Chapter 61

1.3K 74 0
                                    

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻



              *ZYNAH*


(An Interesting Luv Story 2017)


By Aisha Muhammad (Mzz Daddy💋)


*BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*


QUOTE:-"Living in d favorable n unfavorable situation is called a Part of Living, But Smiling in all those situations is called Art of Living!!!"


               6⃣1⃣

*WASHEGARI*

     Tun wuraren karfe tara na safe su *ASHRAF* sukazo sukayi sallama suka wuce har da Abba, seda suka fara sauka a Zaria sannan suka dau mota zuwa Abuja, *ASHRAF* kafin ya wuce ya turawa *ZYNAH* text wai kar tayi kuka in za'a kawota saboda kar ta sawa kanta ciwon kai saboda bayason kukan da takeyi. Nan aka dinga shirya amarya saboda jirgin karfe hudu zasubi, a airport sukayi la'asar wanda daga cikin wa'anda zasu raka amarya Adda Hafsa ce da wasu tsofaffi guda uku se su Minal harda Islam, *ZYNAH* tayi kukan rabuwa da gida da kyar akan banbareta daga jikin Daddy wanda shi kanshi kasa lallashin ta yayi saboda shima din hawayen yakeyi, Momsie kuwa bata ma tsaya a wurin ba daki ta shiga saboda bataso tayi kuka a gaban *ZYNAH*, sosai aka mata nasiha sannan aka sata mota basu zame ko ina ba se airport inda da zuwansu ko minti talatin ba'ayi ba jirginsu ya tashi, *ZYNAH* wani barin na zuciyar ta na bakin cikin barin iyayenta wani barin kuma farin ciki ne fal na za ta tare a gidan masoyin ta, sanyin idaniyarta. Tafiyan 45min sukayi jirginsu ya dira Abuja, driver din Adda Hafsa ya kwashe su zuwa gidan *ZYNAH*  wanda yagaji da kanshi dan kyau, gabadayansu seda sukayi kauyanci a gidan dan ba wacce ta taba zuwa cikinsu se Adda Hafsa itama masu jere ta rako, sama aka kai amarya inda dakuna hudu ne a wurin, na tsakiya by d right aka kaita, dakin yayi kyau combination of purple nd pink aka mata, zaunar da ita suka yi a tsakiyar gado sannan suka kara mata nasiha inda a halin yanzu ta gaji da kukan ta hakura, suna gama mata nasiha Adda Hafsa tace su zasu wuce amma zata bar su Minal in angwanai sunzo se su dawo, saukowa kasa tace "Minal ki kula da yarannan karsu mata barna, shiyasa zan barki dasu, idan angwanai sunzo ku taho gida komin dare", Minal tace " toh Adda Hafsa", sannan ta wuce tareda sauran tsofaffin.



