Chapter 51

956 63 1
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

              *ZYNAH*

(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"Relationships are a lot like yard sales, they look really fun from a couple hundred feet away, but then you realize it’s just a bunch of crap you don’t need."

    _Godiya dubu ga masoya na, naji sauki yanzu ba laifi, kuma na gode da addu'oin da kuka dinga min🙏🏻🙏🏻🙏🏻 Allah ya  bar zumunci, luv u all😘😘😘_

              5⃣1⃣

     KB ne zaune da SMART a kusa dashi, gabadaya ya rame ya lalace ya zama wani iri saboda tunani da ya daurawa kanshi, SMART ne yace "wai boss ni bangane maka ba, daga tafiya ka dawo, shine kayi wannan raman, ko dai ruwan garin ne be karbe kaba", kallonshi KB yayi sannan ya sauke idonshi yace "ba ruwan garin bane, tunanin wannan yarinyar ne ya addabeni", " boss har yanzu baka hakura ba, at least ka kyaleta itama tasha iskan duniya, yanzu saboda sha'awanta kayi wannan rama haka, haba boss sekace ba namiji ba, ai naga ba ita kadai bace mace", wani kallo KB yayi mishi yace "SMART bazaka gane ba, wannan yarinyar ni nasan abunda nagani tattare da ita, nd inaso kasani ba sha'awarta kadai nakeyi ba, sonta nakeyi, so kuma na aure, kuma ina tabbatar maka da cewar ko ana ha maza ha mata sena aureta", kallon mamaki SMART ya bishi dashi yace " so kuma, yaushe kafara sonta", wani ajiyan zuciya KB yayi yace "nima bansani amma dan wannan tafiyan danayi na tabbatar wa kaina cewar son yarinyar nakeyi saboda kullum safe rana dare tunanin ta nakeyi, da tunaninta make wuni, nake kwana, nake tashi, kuma yanzu kwanciyar hankali na shine naga na mallake ta" (lallai KB ka debo da zafi😅).

     Kallon tausayi SMART ya mishi dan yasan wannan karon dai da wuya ogan shi ya samu abinda yakeso, seda ya sauke ajiyar zuciya sannan yace "toh yanzu  boss ya zakayi, ka riga ka bata reputation dinka a wurin yarinyar nan, kallon daniska take maka, kaga ba yanda za'ayi ta yarda da kai", " hakane, shiyasa ma ba zanbi ta kanta ba, kawarta ce weapon dina, da ita zanyi amfani, kuma nasan zan dace in nabi ta kanta", "kagana ganin zata baka hadin kai", " ai dole ta bayar, ba yanda ta iya, dan in tace bazata ban hadin kai ba, sena sata dole, kana magana kaman bakasan KB ba, tsaya ma ka gani", wayanshi ya dauka ya kira Humaira wacce ta riga ta dade da give up akan lamarin *ASHRAF* dan ya kai stage din da data turo mishi text, zagin ta yayi tatas harda cemata ya tsani mata masu cewa suna son maza, saboda haka tun lokacin ta hakura, ganin wayanta na ringing ne yasa ta duba, ganin KB yasa taki dauka, seda ya mata kusan 5 missed call sannan ta dauka ba tareda tace komai ba, "ina kika ajiye waya inata kiranki", tace " me kake bukata, kaga banda wani business da kai yanzu dan Allah ka kyale ni", wani bazawarin dariya yayi yace "yarinya kinyi kuskure da kikayi tunanin zan rabu dake ba tareda mun gama deal din da ke gaban mu ba, inaso kisani cewar  ni yanzu son *ZYNAH* nake kuma da  aure kaman yadda kikeson *ASHRAF* saboda haka dama tafiya nayi shiyasa kika jini shiru amma yanzu na dawo, yanzu zamuci gaba daga inda muka tsaya", jin yace son *ZYNAH* yakeyi da aure yasa tuni shaidan ya buga mata ganganshi taji tanason taci gaba da harka da KB, maybe he is d only key she can use to get to *ASHRAF* , nan tace mai " toh taya zakayi haka, taya zaka maida ita naka? nima taya *ASHRAF* ze kula ni", ni shu'umin murmushi yayi ganin tarkon da ya dana ya danu yace "kina school ko kunyi hutu?", " cikin week dinnan zamuyi hutu", "good da zarin kunyi hutu ki san yanda zakiyi kizo Zaria, in kinzo ki neme ni", tace " ba matsala dama i hav plans of coming", yace "se kinzo", dif ya kashe wayan. Zama tayi tana tunanin hanya wannan abun da takeyi bazeyi affecting relationship din ita da *ZYNAH* ba (ni kuwa nace ai yariga yayi).


