Chapter 60

1.2K 68 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻


              *ZYNAH*


(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:-"When something bad happens, something good happens in return because no matter what you do somebody is looking out for you and you never know who that could be."

                 6⃣0⃣

*BAYAN WATA BIYU*

    *ASHRAF* da abokanan shi da Fahad da abokanan shi da Haydar sun diro Lagos inda sukayi lodging hotel ko wani daki mutum biyu, su Ammi duk sunzo wannan karon har da Ummi Abba kadai suka bari a gida shima yace ana jibi daurin aure zezo, Ashanty ta samu zuwa, dagin Daddy dasu ke kano duk sunzo, haka iyayen Momsie ma sunzo, gida ya cika da dangi da abokan arziki, dole en matan suka koma gidan Minal saboda cika, amma *ZYNAH* tana gida, an bata dakin Uncle na da sun koma ciki dayake a kasa dakin yake, Humaira ma ta dawo gidan take kwana saboda shirye shiryen biki, *ZYNAH* tasha gyara jikinta se kyalli da tsantsi take, ance idan ana aure amarya ramewa takeyi amma banda *ZYNAH* dan ta dan kara cikowa, in ta fito ta gifta mutum se kayi minti biyu baka daina jin kamshin ta, Momsie kai yayi zafi tana aurar da 'ya, Islam kuma koda yaushe cikin fice da shige take ita kanta batada lokacin kanta. A ranan dasu Ammi zasu zo a ranan aka kawo lefe kowa ya yaba da kayan se albarka ake sawa auren.



     Sun shirya events kala bakwai wanda zasu fara Monday nyt su gama Sunday, yau yakama Monday wanda ana idar da sallan isha suka fara shirin zuwa Sheraton hotel inda zasuyi couples nyt wanda Minal ce ta shirya musu wannan liyafar, *ZYNAH* ta fito cikin ball gown pink me ratsin silver a jiki tayi kyau sosai, nan su Humaira kuma suka sa evening gown amma kowa nashi da ban suka shiga mota se Sheraton, koda sukaje *ASHRAF*  be karaso ba saboda haka *ZYNAH* tayi zaman ta a mota tana jiranshi, cikin minti biyar ya karaso inda shima yayi shigan black suit da pink inner tareda silver necktie ga gashin kanshi nan yasha gyara, zuwa wurin motan da amarya ke ciki yayi ya bude, mutuwan tsaye yayi ganin halittan da ke gabanshi dan rabonshi da ita wata daya kenan, seda Sameer ya taba kafadanshi sannan ya dawo hayyacinshi yayi murmushin da shi kadai yasan ma'anar shi ya mika mata hannu ta rike  hannunshi tareda fito kafarta sanye da silver baby shoe flat, cikin hall din suka nufa su Basma da Humaira da Islam suka mara musu baya, wakan My Darling by Tiwa Savage aka samusu as dey step into d hall, suna shiga ko ina ya dau tafi saboda yadda suka birge, hall din amshi decoration da pink nd silver, table of four ne zagaye da wurin, ko wani table couples biyu, wanda yawancin su abokan aikin Uncle ne, zuwa sukayi suka zauna inda aka tanadar musu su Uncle sune en high table se Fahad da bayan da ba'ayi da shi a kan ya zauna high table ba ya kiya, yaje ya zauna kusa da abokanan shi sunata mishi tsiya wai yazama gauro yabari kaninshi ya rigashi aure, nan aka gudanar da taro bayan an bude taro da addu'a akayi abunda za'ayi aka tashi amarya da ango sunsha barin kudi. A gajiye suka koma gida saboda haka suna zuwa kowa ya nemi lafiyarshirin gado.



     Washegari bridal shower suka wanda Humaira da Basma ne suka hada mata, amarya ta fito cikin white gown inda su Basma sukayi shigan riga pink da wando blue suka fito as bride's maid Islam kuma bride's sister, a gidan Minal sukayi wannan anyi party na gani na fada karfe shadaya suka gama, duk suka koma gida. Ran Thursday kuma sukayi Red carpet wanda Islam ce tayi organising dinshi, shima din gown *ZYNAH* tasa white su kuma yayi sukayi na wani material, sunyi partyn ya kayatar sosai, duka wannan shagalullukan da akeyi *ZYNAH* hankalinta kwance.



     Washegari Juma'a kuma ranan za'ayi kamu, tun da safe er Maiduguri tafara wa amarya kunshi basu suka gama ba se shabiyu na safe, wanka tashiga ta wanke kunshin da aka mata tayi wanka ta fito wani atampa super Holland aka bata tasa, tayi kyau sosai zama tayi aka kawo mata abinci taci sannan tayi sallah, karfe hudu aka fara shirye shiryen kamu wanda za'ayi a compound din gidan, *ZYNAH*  lace tasa milk colour dinkin buba da ipele wine tayi head dashi, zanso kuga yanda *ZYNAH* tayi kyau ta fito shar amarya se smilling takeyi, su Humaira kuma yayi suka sa na atampa suma sunyi kyau, anyi kamu nagani na fada wanda duk wanda yazo seya tafi da mafici ko tsintsiyan laushi, kayan gargajiya dai aka raba a wurin su *ASHRAF* se da aka kusa tashi suka zo shida mukaraban shi shima liki yazo yayi sannan aka dau hotuna suka wuce, sosai ya yaba da kyan da tayi. Washegari akayi biki na gani na fada inda amarya ta fito cikin material blue da head off white, sosai tayi kyau shima anyi sagali kaman ba gobe an raba kayan bokatai da sauransu.



