Chapter 39

943 64 1
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

            
             *ZYNAH*


(An Interesting Luv Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)

*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*

QUOTE:- "Stop trying to get the attention of the people who dont care about you and try keeping the attention of the people who do."

             
                3⃣9⃣

*WASHEGARI*
     Humaira ta gama abunda zatayi ta fito da kayanta, *ASHRAF* yasamata a mota, itakuma taje tayiwa su Ummi sallama bayan sun hada mata shatara ta arziki, Abba ma taje tayi mai sallama shima haka ya cika mata jakanta da kudi, se godiya takeyi, har bakin mota suka rakota ta shiga mota, *ZYNAH* da Minal ne en rakiya, koda sukaje airport basu wuce ba har seda jirginsu ya tace (sedai muce a sauka lfy), *ZYNAH* har kuka tayi saboda rabuwa da bestee dinta, ita kuwa Humaira da takaicin KB ta koma na rashin kiranta da beyi ba gashi har ta bar garin, su *ZYNAH* kumawa gida sukayi, tana shiga dakin ta setaji dakin ya mata girma saboda ba Humaira ciki, zuwa tayi ta dauro alwallah tayi sallahn azahar sannan ta dauko wayanta tana dannawa, Basma ce ta shigo kiranta tazo taci abincin rana, mikewa tayi suka fita tare, dinning suka nufa sukaci abinci sannan duk suka zauna a parlour, tun tana shiru batasa musu baki sosai har tazo ta sake se dariya take kyalkyala dashi, Fahad da *ASHFAR* kuwa se kallonta sukeyi kowa da abinda yake ayyanawa a ranshi.

*LAGOS*
     Islam ce a dakin *ZYNAH* se bincike takeyi hankalinta kwance dayake ba kowa gidan daga ita se Jummalo, bincike take sosai, duka wardrobes din ta duba amma bataga komai ba, last wardrobe ta bude wanda kayan jallabiyan *ZYNAH* ke ciki amma a garkame kuma b key a jiki, toh ina key din ya shiga? tambayan da tama kanta kenan, nan ta shiga neman makulli, ba inda bata duba ba amma ba key ba alamanshi, duk ta gama har gista dikin zama tayi kan gado tana hutawa tunanin ta duk ya dauke tsabar gajiya, wani abu yace mata bata duba saman wardrobe din ba, tashi tayi ta janyo kujeran dressing mirror ta kawo daidai wurin wardrobe din, seda ta tabbata kujeran yayi balance bazata fadi ba sannan ta hau amma duk da haka tsayi ta be kai ba, saboda haka tasa hannu tana lalube, batayi nisa ba taji ta lalubo wani abu kaman makulli, daukowa tayi ta sauko ta bude wardrobe din tana dube dube amma bataga komai ba, haushi da takaici duk sun gama kamata, hawaye ne yafara zubo mata ba kakkautawa, zubo da kayan kasa tashiga yi tana kuka saboda haushi, zama tayi kan gado tana  maida numfashi duk da haka hawaye basu daina zuba daga idonta ba, hango wani abu tayi kaman brown envelope kwance cikin kayan, tashi tayi ta dauko envelope din tareda budewa, ganin papers din filin ne yasa taje wani irin dadi, tsalle takeyi a kan gadon kaman karama yarinya, fita tayi da sauri ta shiga dakinta ta dauko school bag dinta tasa documents din ciki sannan ta koma dakin *ZYNAH* ta gyara ko ina da kayan da ta zubo dasu, duk seda ta gyara kaman ba abunda tayi a dakin sannan ta fito ta koma dakinta, wayanta ta dauka ta kira Kamal tana fada mishi taga documents din saboda haka ran Monday in tazo school se suje su siyar, shima ya tayata murna, sannan yace mata ran Monday karta shiga school intazo ta jirashi a gate din school din,  tace toh, da haka sukayi hanging din call din sannan ta ajiye wayan ta, ranan murna wurinta ba magana.

*MONDAY*
     Islam ta gama abunda takeyi ko breakfast bata tsaya tayi ba tayiwa su Momsie sallama tayi tafiyarta, driver na kaita bakin kofan school din tace ya tsaya a nan base ya shiga ciki ba, ba musu yayi parking ta sauka, shikuma ya kara gaba, wayanta ta dauka ta kira Kamal tace mishi gatanan a gate din school "na ganki", abunda yace kenan sannan ya fito daga cikin wani rantsaten mota kirar _RANGE ROVER 2017_ white color (ashe dan manya ne🤔), karaso wa yayi inda take yace mata muje, ba musu ta bishi suka shiga motan da ya fito daga ciki driver ya jasu batare da yace kala ba, dayake Kamal ya riga ya fada mishi inda zasu, kofan wani karamin building suka tsaya, fitowa sukayi suga shiga ciki, Islam tun a gaban gidan gabanta ya fara faduwa, ji takeyi kaman ta koma, sun kai kofan shiga Kamal ya dago hannu ze kwankwasa kofan tayi saurin rikemai hannu tace "Kamal mukoma, i don't want to do dis again", kallon hala bakida hankali ne ya mata sannan ya kwace hannunshi daga rikon da ta mai yashiga knocking din kofan batare da yace mata kala ba,  "d door is open come in", muryan wani gardi kenan wanda it sounds more lyk iyamiri ne, bude kofan yayi sannan yaja hannunta suka shiga ciki, jikinta se rawa yakeyi, wajen wurin kaman gida amma ciki is more lyk office, zaune yake a kan wani kujera ga babban table a gabanshi se kujera biyu na baki, table din ya cika da files ba adadi, ganin Kamal yasa mutumin yayi murmushi saboda ya sanshi dan yasha siyar da properties din mahaifinshi wurin mutumin, dama shi irin kaya haka yake siya amma hukuma basu sani ba, dan kar ayi suspect dinshi ne yasa yayi ginin kaman gida.