     A cikin satin kuwa su Humaira suka gama exam, tace wa Umman ta zataje Zaria ganin *ZYNAH*, bata musa mata saboda tasan kusancin su, nan ta kira *ZYNAH* take shaida mata cewar jibi zatazo , nan ta dinga murna bestee dinta zatazo gaishe ta (da kinsan zuwanta ba alheri bane da bakayi murna ba😔), ranan asabar Humaira ta dira garin zazzau, seda ta huta sannan ta kira KB ta shaida mishi tana Zaria, sosai yaji dadin zuwanta yace mata gobe zezo unguwar su ta tabbata ta fito mishi da *ZYNAH* amma kar ta kuskura ta bari su fito tare, ko ita ta fara fitowa ko *ZYNAH* ta fara, kar dai a gida agane sun fito tare saboda kar ayi suspecting wani abu, cike da mamaki tace "me za'a yi suspect dan mun fito tare", " kedai kawai kiyi abunda nace, nd believe me idan kika bi instructions dina daidai bazamu samu matsala ba", cikin sanyi murya tace "shikenan, in kazo seka kirani se na fito", da haka suka gama ta kashe wayan tana tunanin wat is KB up to.

*WASHEGARI*

     (Ga ranan da ni da kaina writer din nake tsoron zuwanshi😭😭), KB bashi yazo ba se yamma lis wuraren karfe shida be shiga cikin unguwan sosai ba, yayi parking a ta waje wajen unguwan ya dau waya ya kira Humaira, itace kadai  a dakin saboda haka tana ganin kiran ta dauka, nan ya mata kwatancen inda yayi parking mota tace gata nan zuwa, hijab tasa ta fita ba tare da wani ya ganta ba saboda duk suna kitchen, wurin KB taje ita da kanta raman da yayi ya bata mamaki, amma gudun kar  su bata lokaci wani ya ganta yasa tayi sauri tace "KB gani me zamuyi yanzu", murmushi yayi yace " yanzu kirata kice ta fito tazo ta same ki anan amma karta bari wani yasan da fitowar ta", kiran *ZYNAH* tayi wacce fitowan ta kenan daga bathroom taga wayan ta na ringing, ganin Humaira ce me kiran shiyasa tayi sauri ta daga tace "hello bestee, ba kya gida ne kike kirana", " eh, ina waje yi sauri ki fito abu zan nuna miki, nd ke kedai zaki fito kiyi sauri", seta kashe wayan KB yace "dats gud", ita kuma *ZYNAH* mamaki takeyi me Humaira zata nuna mata da zatace tazo ita kadai, se kuma tace " well mayb she wants to surprise me" tayi murmushi (yh a big surprise my bae😥), highwaist skirt tasa baki da Vinci top blue, mayafi tasa sannan tasa kalaminta ta dau wayanta ta fita, ita ma data fito bataga kowa a parlour din ba, taso taje kitchen ta shaidawa Ummi taza fita amma kuma seta fasa tayi ficewarta wanda me gadi ne kadai yaga fitan ta, dan yana zaune yana alwallah saboda an fara kiran sallan magrib, koda ta fito bata ganta ba saboda haka ta kira ta, Humaira dauka tayi ta mata kwatancen inda take *ZYNAH* ta karasa wurin, ganin KB da Humaira tare ba karamin mamaki tayi ba, sannan ga fargaba da tsoro nan karara a idonta dan rabonta da KB tun lokacin da yasa aka kai mishi ita love garden, cikin in'ina tace "Humaira kinsan kowaye wannan kuwa, me kikeyi a nan", kafin Humaira tayi magana KB ya rigata da cewar " hey baby girl, longest tym, ashe baki manta dani ba", hararanshi tayi ta juya zata bar wurin yayi sauri ya kamota da hannu daya tareda ciro hanky da dayan hannu ya shaka mata a hanci, tun tana turjewa har tazo tayi lamo a jikinshi, wani murmushi yayi ya turata mota, Humaira kuwa kallon wurin tayi taga ba kowa sannan ta juyo gaban KB tace "wat ar u doing, we neva planned dis, me kake shirin yi", tana magana muryanta na rawa, shafa sajensa yayi ya kalleta yace " look here, kwantar da hankalin ki,inaso ki yarda dani dis tym around, inason *ZYNAH* saboda haka bazan cutar da ita ba, na mata hakane saboda nasan ta da taurin kai, yanzu abinda za'ayi shine kije gida zan turo miki address din da zaki zo ki same ni gobe", cikin tabbatar da maganan ta tace "kana nufin tafiya da  ita zakayi", cikin halin ko in kula yace " yes, akwai maganan da nake so muyi da itane, kinga banda lokaci, ga wayan ta ki tafi mata dashi gida, karki kuskura ki bari a gane u hav sumtin to do wit her disappearance", yana fadan haka be jira cewarta ba yaja mota yayi gaba ya bar ta nan tsaye kaman an shuka dawa.


      _kuyi hakuri da wannan ba waya, nasan u will all b eager to no wat d next chapee holds, well der will b a bomb blast in d next chapee, comment plss😊_

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now