      Rana bata karya yau Allah ya kowa mu, inda dun bin jama'a suka shaida  daurin auren *ASHRAF SAGIRU FILLO* da *ASEEYA (ZYNAH) MUHAMMAD SANI MAI DALA* akan sadaki naira na dukan naira har naira daidaidai har dubu dari lakadan ba ajalan ba, *ASHRAF* na jin an daura aure ya tashi yayi sujjadan shakur yana godema Allah daya bashi *ZYNAH* a matsayin mata dan yasan ko ba'a fadamai ba yayi dace, nan abokanan shi suka fara mishi tsiya ana ango kasha kamshi, shikuwa murmushi kawai yake musu a zuciyar shi kuwa  cewa yake "yau lissafi ya cika, *ZYNAH* ta zama iyalina na, nima yanzu ina da iyali". Ta bangaren *ZYNAH*  kuwa ana daura aure taji alama jikinta, shiru tayi duk hiran da akeyi ta daina sa musu baki se tunani takeyi yanzu shikenan ta zama matar aure, Minal ce tashigo da dan karamin cikinta ta hai guda sannan tace " yau wata ta zama ta *ASHRAF* yanzu Uncle dinki ya bugo min yace an daure ki, yarinya kema kinshiga sahun mu, zo inmiki lecture", tana magana tana dariya, *ZYNAH* kuwa gabanta ne ya fara dukan uku uku, kan kuce me ta fashe da kuka bil hakki, Basma ce tace "la ilaha illallah, mezan gani haka, bake kikace bazakiyi kuka ba, kikace da bakya sonshi ne shine zakiyi kuka, amma yanzu kukan me kikeyi",  ko kulata *ZYNAH* batayi ba Minal ta matsa kusa da ita tana lallashin ta, da kyar tayi shiru Basma tace " yanzu me yasaki kuka", harara *ZYNAH* ta bita dashi ta tashi ta shiga bathroom ta wanke fuskanta, tana fitowa taji ana ga angwaye sunzo gida duk ya dau guda da me hanci da mara hanci duk yi suke, da sauri aka gyara mata fuskan ta aka mata dauri sannan aka bata mayafi ta rufe fuskan ta dashi suka fito compound inda suka tarar anata daukan hoto, karasawa tayi akaci gaba da hutunan da ita amma *ASHRAF* kallo daya ya mata ya gane tayi kuka, suna gama daukan hotunan suka wuce parlourn Daddy inda akayi musu fada tareda nasiha me shiga jiki wanda *ZYNAH* banda kuka ba abinda takeyi, *ASHRAF* kuwa har cikin jikinshi yakejin zafin kukan da takeyi.



     Karfe biyu aka fara walima inda aka gayyaci Malama Shopie ta mata wa'azi akan zaman aure da hakkokin aure, can na hango su Meela Adeel, , Meenah parrot, Deejatou da en kungiyan su anyi shiru ana saurare kaman da gaske😂 ba kaman meenah dan ita har da sharar kwalla, gefe daya daya kuma en kungiyan Mzz Daddy's Novels ne da ZYNAH  FAN'S CLUB suma sun nutsu suna jin wa'azi, ba kaman Mzz Adam da ABU da Maryam B Sani😂, daga dayan gefen kuma su Fateema Muneera ne da Aisha M Mu'azzam da Anty napi, walima ya kayatar kuma ya ilimantar anci ansha sannan aka watse. Yamma nayi aka fara shirin zuwa wurin dinner. Karfe takwas da rabi su *ASHRAF* suka zo daukan amarya zuwa wurin dinner inda amarya taci kwalliya cikin black material less wanda ta dinka fitted gown dashi amma bayan na jan kasa se silver head, kyaun da tayi bata taba irinshi ba, shima *ASHRAF* ya shirya cikin farin  dinkakkiya shaddanshi wanda yaji aiki da bakin zare kanshi sanye da hula zanna bukar baki shima ya fito shar dashi, kowa ya ganshi yaga angon karni. Anan  Sheraton hotel sukayi  inda dinner ya kayatu Humaira ce tabada brief history din amarya wacce har kuka tayi wurin bada lbrn saboda ta tuna tabarar da tama aminiyarta, Sameer kuma ya bada brief history din ango wanda banda shakiyanci ba abinda yakeyi, taro yayi taro, anyi barin naira, naira tayi kuka wurin *ASHRAF* sannan daga bisani akace lokacin menu menu yayi ai Meenah parrot baki har kunne anji abinci, anci ansha an watse inda aka raba cassette din wankan da akama amarya da ango da memo, calendar, t shirt da sauransu wanda hoton amarya da ango ke kai, an tashi taro lfy an watse kowa ta wuce gida inda su *ASHRAF* washegari da safe zasu daga saboda zuwa dare za'akai amarya.


     _Ba nan naso tsaya wa ba, amma ba3 dina yayi low, manage dis_

     _Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHWhere stories live. Discover now