     "Sit", abunda yace musu kenan tareda nuna musu kujera, zama Kamal yayi itakuwa Islam duk ta gama shan jinin jikinta dan gabadaya bata yarda da mutumin nan ba, gashi ta riga tazo ba dama tace ta fasa saboda Kamal zeyi fushi da ita, da ido Kamal ya nuna mata cewar ta zauna sannan ta zauna, suka gaisa da mutumin sannan yace "Kamal, my boy, long tym", "am doing good sir", "dats gud to hear, is she ur girl", ya tambaya yana nuna Islam, murmushi Kamal yayi yace "yes, she's my girlfriend", "dats gud", juyawa yayi wurin Islam yace "Hw u", "
tace "fyn", ganin batada niyyar sakin jikinta yasa ya koma ga Kamal yace "so hw may i help u", gyara zama Kamal yayi yace "my girlfrnd here wants to sell some portion of land to u", kada kai yayi alamun gamsuwa sannan ya juya wurin Islam yace "wats ur my", har zata ce mai Aisha seta tuna ba sunan ta bane akan documents din ba, saboda haka tace "Aseeya Muhammad sani", gyara zama yayi sannan yace "is d land ur's", cikin in'ina tace "yes sir, d land is mine", "gud, why do u want to sell it", kallon Kamal tayi dan batasan me zatace ba, Kamal yace "she needs d money more dan d land, dats y, she's having problem regarding money issues, so if u can help we ar ready to sell out d land", kallonsu yakeyi saboda yanaso ya tabbatar inda gaske suke saboda bayaso yayi abunda zesa a gano shi har ya kaiga kulle shi, ganin alamun kamshin gaskiya a tattare dasu ne yasa yace "can i take a look of d documents", ba musu Islam taciro daga cikin jakanta ta mike mishi, duba yakeyi amma ganin 10 plot of land yasa ya dago kai ya kallesu tareda tambayarsu, "is it all d plots dat u want to sell", "yes", suka amsa mishi dashi ba tareda sunyi tunanin komai ba, ganin basu san me sukeyi ba yasa yamusu tayin banza akan cewa million goma ze siya, kenan kowani plot million daya, ba musu Islam tace ta yarda sannan ya dauko wani file yace tayi signing agreement paper ne, dama ta iya irin signature din *ZYNAH* saboda haka tayi fordging signature din ba tareda ya gane ba, "i will transfer d money to kamal's account nw", suna zaune wurin yayi musu transfer sannan suka wuce.

     Kudin gida uku Islam ta rabashi, ta dau 4% wanda tace Kamal ya ajiye mata a account dinshi, zata karba nan gaba, sannan taba Kamal 3%, 3% kuma suka kai gidan marayu wai donation, ranan ba ita ta dawo gida ba se past 7, cikin sanda ta shiga daki ba tareda wani yaganta, zama tayi kan gado tareda jingina jikin bango, se hawaye(na bakin ciki ki farin ciki🤔), "sister am sorry, i didn't mean to be dis unfaithful, i just can't help myself, ana nuna min tsana a gidan nan duk ta dalinlinki, basan laifin me nayiba",  kuka take sosai tanata maimaita "am sorry sister" ba adadi, kowa ya ganta a wannan halin seya tausaya mata, Itada kanta batasan me ya kaita aikata wannan abun ba, se yanzu take regretting amma aikin gama ya riga ya gama, jin kaman za'a bude kofa ne yasa tayi sauri ta shiga bargo. "Islam", Momsie ta kira ta amma shiru, jin sheshekan kuka ne yasa taje ta yaye bargo,  halinda taga er ta aciki sosai ta razana, "lfy Islam meke samun ki", "Momsie kaina na ciwo, ze tsage", sosai tausayin ta ya kamata, dagata tayi dan ko uniform bata cire ba, bathroom ta kai tace "wastsa ruwa, muje hospital", ba musu tayi abinda aka sata, sunje hospital doctor yace stress ne, nan yabata magunguna yace a bari ta dinga samun hutu. Sun dawo gida Momsie da kanta ta roka Daddy kan ya janye extra lesson dinda Islam takeyi saboda a ganin ta shi yasamata stress, ba musu Daddy ya amince saboda shida kanshi ya tausayawa Islam.

*ONE ND A HALF MONTH LATER*

     _Mzz Daddy 💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin