Chapter 6

1.4K 93 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

               *ZYNAH*

(An Interesting Love Story 2017)

By Aisha Muhammad (Mzz Daddy 💋)

     *Ina mai matukar  ba  fans  hakuri  na rashin typing  da banyi kwana biyu akan wani dalili amma yanzu In Sha Allah zan cigaba daga inda na tsaya da yardar Allah with much luv#FANS#ILYSVM❤*

QUOTE :- "u've got to follow ur passion. U've got to figure  out  wat it is u luv - or u really  are. And have d courage to do dat . I believe  dat d only courage  anybody ever needs is d courage to follow ur dreams".

     _I dedicate dis page to each nd every member of *ZYNAH FANS CLUB*

                0⃣6⃣

     Sanye  yake  cikin  hadadden  shaddanshi  sky blue wanda yaji aiki da dark blue din zare , hulan kanshi baki wanda  ya zauna mishi  das a kai  sai  agogon shi  kirar  rolex shima  baki sai takalmin shi shima baki yayi kayu matuka sai  zuba kamshi yakeyi. Fitowa yayi daga dakinshi ya zauna parlour  tare da kallon agogon hannun shi da alamun wani yake jira , tsaki yayi tareda dauko wayan shi kirar iPhone  7+ yana daddannawa , sai alokacin nasumu na kare mishi kallo.

     Fari ne sosai kaman farin  balarabe , dogo mai fadin kirji da cikar zati , da yalwataccen  gashin  kai  mai uban laushi da tsantsi kaman  yayi relaxing  dinshi. Yanada oval shaped face da pointed nose , golden eyes mai tafiya da imanin  duk wanda yagani , yanada madaidaicin pink lips wanda koda yaushe yana nan a tsuke kaman wani mace. *ASHRAF* kenan  yaro dan kimanin shekara ashirin da hudu (24) a duniya mai jini a jiki , yanzu zai shiga final year dinshi a ABU zaria inda yake karantar architect wato ilimin zane .  Wannan kenan.

     Wayan dake hannunshi  ne yafara ringing , yadaga fuskar sa ba yabo ba fallasa tare da cewa "Mallam wai kana inane ka barni zaune tundazo kamar wani kayan wanki ko sai munyi miss din sallahn juma'a hankalin ka zai kwanta" , ta dayan  side din akace ,"bros ganifa awaje kafito mutafi" , "da mota hannun ka ko babu", a takaice yace "babu kasan  motan nawa ba lfy","ok gani nan fitowa" , tareda kashe wayan. Daki ya shiga ya dauko car keys dinshi sannan ya fito tareda kulle kofa , da ya fito compound din gidan saida nasaki baki da hanci ina kallon girmansa wanda part daban2 ne a gidan ya kai part biyar, part biyu ginin iri daya ne sai part dinda *ASHRAF* yafito daga ciki sai wani karamin gini shima amma ta ćan baya yake kaman boy's quarter ne sai babban wanda shi kadaine ginin sama kuma duplex ne .

     Parking lot ya nufa inda motoci ne wurin birjik kaman company , wata bakar Mercedes  benz 2017 ya dauko baka ya fito da ita tareda yin horn mai gadi na gefe yana alwallah yabude masa gate din , yana fitowa ya hango Sameer tsaya a kofan  gidansu yana jiranshi , karasawa yayi wurinshi Sameer ya shiga suka kama hanya zuwa masallacin dake fada cikin zaria city.

     Sun dawo daga  masallaci  inda dukkansu sukayi gidansu *ASHRAF* , sun shiga sukayi parking suka fito nan sukaga Minal kanwar *ASHRAF* zata fita ta gaishe su sannan tace"Yaya Ummi na  neman ka wai in kasamu lokaci ka leko ta","toh zan leka ina zaki yanzu","zanje ziyara ne","sai kin dawo ",Sameer yace "a taho min da tsaraba"cikin tsigar tsokana , dariya tayi tace " za'a kawo karka damu"sannan  ta shiga motarta sukuma sukayi cikin gida.

     Bayan  sun huta Sameer yace zaije ya chanza kaya yadawo  saboda mayan  kayan sun ishe  shi , shima  *ASHRAF* kayan ya chanza zuwa blue jeans da black top ya fito  ya shiga daya daga cikin sashen dake gidan wanda wannan ne mahaifiyarsa  take ciki. Ummi ce zaune  da Husnul  Muslim  a hannu tana karantawa tasa recommended  eye glasses na ciwon ido , tana cikin  shigar  alfarma wanda  daka ganta kasan kudi na magana anan. Sallama  yayi ta dago tare da cire glasses din sannan ta   amsa masa sallama tana kallonsa da murmushi tace "babana ka dawo" yace "eh Ummi   tundazu na dawo naje na hutane tukun da fatan ban makara ba" tayi dariya ganin yadda yayi maganar a shagwabe  tace "ko kadan,dan dama  abbanku  ne zai dawo jibi which is Sunday so kai nakeso kaje ka dauko shi a Airport","ba damuwa Ummi Allah ya kaimu"ta amsa  da "Ameen" yace" kaman  karfe  nawa jirgin zai sauka","2pm","ok toh ni zan dan leka Sameer sai zuwa yamma zan dawo gida","kai dai da Sameer  dinnan Allah ya barku tare"yace "Ameen" tare da sosa keya yana murmushi  ya fita sai gidansu Sameer dayake unguwa daya suke.

     Yaje ya tarar Sameer na kallon wani American  movie _ESCAPE_shima ya zauna sannan ya kalli Sameer yace "guy an kusa komawa school fa hope u are ready" Sameer yace "ni kai ne komai school  komai school ba kada wani lokaci saina karatu,ni ko ankoma sai na kara one week sannan zan koma","bakada matsala shiyasa amma ina gayamaka ka gyara halinka" Sameer yama *ASHRAF* wani irin  kallo irin na bangane ba dinnan sannan yace "wani hali ne dani mara kyau"? A takaice *ASHRAF* yace"na rashin son karatu" hararar  *ASHRAF* yayi kasa kasa *ASHRAF* yace " na ganka" tare da daukan trow pillow zai jefa masa Sameer yayi dodge yana dariya.

      Kuyi hakuri da wannan ba yawa banda enough  ba3.

     Mzz Daddy💋

ZYNAHWhere stories live. Discover now