     Seda akayi isha sannan  Minal tasa *ZYNAH* tayi wanka ta dauko mata wani rantsaten lace red me touches of black ajiki tasa sannan suka mata kwaliyya sama sama tayi mata wanka da turare amarya se kamshi take sannan su Basma kuma suka kara gyara mata gidan suka kunna burner suka  sa turaren wuta nan da nan gidan ya dau kamshi, karfe tara da en mintina angwanai sukazo, tun daga compound akejin hayaniyarsu har suka shigo parlour inda Minal ce kawai a zauna suka gaisa sannan tace musu amarya na sama, suka haura bayan tagama yima wanta tsiya tana tsokanan shi, shikuwa se murmushi yakeyi yakasa rufe bakin(ba abunda ya kai ka auri masoyinka dadi😊). Da sallaman su suka shiga dakin inda suka ga amarya zaune a tsakiyar gado fuskarta lullube da mayafi, nan suma suka dan jijjin gina *ASHRAF* yaje ya zauna kusa da amarya shi yasa hannu ze yaye gyale su Basma sukace "a'a hamma karka bude, baku bamu kudin siyan baki ba", *ZYNAH* murmushi tayi jin abunda sukace yace " nawane", Islam da bakinta yafi na kowa tsayi tace "200k", zaro ido angwanai sukayi Sameer yace " me laifin ku karba 50k", suka kuma sukace sam basu yarda ba, shi ango daya kosa yaga fuskar amaryarsa yasa hannu a aljihu ya zaro bundle din 500 guda biyu ya mika musu saboda suna bata mishi lokaci😂, karba sukayi shikuma yasa hannu ya yaye mayafin tareda cewa "aminci ya tabbata ga Allah wanda ya kera wannan halitta dake gaban", gabadaya dakin dariya suka bushe dashi, shikuwa ko ajikinshi ya kai baki yamata peck a kumatu Sameer yace " kunga kuzo muyi abunda ya kawomu dan wannan angon ba kunya bace ta ishe shi ba", nan duk sukawa amarya da ango nasu gutun nasihar wanda bai wuce ayi hakuri ba, suna gamawa suka fito tareda yima amarya fatan alkhairi, nan suka ce su Minal suzo a sauke su gidan Adda Hafsa, *ASHRAF* har compound ya rakasu, Sameer yaje daidai kunnenshi yace "guy a ma amarya sannu sannu dan wannan zumudin yayi yawa", duka *ASHRAF* ya kaimai ya goce yana dariya sannan ya shiga mota yabi bayan sauran suka fita, *ASHRAF*  yaje ya rufe gate ya dawo ciki ya rufe kofa ya haura sama.



     Da sallama ya shiga dakin, cikin sanyin murya ta amsa mai sallaman shi sannan ya karasa ya zauna kusa da ita, ya dade yana kallonta itakuma kanta a kasa sannan daga bisani ya rungumota a jikin, a tare suka sauke ajiyar zuciya yace " *DAMSEL*  yau ina mai tabbatar miki da cewar kin cika min burina, saboda da dade ina burin ganin wannan ranan, kuma nafi kowa jin dadin zuwan wannan ranan, *DAMSEL*  inaso mu gina rayuwar auren mu akan tafarkin gaskiya da yadda, inaso ki yadda dani kaman yanda na yadda dake kinji", daga mishi kai tayi sannan yace tashi kiyi wanka kiyi alwallah kizo muyi sallah, mu godewa ubangijin mu daya nuna mana wannan rana", cikin sanyin murya tace "ai nayi wanka", yace " nasani, amma inaso ki sake", ba musu ta mike ta ajiye mayafin ta kan gado ya rakata har bakin kofan bathroom din sannan ya dawo ya shiga closet dinta wanda yake sheke da kaya, rigan bacci ya dauko mata ya ajiye kan gado sannan ya fita zuwa dakinshi. Seda ta tabbata baya dakin sannan ya fito taje wurin dressing mirror tayi shafe shafen ta, har zataje ta dau kaya ta hango wanda ya ajiye mata, komawa tayi ta dauka, silky gown ne wanda tsayinshi iya rabin cinya ne *ZYNAH* tace "kai bazan iya sa wannan ba", ajiye wa tayi se kuma wani zuciyan yace mata " karkiyi haka, abunda mijinki yake ra'ayin ganin a jikin ki kenan, in bakisa ba bazeji dadi ba", shahada tayi ta dauka tasa nan rigan ya tame mata jiki shape dinta gabadaya ya fito waje, ganin bazata iya zuwa wurinshi a haka bane yasa ya dauko after dress ta dora a kai sannan feshe jikinta da turare tasa hajabi ta fita, dakin shi ta shiga da sallamanta ya amsa mata yana sanye da jallabiya da alama shima daga wanka ya fito, murmushi yayi yace "amarya kinsha kamshi", shiru tamai ta makale jikin kofa yace " karaso mana, ko kunya na kuma akeji yau", kanta kasa ta kara ciki ta zauna bakin gado shikuma ya shinfida musu sallaya yace "taso muyi sallah", tashi tayi ta karasa sukayi sallah raka'a biyu suka sallame sukayi addu'an neman zaman lafiya sannan ya rike kanta yamata addu'a ya kuma yi mata tambayoyi ta bashi amsa yace " ashe ustaziyya ce", murmushi tayi yace "ina zuwa", tace " toh" tashi yayi ya fita ita kuma ta linke sallayar ta koma kan kujeran da ke dakin ta zauna, be dade ba ya dawo dauke da tray a hannunshi ya ajiye kan tebur ya zauna kusa da ita ya janyo glass cup ya zuba mata hollandia yoghurt aciki yace mata "bismilla", yoghurt din tasha sosai amma bata iya taci kazan ba yace " bakya jin zafi ne, kinsa after dress kinkuma sa hijabi", shiru tayi mishi yace "bari a cire hijabin kisha iska", nan ya cire mata hijabin gashin kanta dayagaji da gyara ya bayyana yayi murmushi yace " cire after dress din kisha iska", da sauri ta dago kai tace "a'a barni haka bana jin zafi", murmushi yayi yace "Allah se kin cire", jin yace Allah yasa ta sadaukar ta mike ta samo cirewa kanta a kasa shikuma idonshi kyar akan ta ko fitawa ba yayi, tana gama cirewa yaji wani yarr a jikin shi itakuma ta koma ta zauna a takure ya rungumota yace " ki saki jikinki saboda a gaban mijin ki kike", da haka suka gama ciye ciyensu, ya tashi ya fita da plates din ya dawo suka wanke baki sannan yacire jallabiyanshi yaja hannunta sukaje kan gado suka kwanta, yatsun hannunta ya fara wasa dashi yana tambayarta wacce ta mata kunshi da haka aka fara zarcewa nikuma naja en sirarun kafafuna nayi waje tareda ja musu kofa saboda wannan sirrinsu kuma Allah ya la'anci mai bayyana sirrin aure(Allah yasa mu dace amin).



