" ta daya bangaren Sameer yace "i'm very sorry, amma bazan samu zuwa ba, yanzu mummy ta aike ni kano, zan kai sako" ,"ok no prob, drive carefully ok" ,"ok, bye". Motanshi ya bawa wuta ya harba titi, dede wani store ya tsaya ya shiga yayi mata  siyayyan kayan drinks, su hollandia, five alive da saransu, sannan ya siya mata kayan strawberry, grape da saransu, ya fito yasa kayan a mota, seda yayi gaba kadan sannan ya samu me siyar da orange  ya siya mata orange da Apple ya shiga mota ya dau hanyar asibiti. Duk wannan bidirin da yakeyi GAINT na bayanshi yana binshi. Yana zuwa harabar asibitin yayi parking ya shiga, dama Shaheeda ya fada mishi dakin da take saboda haka wurin ya nufa direct, tsayawa yayi a bakin kofan dakin yana tunanin yanda zeyi ya shiga. Daga baya kawai seya sadakar yayi knocking Shaheeda tace "come in" ya bude kofan ya shiga da sallamanshi suka amsa, Shaheeda ta tashi ta tayashi da kayan hannunshi, ta karba ta ajiye akan tebur tayi ma *ZYNAH* sallama tace zataje ta dawo. Fita tayi ta basu wuri *ASHRAF* ya karasa ya zauna yace " *ZYNAH* ya jiki" tace "da sauki" ba tareda ta bari sun hada ido ba yace "sannu, ya kike jin jikin yanzu?" ,"yayi sauki ba kaman jiya ba" ,"Allah ya kara sauki" tace "Ameen" da haka dakin ya dau shiru, shi bece komai ba itama haka duk sunyi shiru. Da taga beda alaman yin magana seta gyara kwanciyar ta dan barci takeji, ai kuwa koh minti biyar ba'ayi ba tafara gyangyadi, duk yana lura da ita amma yayi shiru kuma beson ya wuce dan be gaji da ganinta ba, ganin tayi barci ne yasa ya matso kusa da ita yanata kallo  ta daga bisani yasa hannu ya dau wayanta, cikin sa'a kuwa yaga ba password ya bude yayi dailing numbanshi ya kira sega numbanta a screen dinshi ya kashe yayi deleting na wayan ta sannan yayi saving nata da *MY DREAM GIRL* sannan ya maida wayan aljihu ya wuce, har ya kai bakin kofa se kuma ya juyo ya kalleta ya dawo ya bata peck a goshi ya gyara mata blanket dinta sannan ya fita.

     A wajen asibitin kuwa GAINT na nan yayi parking yana jiran fitowan *ASHRAF* sannan ya kira sauran en gang dinsu yace su jirasu gaban asibitin kadan gasu nan zuwa, fitowa *ASHRAF* yayi ya shiga motanshi ya bar harabar asibitin GAINT ya bishi a baya ya dau waya ya kira sauran  yace su tareshi gashi nan zuwa, yana cikin mota Mercedes benz baka, yasa farin shadda da bakin hula, nan dai yayi musu discribing komai akan *ASHRAF* suka ce shikenan ya biyo bayanshi su zasu tareshi ta gaba. Shikuma bawan Allah tafiya ya keyi yana tunanin abar sonshi, rabin ranshi, har yana ganin da ze iya daya dawo da ciwon jikinshi, be an kara ba yaga mota ya tare gabanshi, wani wawan birki ya taka wanda seda tayanshi ya goga kasa, ji kake kiiiiiiiii ya taka birki. Dagowa  yayi dan ganin waye ya tareshi haka, amma ganin wasu karti yasa yasha jinin jikinshi ga ba daman reverse dan motan GAINT ne a bayanshi, cikin sauri GAINT ya fito ya bude motan *ASHRAF* yace "out" *ASHRAF* yaki fitowa, GAINT yace "bana magana so biyu, oya fito" shikuwa yaki fito ya tsaya yana musu taurin kai (dama ASHRAF akwai zuciya) ganin yana musu taurin kai kuma basason wani yabiyo hanyan ya gansu yasa GAINT ya dinga kaiwa *ASHRAF* naushi harseda ya mishi jina jina ya galabaitar dashi sannan ya janyoshi ya turashi motanshi ya nuna daya daga cikin sauran yace "kai ja motanshi muje" cikin seconds dinda be wuce goma ba har sun vacate daga wurin se kura ke tashi(Allah sarki *ASHRAF*😔).

**********
     KB ne da SMART  a guest house suna zaune suna buga chess game, jin tsayuwar mota yasa KB yayi murmushi yace "shegun sun cika aiki" tashi yayi ya tsaya, sega su sun shigo rike da *ASHRAF* fuskanshi duk jini kayan shi ma yayi stain da jini, durkusar dashi sukayi ya durkusa gwiwa bibbiyu a kasa KB fara musu tafi yace "yara kun cika aiki, kuma zanmuku tukwaici" sannan ya juyo wurin *ASHRAF* ya kalle shi ya juya ya kalle SMART yace "kunganshi, so full of himself, nan besan ba'a yiwa KB iya shege ba" seya fashe da wani bazawarin dariya, *ASHRAF* cikin muryan da ke nuna ya galabaita yace "KB y ar u doing dis?" seda ya make *ASHRAF* yasa hannunshi ya matse mishi wurin hakarkarinshi yace "u idiot, don't tell me u've forgotten wat u did to me 1 mnth back, an ce maka na kyale ka ne? toh inaso kasani ba'a taba KB aci lafiya, komin daren dadewa seya rama, dan haka bazaka bar gidan nan ba sena dau fansa akan ka" sakeshi yayi ya juya wurin  GAINT yace "kuyi seizing wayanshi ku kulle shi a daki kafin na dawo" sannan ya juya wurin SMART yace "tashi muje asibitin kar dare yayi" ai kuwa *ASHRAF* na jin ance asibiti hankalinshi ya tashi dan yasan ba makawa wurin *ZYNAH* zasu kuma yasan halin KB amma ba yanda ya iya haka yanaji yana gani suka fita shikuma aka karba wayanshi aka turashi wani daki aka kulle.

_Kuyi hakuri da wannan ba waya amma bayan sallah zanyi updating pages In Sha Allah_

     *BARKA DA SALLAH IN ADVANCE🤝 SAURA INJI SHIRU ZANCEN NAMA😎*

         _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now