     Wuraren karfe uku na asuba na leka nan naga *ZYNAH* se shesheka akeyi ana sauke ajiyar zuciya da alama tayi kuka har tagaji, *ASHRAF* ne yafito daga bathroom daure da towel da alamun wanka yayi ya karasa wurin ta mayar da fuskan ta cikin pillow tayi tasa mishi sabon kuka, rike kanshi yayi da alamun bayason kukan da takeyi yayi kasa da murya yace "only one dan Allah yi hakuri, i didn't mean to hurt u dis much, kukan nan ze kara miki ciwon kai, stop crying kinji", a hankali ta rage sautin kukan ta ya tashi ya dauke ta be ajiye ta ko inaba se cikin bathtub daya cikashi da rufan zafi, ihu ya sake mai tareda kankameshi tana neman fitowa yace " ki zauna a ciki, shi ze rage miki radadin da kikeji", yana mata maganane cike da tausayawa, seda tayi kusan minti ashirin a ciki sannan ya fito ya barta tayi wankan tsarki, koda ta fito baya dakin a daddafe ta karasa kan gado ta dauka jallabiyan shi da tagani ajiye ta dauka tasa sannan kwanta, shigowa yayi dauke da tray a janyo tebur ya ajiye bakin gadon yace "tashi kisha tea", ba musu ta tashi dan wani yunwa takeji, shida  kanshi ya dinga bata soyayyen kwai tagama ta sha tea sannan ta koma ta kwanta duka wannan bidirin nan da akeyi taki yarda su hada ido dashi, fita yayi da kayan kafin yadawo har baccin wahala ya dauke ta, shima din kwanciya yayi ya rungumota jikinshi da haka barci ya dauke su.



     _Mzz Daddy💋✍🏻✍🏻_

ZYNAHOù les histoires vivent. Découvrez maintenant